← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 225

Sashe 12

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wasu yaci banza ni be isa ya dakarmin yataba yaci banza, ku tsammaci sammaci daga koto, dan wallahi bazan taba yadda ba .." Kai dajin yadda take mgna kasan abin yaci mata zafi a zucia. Ajiyar zucia hajiya maryam ta sauke cikin tsananin tashin hnkli ta fara magana "Hajiya Aisha dan Allah kiyi hakuri, Dan darajar iyayenki labari ya iso gareni,dreva dinsa yayi hanzari yazo ya sanar dani abinda ya faru,Dan ALLAH kiyi hkri Hajiya, zan dauki mataki a kan..." Cikin tsiwa hajiya aisha ta katseta "bana bukatar daukar Matakinki ki barni ni da kaina zan daukarwa yata mataki, ace ka kama ma mace hannu ka murde har seda ya karye ya barta sekace jaka ynzu hk muna emergency, wlhy seyasan yarwa ya taba.." Tana gama fadar hkn cikin zafin zucia ta katse wayar. Hajiya maryam ta sauke ajiyar zucia hadi da zubawa wayar ido kmr me nazarin wani abu ita knta ranta a matukar bace yake, wato dukan da AB'ILAL yayima yarinyarnan ya wuce wasa tinda gashi harda karayar hannu har ma ya kaisu ga asibiti, ita a zatonta mari ne kawai ya mata ashe uwar uban marine. "Innalillahi wa'inna ilahirraju'un! Ya ALLAH ka shiryamin yaronnan.." Hajiya maryam ta fadi cikin kunar zucia, ji takeyi kmr ta fashe da kuka, contact din wayarta ta shiga, lalubo number din hajiya Juwairriyya tayi direct tayi dealing din number din bugu daya biyu hajiya ta daga. Ajiyar zucia hajiya maryam ta sauke cikin sanyin muryata ta fara mgna "Assalamu alaykum, hajiya barka da yammaci..." Daga wayar hajiya Juwairriyya ta amsa da "wa'alaykumussalam barkade mom AB'ILAL, yakuke ya iyalin naki?" Ba tareda hajiya maryam ta amsaba tace "Hajiya knga abinda yaronnan ya karayimin kou?" Daga yadda take mgnr ya tabbatrwa da Hajiya Juwairriyya ran hajiya maryam a bace yake, sannan tana cikin tsananin tashin hnkli, tin a farko ta fahimci hakan. kwantar da muryarta tayi irin na manyan mata masu halin dattako ta fara magana "Maryam mi yayi miki? Mike faruwa? Ki kwantar d hankalinki ki gayamin mike faruwa?" Ajiyar zucia hajiya maryam ta sauke zuciarta cike da takaicin AB'ILAL ko salwah datake karamar knwarsa wadda ya bawa kusan 13yrs bata mata abinda yake mata. "ina yar wajen hajiya Aisha matar mataimakin governor din kano alhaji samaila zambur?" Hajiya Juwairriyya tace "Eh naji naji, na ganeta Hajita Aisha na ganota, ko ba wadda AB'ILAL ze auri yar wajentaba, harma ansa rana ban mantaba saura 3weeks Ai, kou wani abun ne ya sameta?" Hajiya Juwairriyya ta jefo mata tambayar itama hnklinta a Dan tashe. Hajiya maryam ta lumshe idanuwanta dasuka cike da tsananin bacin rai ta budesu a kan tamfatsetsenn TV din dake dakin nata a zahiri idonta na kn TV amma zuciarta ta lula duniar tunani, shiru tayi ta gaza mgna sbda duniar tunanin data afka. Shirun nata ya tabbatrwa da hajiya Juwairriyya babu lafia tabbas AB'ILAL ne ya maimaita halin nasa na rashin mutumci daya saba. "hajiya ki sanar dani meke faruwa? AB'ILAL din ya kara kira mana wani ruwa ne a wannan karon?" Hajiya Maryam ta furzar da wata iska daga bakinta me cike da tsananin tashin hankali ta jawo numfashi daga kasan makogaronta da kyar kana tace "Ya kara wlhy, a wannan karon da zafi ya debo mata yarinyar mataimakin governor gabaki daya ya debo mana, ina tunanin dukan tsiya ya mata hadda karayar hannu yanzu haka tana emergency room, .." A matukar razane hadi da dimauta hajiya Juwairriyya tace "What? To metayi masa? Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Bari inzo kawai gidan wannan maganar bata waya bace ..." Tana gama fadar hkn ta katse wayar. Hajiya maryam ta ajiye wayar a inda ta dauketa zuciarta cike da tsananin tashin hankali "very soon senaci kutmar bura uban yaronnan..." Ta fadi hkn a bayyane, hadi da rafka uban tagumi, nan da nan ta afka duniar tunani a zahirin gaskia tagaji da iskanci da bura uba irin na AB'ILAL zata iya cewa ma ya gagareta ta rasa yazatayi dashi, gashi data fara masa fada in seriously seya maida abin wasa a wannan karon tafi kaunar aci ubansa kawai ta huta itama, maybe ta samu ya sassauta daga iskncin da yakeyi. "Allah na tuba ka yafemin..." Ta fadi a bayyane dan a zatonta wani lefin tayima ALLAH ya jarabceta da haihuwar AB'ILAL gashi yazo yafi karfinta, yafi karfin family din ubansa ma, kowa AB'ILAL bawai basa kaunarsa bane Amma rashin jinsa yayi yawa wlhy tin kafin yakai hkn yake abinda ransa keso wasu a family din uban nasa, wasu suyi masa mgna wasu kam basumason lefinsa wadanda basuson sa sunfi yawa, danma hajiya maryam tanada daurin gindi a jigon gidan wato babban yayan mijinta Alhaji Murtala, kasancewar bangon gidan nasu duk sun zube wato sun rasu, ynzu Alhaji murtala shi kadaine babba a gidan, daman su uku iyayensu suka haifa Alhaji murtala ne babba, se Alhaji Muhammad wato mahaifin AB'ILAL, se autarsu hajiya badiyya wadda ke Aure a garin kaduna. A wani bangaren hajiya maryam tana ganin iskancin da AB'ILAL yakeyi ya dangana ne da yadda ubansa ya masa gata kafin ya rasu domin kuwa son duniar nan ubansa ya dora masa, babu irin kaunar da ubansa be nuna masaba, sam bayaso yayi nesa dashi, da kyar ya iya barinsa zuwa kasar waje a can yayi karatunsa bayan kammala secondary dinsa a nan gida Nigeria, ya nufa USA yayi karatu a fannin kasuwanci, yanada zurfin ilmi sosai a fannin kasuwancin. yau kimanin shekara sha bakwai kenan da rasuwar mahaifin nasa, domin kuwa rasuwar tasa tayi dai-dai da ranar haihuwar autarta Salwah. Mahaifin nasu Wato Alhaji Muhammad dauda Auta shahararren dan kasuwa ne daya shahara A fannin kasuwanci domin kuwa yasha gwagwarmaya a dunia sannan an buga dasu kwarai a fannin kasuwanci, shi din haifaffen garin katsina ne, a dutsanma, ya dawo garin Kano da zama domin a nan jigon kasuwancin nasa yafi karfi, zan iya ce muku Alhaji Abubakar shinkari sune kasuwar kwari ta kano, dan duk yawanci shagunansane halak malak, Allah ya rufa masa asiri Alhmdllh. Alhaji Muhammad Autah sun hadu da hajiya Maryam ne a nan garin kano tazo hutu gun Knwar mamarta dake kano, amma su din ba Nigerian bane su din indian ne, domin mahaifinta ba'indiyye ne, mahaifiyyarta kuma balarabia ce. hausa ta shige hajiya maryam ainun, Dan inba ka kula da yanayin halittartaba bazaka taba cewa itadin indian bace, domin tafi jakin kano jin hausa tin lokacin kasancewar karantar hausar tayi, sunyi aure da Alhaji Muhammad Auta bayan sunsha soyayyarsu me karfi, hajiya maryam tanada karatu me zurfi a fannin likitanci, dan hk Alhaji muhanmad ya bude mata dankareren asibitin ta ne suna Mariam hospital a nan garin kano, ALLAH ya azurtasu da yara biyu Wato AB'ILAL wanda yaci sunan mahaifinshi kuma mahaifin hajiya maryam wato Muhammad shine suke kiranshi da AB'ILAL, se Salwah wadda taci sunan