Sashe 222
Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Amihh salwah hadi da gogan suka zubo musu ido dauke da mamaki hadi da alamar tambaya, musammanma dasukaji sunan da Sir Abrah ya kira hilwah dashi, duk fa akasa rayuka ukunnan a wani yanayi hadi da jefasu a zurfin dogon tunani me tambarin nazarirrika, suka kara kuresu da ido kmr sunga wata sabuwar halitta. Hilwah da jikinta ya fara rawa ta tsure Abrah da kwayoyin idanuwanta da tini suka ciko da kwallah ta shiga tunano rayuwarta ta baya. Abrah mutuwar tsaye yayi hadi da kara matsowa dan kara tabbatarwa da idanuwansa Princess dince yake gani ko gizau take masa daman ta saba masa hakan sbda da soyayyarta a ransa har ta kawo zuwa wannan lokacin. Ganin Abrah na kokarin matsowa sosai kmr zasu hade da junansu yasa ab鈥檌lal hade rai kamar an masa aiken mutuwa, shi yama fara zargin anya Abrah ba tsohon dattijon dan iska bane, sbda yasan halin bature da son matan tsiyya, yana kokarin matsowa ya jawo hannun hilwah su fice a falon Abrah ya zube kasa hadi da miko ma hilwah gaisuwa ta girmamawa,, tohfa a nan hankalin kowa ya kara rikicewa ganin babban mutumin ya zube kasa a gaban hilwah, ab鈥檌lal kam ai sumar tsaye yayi ya dakata daga abinda yayi niya, hilwah ta dago ta kalli halittu ukun da suma suka zubo mata ido da Abrah dake tsugunne gabanta. Hilwah ta dawo da dibanta ga Abrah cikin wani harshen turanci tace 鈥淚na mommyna?鈥� Abrah dake tsugunne gabanta yayi zaman dirshen a kasan falon kawai ya fashe da wani irin kuka me tattare da tausayi hadi da zallar dumbin dmwa me tamfarin daukewar farin ciki a lokaci kankani. Jikin ab鈥檌lal amihh salwah da duk suke tsaye ya karayin sanyi suka kara shiga rud鈥檃nin me dumbin yawa, amihh ce kadai take iya tunani a cikinsu amma kaf tunaninsu ya tsaya, sbda rikice da mama Kim dasuka shiga musammanma ab鈥檌lal Wanda yabi kowa mamaki Uban dakinsa yau shine a kasa a gaban iyalinsa hilwah, lallai akwai boyeyyen Al鈥檃mari. Amihh kam tunani ta shigayi kode shine mahaifin hilwah, to se kuma ta kara shiga rikici sbda tsugunna matan da taga yayi. 鈥� ta Yaya uba ze tsugunnawa yarsa?鈥� Tayima zucia da tunaninta wannan tambayar. 鈥淧ls Ina mamana? Ko wani abu ya sameta?鈥� Hilwah tayi magnr cikin harshen nasara kwalla na zirya a kuncinta. Abrah ya kara fashewa da kuka hakan ya bawa hilwah tabbacin akwai matsala, nan take itama ta fashe da wani matsanancin kuka. 鈥� iyaye na basa raye kou? Jikina na bani hkn tin tini鈥︹€漷a Fadi da harshen nasara yayinda turancinta ke fita sak na turawa, zuwa ynzu ab鈥檌lal da hjya maryam da salwah sun fara fahimtar wasu abubuwa hamdala ga ubangiji hjya maryam tayi, shi kam gogan kukan datakeyi ne ya daga masa hnkli sbda be Damu yasan ko ita wacece ba, shide kawai yasan yana sonta koda kuwa bata da iyaye shide ynaso a hk musammanma dayaci gindi ai ynzu ma kiris yake jira ya fara bin ti-ti a kan son da yakewa yarinyar ko ganinta yayi se yaji wani sanyi kmr kansa ze fashe inya kalleta ya tuna wannan sama da kasan fa da d鈥檃n tulluwarnan me kacia duk nasa ne, shi ynzu kukan datakeyi ma har ga kasan zuciarsa yake jinsa. Abrah na kuka yace cikin harshen nasara 鈥渨uta ta kama da gidan Sarki Jon mun rasashi mun rasa gimbiya gabaki dayansu!,鈥� ya karashe muryarsa na sarkewa yayinda klmn dake bakinsa seda suka fito kana ya iya fahimtar be dace ya fadesu ba sbda sunyi tsauri dayawa. 鈥淚nnalillahi wa鈥檌nna ilaihirraju鈥檜n!