Sashe 44
Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ranar talata Alhaji Murtala ya nufa garin Kaduna tin 10:am ya taso, yayinda Muhammad ne ke driving dinsa, har suka isa garin Kano 12:pm suka shigo kaduna. 12:32pm Muhammad yayi packing katotuwar mota irin ta daukan governors a gidan hajiya maryam, daman already Alhaji murtala ya sanar da maryam zuwan sa a yau din, dan hk bata fita ba, dukda kuwa tanada operetion a asibitinta amma sam bata fita sbda murtala ya sanar da it akwai muhimmiyar mgnr dazeyi da ita. Jin packing din motar tasa yasa hajiya maryam da Salwah fitowa daga cikin falon, suka nufo compound kowaccensu fuska dauke da annashuwa, hajia maryam sanye take da rigar abaya kalar dark brown ba karamin amsarta tayi ba abnka da farar mace alkyabbar mata, ta yane kanta da mayafin abayar ba krmin kyau tayi ba kai kace yar 30yrs ce se ynzu na tabbatr da ita din benu ce bata tsufa sede ta sake sabon gashi. Autarh Salwah kuma sanye take da riga da zanin atamfa, burguzuma burguzuma kmr dinkin tsoffi, har wata rama tayi duk tabi ta kosa hutunta ya kare ta koma kd da zama ta ci gaba da walwalarta yadda takeso. Ta daure kanta da dankwalin atamdar dukda burguma burguzuma din kayan datasa surar jikin da ALLAH ya mata bata boyu ba, seda ta bayyana knta, shiyasa kullum cikin fada suke da Amihh ita ganinta matsatstsun kaya ne take sawa nan ko kirar jikinta ne hakan komi tasaka siffarta bata boyuwa. dukkanisu kafafuwansu sanye suke da plat shoe masu nugun kyau da tsaruwa ga uwa uba kuma tsada, classic shoes ne a kafafuwansu , yayinda kafafuwan nasu keta walwali, zallar hutu kawai. Fuskar hajiya maryam sanye da farin siririn glass suka karaso bakin motar inda Alhaji babba tini ya fito daga gidan baya daman a nan yake zama ko wate kuwa zeyi driving dinsa be zama gidan gaba. Muhammad daya bude masa murfin ya fito se rissina masa yakeyi. idanuwan alhaji murtala suka sauka a kan salwah ya washe baki cike da farin ciki, ya bude babbar rigarsa kasancewar mnyan kaya ne a jikinsa wata danyar shadda ce kalar milk tasha aiki na fitina, ba krmin kyau tamsaba. Yana bude hannayensa Salwah ta shige jikinsa zucia cike da kaunarsa shima yana mugun sonta kuma yana nuna mata kulawa, bata wani jima a jikinsa ba ta dago sbda tunawa da tayi da kashedin da hajiya maryam ta taba mata kan kada ta rinka jimawa a jikinsa inma ya zama dole se ya rungumetan a matsayinsa na ubanta domin kuwa zucia bata da kashi a cewar hajiya maryam. Murmushi Salwah ta sakarwa alhaji murtala ta rissina ta gaidashi ya amsa zucia fal kaunarta data gaza boyuwa seda ta bayyano kan fuskarshi, sosai alhaji ke kaunar yayan kanin nasa. Muhamnad dake sanye da kananan kaya ya karaso ya rissina ya gaida hajiya maryam wadda keta barin murmushi a kn fuskarta amma be kai zucia ba hk kawai 2days dinnan tana yawan jin faduwar gaba. Amsa gaisuwar Muhammad tayi zucia cike sa kaunarsa. Muhamnad da salwah suka ja gefe suka hau aikin gaisawa a matsayinsu na yan uwa. Hajiya maryam ta gaida alhaji murtala ya amsa cikin farin ciki idonshi na kan hajiya maryam yayi Murmushi kana yace "likita bokan turai..." A wannan karon murmushi sosai hajiya maryam tayi kana