Rukayya wato sunan mahaifiyar Alhaji muhammad kenan. Se bayan va ransa aka haifi salwah. Alhaji Abubakar ya rasu bayan yasha jinya kusan ta watanni biyu, sun kwanta asibitoci da dama har ALLAH ya amshi rayuwarsa, ya bar hajiya maryam da tsohon ciki, rnr tayi nakudar dole. AB'ILAL yayi kuka kmr ransa ze fita har seda yayita suma, zan ita cewa ma yafi hajiya maryam shiga damuwa a rashin mahaifin nasa saboda sun shaku sosai fiye da yadda suka shaku da mahaifiyarsa hajiya maryam domin kuwa ita macece me zafi sam babu wasa a lmrinsa a ynzu nema har danta keshan ruwa a gabanta sanadiyyar rashin mahaifin nasu. Amma dukda hkn sam Salwah bata saba da mahaifiyar tataba sbda bata janta a jiki kwata-kwata dan hk tafi zama a gidan kanwar mahaifinta Hajiya badiyya wadda ke zaune a garin kaduna tinda ta gama secondary ta koma can dindin din da zama a can taci gaba da krtunta na gaba da secondary, se weekend take zuwa ta kwana biyu a daddafe ta koma kaduna gidan hajiya badiyya. Maza da dama sunyita kawowa Hajiya maryam hari byn rasuwar me gidanta Amma fir bata saurarensuba, taci gaba da riqe mutumcinta tana Aikinta a asibitinta cikin aminci , daga ita se AB'ILAL suke zaune a gidan se ma'aikatan dake musu hidima, tin Rasuwar mahaifin AB'ILAL hajiya maryam ta matsa kan AB'ILAL yayi Aure ta hadashi da mata Sunfi goma amma karshe dacin mutumci suke rabuwa, daga wadda zewa zagin kare dangi se wadda zemara ko yamata dukan tsiya, wai acewarsa basu da tarbiyya , Yawancinsu suna cewane suna sha'awarsa shiyasa yake dukansu, ko su taba masa jiki, kasancewar shi din me kyau be, dole duk isashshiyar mace taji sha'awarsa. Dalilin dayasa ya karyama Hameedah yar mataimakin governor haannu yau saboda takai hannunta kan jikinsa kuma tayi kissn din kumatunsa shine ya mammareta ya murde mata hannu har seda ya karye kana yabarta, a ganinsa yar iska ce daman tana bin wasu mazan suna kissn juna shi abindama yasawa knshi an taba ciccin gindinta, abinda AB'ILAL yafi tsana a rayuwarsa macce mara tarbia, ko lbrin macce mara tarbiya yaji se yaji duk duniya beda wadda ya tsana kmr ita, da ace ze gantama ze iya kasheta, zan iya cewa ma AB'ILAL ya tsani mata tin tasowarsa har zuwa ynzu, a halin ynzuma daya mallaki hnklinsa seyafi tsanar mata fiyeda duk tunanin me hnkli, AB'ILAL yanada tsananin kyau na fitar hankali, shi din dogo ne Na bugawa a mujallah, sannan baki neshi wuluk domin Mahaifinsa ya dauko a duhun fata, sede kamanninsa sak na hajiya maryam ne, AB'ILAL yanada kyau fiye da yadda nake misalta muku, ynada dogon hanci bakinsa dan karami ne sannan ja jawur yake, yanada dara-daran idanuwa masu kashe idanuwan me kallo, yanada yalwar gashin gira, infect de shi din gargasane. Wani irin kayataccen saje yayiwa fuskarsa kawanya, fans shidin kyaunsa na tayarda sha'awar manyan matane, domin kananan mata basu isa su kalleshi bama, dan suna iya mutuwa da tsananin sha'awah nan take. Kasancewar yanada kirar karfafan maza domin kirjinsa a bude yake dukda baya cin karfe, kawai halittarsace hk, shidin faffadane, tako ina jikinsa a bubbude yake, kallo daya zaka masa ka gane inya riqe kato seya girgiza, wasu lokutan wasuma na tunanin shi din soja ne, nanko shahararren dan kasuwane, wanda aka sanshi a garin kano fiyeda tunanin me lissafi, sannan an sanshi a garuruwa da dama A fadin nigeria. AB'ILAL beda kiba sosai jikinsa
Chapter 12 · 0% Book details