← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 225

Sashe 11

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*in tsarin book dina be mikiba ki bar min abina plx....* *WRITER OF KYAUTAR ALLAH* SAADATU BINTU ABDULLAHI鉁嶐煆� *Malikinnass* 馃吙锔�3 *Kano state Nasarawa G R.A* "Ashe bakada mutunci bansaniba se yau, wai meyasa a ko ina seka nunamin ban isaba? Shikenan..." Sautin wata babbar mace ke tashi cikin bacin rai, a babban falon tamfatsetsen gidan na masu rufin asiri, babban falone me dauke da manya manyan kujeru na Turkish kirarsu kirar Royal chair ne amma kuma sun bada wata siffar daban , sunyi kmr Royal amma sunfi tsarin Royal kyau da daukar ido, kalar kujerun kalar ash ne light, sunsha filoli masu kyau irin na zamani da ake kayata kujeru dasu (throw pillows) tako ina falon yayi kyau, yaji kayan more rayuwa kama daga wadanda nasani har zuwa wadanda ban saniba. "Am very sorry Auwal hubb inada dalilin dayasa na mari yarinyarna, kwata kwata bata da tarbiy..." Cewar kyakyawan saurayin dake zaune kasan kafafuwanta black handsome guy, dukda a zaune yake Amma na gano dogone neshi wato uban gidan wadah. Cikin kunar zuciya kyakyawar dattijuwar ta daka masa tsawa "Ka rufemin baki ko in dauke ka da mari..dalilinka na banza da hofi, karka kara cemin komi, tin ban tafka maka rashin mutumciba wanda yafi naka daka aikatamin...ina magana kana magana, stupid! Ni kake gayawa kanada dalili, dalilinka daya ne bakason Aure kafiso kayita zama a haka tuzuru, mata nawa yaran frnds dina masu tarbiya nake hadaka dasu karshe sede ka bisu da cin mutumci, da zagi, kuma ba kowa kake ciwa mutumciba bace ni uwarka danayi naqudarka na kawoka duniya, koda yake ba lefinka bane lefin rashin sanin darajata ne da bakayiba.." Ta karashe mgnr cikin kunar rai, tana gyara farin siririn glashin dake manne da kwayar idonta kai da ganinta kaga cikakkiyar yar boko kyakyawa ce ita fara sol take kmr a taba jini ya fito. Kasa yayi da kansa yayinda sumar knsa baka kirin keta shining tana daukar ido kai kace bakin balarabe ne, kwantar da muryarsa yayi kasa-kasa ya fara magana still kansa na kasa, danya kula uwar tasa ta harzuqa ainun "Ba haka bane Auwal hubb pls ki fahimceni bawai na rainaki bane, Wallahi basu da kamun kaine ni matan yanzu, ina ganin ma duk yan DANDI ne, gaskia bama wani tantama yan iska ne... Plx Auwal hubb ki fahimceni, dan ALLAH kar ranki ya baci a kan dan.." Kara daka masa tsawa tayi cikin kunar zuciya "Banace karka kara magaba! Zanci ubanka wallahi kaji na fada maka, idan shaye shaye ka fara yau zan sauke maka haukan dake kanka, na gaji da isknci da bura ubar da kakeyimin a cikin gidan nan, kana hadani da friends dina da muka taso tare, ko dankaga ubanka beda raine? Wato ni ina mace ka rainani ko? " dagowa yayi ya zuba mata sexy eyes dinsa madu jahilin kyau bakin kwayar idonsa se walwali yakeyi kmr danyan gold a rana, tinda yaji zagin zanci ubanka a bakinta yasan ranta ya baci Ainun. "Allah Ba haka bane..." Ya fadi cikin sanyin muryarsa me mugun dadih. A wannan karonma daka masa tsawar ta karayi "Inka kara magana a falon nan, sena tafka maka rashin mutumci kaji na fada maka ! Inba raini ba uwarka kayimin , harni insaka kayi abinda raina keso kuma ze zama me amfani a gareka amma ka nunamin