tace "Alhaji babba mu shiga ciki..." Ba muau Murtala ya fara takawa zuwa cikin gidan Hajiya maryam ta kalli su salwah da Muhammad daketa ma junansu murmushi tace "to ku ku shigo ciki, tinda de gida muke ba jejiba, balle ayita tsayuwa..." Salwah da Muhammad suka mara musu baya, yayinda alhaji Murtala ke gaba maryam na biye dashi se su salwah da Muhammad dake bynsu a jere suke, a hk suka karaso cikin kayataccen falon hajiya maryam, se uba kamshi da sanyin AC kawai ke tashi. A kan kujerar 3sttr alhaji babba ya yada zango ya cire hular dake knsa ya ajiyeta a gefensa ya sauke ajiyar zucia. Muhammad zaunawa yy a kasa domin su a tarbia basa zama kn kushin in manynsu na kai sede ko inda izinin manyan nasu. Salwah kam kiching ta nufa. Hajiya maryam dake tsaye ta zubawa Muhammad dake zaune a kasa ido, tace "Alhaji ka hau kan kushin mana alhajina..." A kunyace Muhammad ya tashi ya zauna a kn kushin 1ct Hajiya Maryam tayi murmushi tanason mutum me tarbia ko babba ko yaro ta tsani ganin mutum mara kunya ko ince mara tarbia. Sannu da zuwa hajiya maryam keta jerowa alhaji murtala shikam se aikin amsawa yakeyi yana Murmushi, itana ta juya ta nufa kiching din dan gababar musu da abinsha. Tana shigowa kiching din taga salwah da masu aikinta guda biyu sunata koqarin shirya abubuwan motsa baki a kan tamfatsa tamfatsa din trea na alfarma. Haji maryam ta rufesu da fada musammanma salwah cewa takeyi wai ta cika yin abu a hnkli, hkri kawai salwah ta shiga bata, domin fadan nata ta inda take shiga bata nan take fita ba wai meyasa tin dazu datace a shirya ba a shirya ba, se ynzu da baki suka riga suka iso, daman ita maryam hk take sam ba a iya mata, shiyasa wasu lokutan da knta take Aikace Aikacenta musammanma girki, ko salwah tace zata tayata to fa se sun babeh inma ta tayatan. Manyan trea guda uku aka cika kusu da jayan motsar baki da drinks Salwah da ma'aikan suka dauko trea din zuwa falon, suka ajiye ma kowannensu a kan dan table din dake gabansu, domin kowanne da table a gabanshi hk tsarin kujerun suke, sede gefen hannun kujerun ake ajiye tables din kowacce kujerar. Suna ajiyewa suka juya suka koma kiching Salwah kuma ta nufa bedroom dinta. Hajiya maryam ta karaso ta zauna kan kujerar dake facing alhaji babba se kara jero masa sannu takeyi. Shi kuma yana aikin amsa. "Ina wuni Alhaji babba bamu gaisaba.." Hajiya Maryam ta koroma alhaji babba gaisuwa, murmushi alhaji yayi yace "Mun gaisa mna amma yawan gaisuwa ai yafi yawan fada...lafia lau..." Ya amsawa gaisuwar tata a karshe still fuskarsa dauke da murmushi, Hajiya Maryam se binsa takeyi Da ido ta fara mamakin wannan fara'ar tasa domin bata taba ganin fara'arh irin ta yau ba a kn fuskarshi. "Tabbas da walakin goro.a miya.." Hajiya maryam ta fadi a ranta. Nan suka hau dan taba hira sunayi su kuma suna motsa bakinsu da abubuwan alatun dake gabansu. "Maryamu ya fama da Aiyuka?'' Alhaji murtala ya jefowa Hajiya maryam tambayar. Hajiya maryam ta amsa da "Alhamdulillahi Alhaji..ya iyalin kuma?" Alhaji murtala yace "Iyalina lafiarta lau, zainabu abu ba, tana gaidaki, daa ta nace ma se munzo tare Amma ALLAH be nufa ba, na bata hkri karamar yarinya ce sam bnso ta