← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 225

Sashe 163

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Paid book ne...*08136349646*
08/01/2022 脿 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 49

Abu kmr wasa, salwah ta daukewa hilwah kafa kwata kwata a yan kwanaki biyun nan, ita da ita sede gaisuwa Tasa hilwah a dogon tunani kn meta mata, amma ta gaza gani meta matan....yau tsawon Kwanaki hudu kenan suna wannan yanayin , hilwah ta sameta ta tambayeta kn meta mata take ta faman daure mata a kwanakinnan..", salwah tace mata ba komi,..." Inside haushi ya kara kashe salwah kn duk bacin ran data rinka nuna ma hilwah bata gane ma inda ta dosa ba, kawai ta barta ta kara fita a harkarta, basu ma wani zama a gidan kullum suna mkrnta ko zaman gidan ma basu yi, in suka fita tin safe se 6;pm duke dawowa wasu lokutan kuma 5:pm kasancewar sun kusa fara exam ne shiyasa knsu ya fara zafi, ko a mkrntarma sama sama suke da salwah amma sam salwah bata bari a fahimci hkn... A bangaren gogan ma basu haduwa ko ganinta ya bayayi gashi ta riga ta lasa masa zumar nonon dadih, a bakinsa duk yabi ya kara haukacewa ya birkice a yan kwanakin nan, ya zama kmr zautacce, har yar rama yayi ko yazo side din Amihhn baya ganinta, da safe ko rana da daddare daya shigo side din Amihh seta koraresa, tace karya kara shgo mata side amma yaki daddara da zuwa dukda wulakncin datake masa inya shigo mata side dinta amma kullum seyazo 2tyms 3tyms, suna haduwa da salwah amma sam be ganin hilwah wasu lokutan se yaji kmr ya tambayi Salwah ina yarinyar amma se yaga kmr inyayi tambayar girmnsa ze zube, dole take sawa ya hkra ya dawo side dinsa jiki ba laka sbda bega abincn ruhinsa ba ... A bangaren Amihh kam da zallar haushinsa a ruhinta , sbda duk abubuwan da yake ma hilwah tasani ta hnyar CC camera datasa a side din, hatta da barin ta da yayi ta kwana a wajen compound, rnr data dawo daga side dinta, Amihh ta sani ta kira Hajiya Juwairriyya ta sanar da ita, sbda ta nemeta da sha'awara kafin rasa CC din, ta gaya mata zata saka CC camera a side din AB'ILAL din, hajiya Juwairriyya tace kar ta saka ay zaman Aure ya gaji hakuri hadi da jarabawa dogon bincike beda kyau...", amihh tace bazata iya hkn ba sbda soyayyar yarinyar tada bance a zuciarta, shine daga bisani hajiya Juwairriyya tace shikenan ta saka CC din, amma ta jure komi zata gani ta CC din... Amihh tace shikenan zata jure
.. Da abubuwa marasa kyau suka biyo baya Amihh ta sanar da hajia Juwairriyya, na farko kn Ab'ilal ya bar yarinyar ta kwana waje hajiyar tace tayi hkri ta batta kuma kar ta nuna komi wata rana se lbri ita jarabawarta kenan ta Aure,,,se amihh ta daurewa ranta, duk rnr weekend seta bude CC din taga halin dasuke ciki kuma ta gayawa hajiya juwairiiyya ita ke tausarta, hadi da shawarwari, dabadan ban baki da hjya Juwairriyya ke ma hjya maryam ba da tini ta dawo da hilwah side dinta, tin karon farko,, a wannan karan ne daya mareta yayi na karshe Amihhn bata nemi shawarar kowa ba ta dawo da ita side din nata, hatta da farkon fara tabata da yy a falonsa Amihh na ta gani ta CC din, ita a rainin hnkli ta dauki hkn gani takeyi be sonta amma yanason albarkatun jikinta, sbda jikinta najan hnklin d'ana miji ne,, Akwai wani abu na sirri da amihh ta barwa ranta zuwa wani dan lokaci, shine seta raba Auren sbda a ganinta hkn ne masalaha, Amihh na ganin ta rabasu kowa ya auri wanda ransa keso,, musammanma da Amihh ta fahimci alhasan nason hilwah kuma sun shaku, a yan kwanakinnan ta ankara da hkn, sam Amihh bata dakatar da Alhasan ba na soyayyar hilwar da yakeyi... ta dauki aniar zatasa ab'ilal ya saki hilwah kawai se ta hadasu auren da ita da Alhasan sbda dukkaninsu ta isa dasu, in bayaso se a dauka a bawa meso, Amihh nada haushin AB'ILAL kuma tayi alqawarin seta hukuntashi a lokacin da bazeso karbar hukunci ba, ynzu de ta barshi shima ya mori lokacinsa..

Alhamdulillahi sunyi exam lafia yayin da suka karkare lafia, suka tafi hutun 2week. Hajiya karama dasukayi waya da Amihh take tambayarta ya su salwah da sirikarta hilwah " amihh ta amsa ta dasuna lafia qalau..." A nan Amihh ke sanar da ita ai sunyi hutu a scul ma na 2wks,...'' Hajiya karama taji ddn hkn, ta roki alfarmar kn amihh ta barsu suzo gidanta suyi hutunsu a nan, amihh tace a'ah sede suje su wuni su dawo .." Nan hajiya karama ta cikata da magia kn ta barsu suyi hutunsu a gidanta, koda na 1week ne,, badan Amihh taso ba, ta amince da hkn washe gari tace salwah da hilwah su shirya suje gidan hajiya karama gobe amma 1week zasuyi su dawo, hilwah da salwah dmn sun gaji da zamansu daya farin ciki ya rufe zuciyoyinsu,, nan suka hada yan kayayyakinsu da abubuwan dazasu bukata a akwati, washe garin har bakin mota Amihh ta rakosu 10:am, suka shiga mota Amihh ta misu fatan dawowa Lafia , dan ustaz yajasu suka fice a gidan, Zuciyar Amihh cike da kewarsu ta juya ta koma cikin falonta tasan zatayi kewarsu sosai a 1week din daza suyi basu nan.
Chapter 163 · 0% Book details