sam ni ban isaba, Wallahi AB'ILAL bakasan mutumcinaba, mata na goma kenan ina zaba maka kana watsamin kasa a ido, daga wadda zaka duka se wadda zaka cima mutumci saboda Allah fa? Ka tunafa shekarunka talatin a duniya, baka taba sawa ranka son kayi aureba a rayuwarka , hasalima baka taba ganin mace kace kana sontaba, ballantaba kayi tunanin yin Aure," dan jim hajiya maryam tayi idonta na kn Danta AB'ILAL wanda kansa ke kasa a hasale taci gaba da magana hadi da girgiza kai cikin tsananin takaici " kai! Na fara tantama a kanka AB'ILAL anya kanada lafiya a jikinka kuwa?" Cikin hanzari ya dago lum-lum eyes dinsa ya Kara sauke mata su a kanta babu alamun kunya a cikin kwayar idonsa ya daga mata kai da girah a lokaci daya kana ya fara magana da daddadar muryarsa me natsar dame saurare " Yauwa Auwal hubb kinga abinda ya kamata ki tambaya kenan tintini baki tambayaba,..gaskia inajin banda lafia ne Auwal hubb, nifa ban tabajin sha'awar kowacce maceba,ni banma sonsu ne gabaki daya, Kinga fa Auwal hubb dukfa yan iska ne matan yanzu, ba matan arziki bane wlhy, basa riqe mutumcinsu, ni kuma gaskia inde har na Auri mace ba virgin ba sakinta zanyi, to kinga Auwal hubb maganin Ayi kar a fara, gaskia nide, bnsan wannan zabin naki.." Baki sake take kallon Dan nata tilo namiji kmr rai su biyu kawai Allah ya bata AB'ILAL se kanwarsa Salwah yar 17yrs. Tsawa takeson ta daka masa amma sam ta kasa daman tini tasanshi beda ta ido yana da tsananin tsaurin ido tin yana yaron shi duk abinda ke ransa kawai yana fadine ba ruwansa, sam be da kunya ko miskala zarratin, sannan be iya karyaba a ko ina gaskia yake fadi koda kuwa za a kasheshine. "Tashi ka fitarmin a falo dan ubanka! Mara kunyar banza mara kunyar hofi! Na kusan iyakance iskancinka!!" Hajiya Maryam ta fadi a kunyace hadi da kosawa da iskncinsa a cikin ranta, can kasa kuma bacin ransa ne fal ranta. Matsowa yayi ya dafa kafafuwanta cikin sanyin murya ya fara magana "Auwal hubb to zaki samo min magani ne ko? Knce meke damuna na gaya miki kuma kina korata why now?" Ya karashe mgnr yana shafo yatsun kafafuwanta hadi da mammatsasu. Hajiya maryam ta zuba masa idonta masu kama da nashi, a hasale tace "Ubanka zan maka ? Ka tashi ka barmin falona nace!!" AB'ILAL ya dago ya kara satar Kallon mahaifiyar tasa yasan ya bakanta mata matuka. Cikin muryarsa ta shagwaba ya fara magana "inje ina?nace miki bnda lafia ne Auwal hubb plx, zaki nemo min mgni ne..." Sosai Hajiya maryam ta hade rai dan ita macce ce da batason raini sannan akwai tsare gida , danma duk AB'ILAL ya gama rainata, Amma ko auta salwah tsoronta takeji. "Tashi ka fitarmin a falo! in har baka bi umarninaba wlhy bazamu taba zaman lafia ba nida kai! Kana karyar iskanci ne!!" Ta karashe mgnr a matukar hasale babu alamar wasa a zancanta. Idanuwansa dake kanta ya kara zarosu sosai a knta, "Allah ya tsinewa muna fukin daya gaya miki mgnr nan Auwal hubb.." Ya fadi da muryarsa ta borin kunya. Ajiyar zucia ta sauke a hasale ta dauke kwayar idonta a knsa domin kwayar idonsa nada wani irin sirri na kwarjini kmr ubansa koma tace yafi ubansa. Bude baki yayi da niyar ya kara magana cikin kunar zuciya tace "inka kara magana a falon nan wallahi sena mareka!" Yadda tayi mgnr Kawai ya tabbatar masa da da gaske take