← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 225

Sashe 95

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

da Amihh suka rako hajiya karama har bakin motar ta, bayan Amihh ta mata sha tara na arziki, turarruka ta bata na alfarma dade sauran gyara namu na mata masu mazaje, seda ta cika mata tankama tankama din ledoji da kaya na alfarma ciki hadda laces manya guda biyu da atampopi super guda uku, daman hajiya maryam bata rabo da kayyaki haka sbda kyautatawa wadanda sukazo gurinta. Ledojin guda biyu Amihh ta cika ma hajiya karama d kaya na Alfarma, hilwah da Salwah ne suka riqo ledojin suka bude gidan bayan motar sukasa ledojin. Hajiya karama daketa kallon hilwah taja hannun hajiya maryam suka koma gefe dan nesa kadan dasu hilwah. "daman Anty zan kara jadda da miki shawarata ne, Dan ALLAH ki hadawa yarinyarnan yan komatsenta ta koma can side din mijinta Wlhy zasu fi shakuwwa in suna ganin junansu a gu daya, ko yaya nasan ze farmaki yarinyarnan, ni wlhy dukna kagu ace ya Mata ciki..." Amihh ta zaro ido ita kunya ma ta rufeta, shiyasa wani lokacin bata ganin lefin AB'ILAL in yana isknci sbda ruwan nashi ba ruwan masu kunya bane. "Allah shiryaku...'' Cewar hajiya maryam Hajiya karama tayi murmushi kana tace "ba mgnr rashin kunya nayi ba Amihh, ..."_ hajiya maryam tace "kwarai ma kuwwa, mgbr kunya kikayi....'' Hajiya karama tayi murmushi danta fahimci gatse ta mata. "Ni de bance komi ba..." Cewar hajia karama, hajiya maryam ta girgiza kai kawai. Hajia karama ta jawo hannun Amihh suka dawo inda su hilwah suke tsaye ita da salwah, sukayi sallahma da junansu, hajiya karama ta shige motarta taja tana kallon hilwah, har ta fice a gidan.. Amihh tasa su Salwah da hilwah gaba suka koma cikin gidan, se nazarin maganganun Hajiya karama takeyi a ranta.
Chapter 95 · 0% Book details