wahala..." Ya karashe mgnr tasa yana murmushi irin nasu na manya, hajiya maryam ta zubawa murtala ido, ita abu daya ke bata haushi dashi shine yanada budurwar zucia ynzu wai a gaban dansa yake fadar wannan mgnr rausayar da kai gefe hajiya tayi tana gyara glashin dake kwayar idonta zuciarta cike da takaici. "Waishin maryamu rashin Auren nan be damunki, naga ai har ynzu da sauranki, ko yayane ai kina da buqatar dana miji...." Alhaji murtala ya sako wannan mgnr dmn shi ba kunya bace a idonsa, iri irin wadannan maganganun duk haka yake tsakowa maryam su sede in basu hadu ba. A wannan karon seda kunya ta kashe maryam sbda yadda yy mgnr a gaban Muhammad wanda yayi kasa da knsa sbda ya fahimci zahirin mgnr. Hajiya maryam shiru kawai tayi tabi Alhaji da ido shide kullum ba girman sede na jiki, ta fadi hkn a ranta. Muhammad mikewa yayi a kunyace ya nufa hnyar dayan falon da wayarshi a hannunshi kirar iPhone yayi dealing number din Salwah yace tazo dayan falon ta samesa suyi hira. Bayan barin muhammad falon Hajiya maryam tayi jim idanuwanta na kan Alhaji murtala ba karamin ddh taji ba da muhammad ya tashi ya fita a falon, sbda alhaji murtala ya rinka sako zance kenan harse illa masha Allahu, ita kuma duk ta k'agu ya sanar da ita dalilin zuwan nasa. Jim alhaji babba yayi da tuffa a hannunsa kallo daya zaka masa ka gano akwai dattako a bayyane dashi, ajiye sauran tuffa din yayi a kan trea din kana ya fara gyaran murya cike da dattako. Hajiya maryam ta natsu ko motsi batayi ganin alhaji na qoqarin fara mgna, a jiikinta kawai taji mgnr babba ce, tindaga zuwan da yayi da kanshi ta yadda mgnr ba karama bace.
*paid book ne....08136349646*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GiclAKDbf2h19M4nZIpDfl
BBM TRUSTED PRE ORDER. Muna yin order na kitchen item, shoes, bag, veils, abayas, bag to school, lace , atamfa .E.T.C
Muna kasuwanci cikin aminci da storon Allah duk wanda yayi business damu inshaallahu zaiji dadi 馃拑馃拑馃拑.Idan kuma kuna bukatar ayi maku order na wasu kayan wanda kuke bukata duk muna yi.A kaduna nike zaune unguwar rimi zaku iya zuwa gida ko shago ku same ni 馃榾馃榾.Domin karin bayani ku tuntube ni a 08068655941 sai na jiku馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑
08/01/2022 脿 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟
*YAR DANDI CEH*
馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟
(SHE'S A WORLDLY PERSON)
*paid book ne....08136349646*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GiclAKDbf2h19M4nZIpDfl
BBM TRUSTED PRE ORDER. Muna yin order na kitchen item, shoes, bag, veils, abayas, bag to school, lace , atamfa .E.T.C
Muna kasuwanci cikin aminci da storon Allah duk wanda yayi business damu inshaallahu zaiji dadi 馃拑馃拑馃拑.Idan kuma kuna bukatar ayi maku order na wasu kayan wanda kuke bukata duk muna yi.A kaduna nike zaune unguwar rimi zaku iya zuwa gida ko shago ku same ni 馃榾馃榾.Domin karin bayani ku tuntube ni a 08068655941 sai na jiku馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑
08/01/2022 脿 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟
*YAR DANDI CEH*
馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟
(SHE'S A WORLDLY PERSON)