ranta ya baci ainun amma dukda hk beyi yunkurin tashiba. " tashi ka fitarmin a falo dan kutmar ubanka!" Ta fadi cikin tsananin bacin rai. Mikewa yayi jiki babu laka amma bakinsa be mutuba "Auwal hubb ke ba Nigerian ba amma kin iya manya manyan zagi kamar bahaushiya..." Yayi mgnr kasa kasa, amma tsaf hajiya maryam ta jishi bakin ciki ya kara rufeta saboda ya riga ya gama rainata, hanyar shiga side dinsa ya nufa ta daka masa tsawa hadi da dakatarwa "Ka fitarmin a gidana gabaki daya!" Ta karashe mgnr tana zabura kmr zata karaso inda yake ta daukeshi da mari. Juyowa yayi dan harya kai hannunsa handle din kofar dazata sadashi da side dinshi, Ya zubawa mahaifiyar tasa ido tabbas har ynzu yna hango bacin rai a kan fuskarta, wai a hk danma bataga abinda ya aikata ba kenan."side dina fa zan shiga..." Ya fadi idonsa karrr a kan nata. "Dan ubanka ka fitarmin a gidana nace, bakai baka da kunya ba baka data ido, zanyi mgninka, ka fitarmin a gidana duk ranar daka kawomin macce da kakeso ka aura seka dawomin gida..." AB'ILAL ya zaro idanuwa waje dajin karshen zancen nata, marairaice idanuwa yayi yace "Haba Auwal hub,..." Ta katseshi ta hanyar daka masa wata iriyar razananniyar tsawa "karka kara cewa komi!! Kawai ka fitarmin a gidana, duk rnr daka shirya aure, ko ka kawo matar Aure ko ka aminta da zabina seka dawomin gidana..." Zaro idanuwa waje AB'ILAL yayi, yana da niyar bude baki yayi magana Hajiya maryam ta mike tsaye a matukar harzuke danta lura mahaukaciya yakeson maidata, Gadan gadan ta nufo inda yake , ganin hakan yasashi ya fice a gidan a guje yana fadin "Auwal hubb, to ina zanje!?" "Kaje duk inda zakaje mara kunyar arziki kawai.." Hajiya maryam ta fadi cikin kunar zucia se haki takeyi kasancewar tanada dan jiki, amma tanada tsawo, jawo kofar falonta tayi ta rufe , tana zancen zuci ta nufa bedroom dinta, tana zancen zuci, tamfatsetsen dakine wanda yaji hadadden gado 6 bye 7, gadon ya hadu iya haduwa, Indian bed ne beda hayania sede yanada matukar kyau na fitar hankali. Karar wayarta dake ajiye a side drower ya cika dakin, da dan hanzari ta karasa ta dauki wayar tata kirar Samsung latest one. Sunan hajiya Aisha ya bayyana rado-rado a kan screen din wayar, gaban hajiya maryam ya yanke ya fadi, ta zubawa screen din wayar ido, tasan Aika aikar da AB'ILAL yayine yasa hajiya Aisha kiranta da Yammacin. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!! Ya zanyi da rayuwata?" Ta tambayi kanta a matukar gigice nan ta hau maganganu ita kadai kmr zautacciya har kiran wayar ya katse wani yakara shigowa dagawa tayi jiki a matukar sanyaye, ta kara wayar a kunne. "Haba maryam! Haba maryam!!" Wannan shine abinda ya fara dukan dodon kunnen hajiya Maryam jiki a sanyaye ta karasa gefen bed dinta ta zauna zucia babu dadih nan da nan taji hantar cikinta ta kada.danta ya zama dan kuka me jawa iyayensa jifa. A sanyaye ta fara magana "Dan ALLAH hajiya Aisha kiyi hakuri, kinsan de ni da kaina bazan sa yaronnan ya aikata abinda y .." Hajiya Aisha ta katseta cikin kunar zucia "Base kincemin komiba, bana bukatar jin komi daga gareki, ashe abinda ake fadi a gari da gaskene, yaronki beda kunya besan darajar yaya mata ba, daga magana kawai seya hau dukan min yata in yana dukan yaran
Chapter 11 · 0% Book details