鈥� Ta fadi cikin gigita da dimauta, dukda bata gama fahimtar Inda kalamansa suka dosa ba amma zuciarta na kara fahimtar da ita zubewa kasa tayi a sume nan take numfashinta ya fara kokarin daukewa ab鈥檌lal ne first daya fara yo knta gadan gadan hjya Maryam da salwah suma suka iso cikin tashin hnkli Sir Abrah kam ya Gaza ko kwakwaran motsi, kukansa se tsananta yakeyi zuwa yanzu harda majina. Ab鈥檌lal ya shiga girgizata yana kiran sunanta amma ina ji kake tsit ta sume , ganin hakan yasa amihh isa ga frij din gidan ta Ruwa me sanyi na gora a gigice take ta karaso ta bude ruwan gorar ta fara yayyafa mata, salwah se kuka takeyi abii ma kukan yake shirinyi harya fara kitsima irin bura ubar daze ma abrah inya kashe masa mata. Seda amihh ta wuce 15mnt tana Watsa mata ruwa Kana aka samu ta farfad鈥檕 abii ya jata jikinsa ya rungume se aikin shashshekar kuka takeyi kmr numfashinta ya dauke kai da ganin irin kukan datakeyi zakasan kuka ne me cike da kuna da rad鈥檃d鈥檌 . Amihh ta zauna ta zuba mata ido a gaskia tanason sanin wacece hilwah. 鈥� Dan Allah yau ki gaya mana wacece ke sweetheart.. ko a yaya kike wlhy zuciyoyinmu na cike da kaunarki da zallar begenki..鈥� cewar amihh. Salwah dake staye ta zauna, ta zubawa hilwah ido wadda keta faman kuka kmr ranta ze fita. Hilwah data tsure amihh da ido ta kara fashewa da wani irin kuka. Abrah ma kukan yakeyi amma mara sauti, ab鈥檌lal kam ranshi a bace yake da ogan nasa, sbda shi ya rikita masa lissafin mata. 鈥淎mihh Dan Allah ki tambayarmin Small daddy da gaske ne Iyayena sun qone sun mutu? Pls kar yacemin da gaske ne pls wlhy Ina sansu duka zan koma garesu Dan Allah a temakamin ace suna raye pls..鈥� a yadda take mgnr ze tabbatar mka data zama kmr zararria, ab鈥檌lal ya shiga wasu tunannika tabbas datana asibiti ogan ogansa ya rasu ta hnyar kamawa da wuta da mahallinsa yayi, baya tunanin shine mahaifinta sbda be cancanci hakan ba. Amihh ta kula da kmr zaucewa hilwah ke nemnyi dan haka ta matso ta dosa mata karatuttuka na alqur鈥檃ni me girma tana tofeta dashi a haka har ta fara samun nutsuwa kadan kadan na dirar mata. Ganin ta fara samun natsuwa yasa amihh ta koro mata da natsiha. 鈥� haba hilwah kefa musulmace, muusulunci hkri yake koyarwa da dangana da tawakkali, wajibine duk musulmin kwarai ya zama me wadannann nasabobi sannan ya kara da tawakkali Ga ubangiji mahallici dan Allah kisawa ranki tawakkali shine cikar musulmi yadda da kaddara me kyau ko mara kyau, komi da kk ganinsa rubutacce ne ga ubangijinmu鈥︹€� hilwah taji zuciarta ta fara natsuwa ainun da tinatarwar da amihh ta mata cikin muryar natsiha, ta sauke gwauron numfashi tana me ambato ayoyin ubangiji hadi da salatuttuka ga ma鈥檃iki salallahu alaihi wasalam, a hnkli taji nutsuwarta ta dawo amma ba dai-dai ba, ta tuna da uwarta mahaifiyya kawai hawaye Masu mugun zafi wadanda suka taso daga zuciiarta suka ci gaba da biin kuncinta. Abii ya kara rungumeta tsam ga jikinsa, ya shiga rada mata wadansu klmai a zucia wadanda bansan me yake ce mata ba, zuwa can de hawayenta suka tsagaita amihh ta juyo ga abrah tace " dan Allah ka gaya mana meke faruwa鈥�" cikin harshen turanci tayi mgnr. Abrah yayi jim zuwa ynzu hawayensa ya tsagaita se goge face dinsa yakeyi da tissues ya Gaza mgna yayin da falon ya dauki tsit bakajin Komi se sanyin AC hadi da numfarfashinsu. Sunfi karfin 1h a hakan amihh ta kure hilwah da ido wadda zuwa ynzu batajin dadin duniar ma kwana kwata adduah kawai takeyi a ranta Allah yasa mafarki ne lbrin konewar iyayenta bawai gaske bane. 鈥淜u cire mu a duhu pls鈥︹€� amihh ta fadi cikin harshen turanci, hilwah ta kureta da ido, ta nisa ta numfasa tabbas tasan bazata iya bada lbrin knta ba a irin wannan halin da take ciki. Amihh ta kula da hakan ta juya ga abrah tana me neman karin byani ta rufesa da magiya a nan ya fahimci basusan lbrin hilwah ba. Numfasawa yayii cikiin harshen nasara ya fara jero musu bayani kasancewarsa na babban yaro ga King Jon babban sarkinsu kenan sunaji dashi yaynda wasu ma suka maidashi kmr wani abin bauta sbda tsabar girmamawa (astagfurillah). Abrah ya shiga basu lbri sbda yasan komi na king Jon sunansa ne king din ubansa ne jon din. Mahaifinsa wato jon haifaffen dan amurka ne wanda ya tashi ya gaji sarauta a gun iyayenaa, su sun karance basu da addini wato su mutane ne wadanda basu da addini. Allah ya azurta iyayensa da zallar dukiya wadda baki baze iya fadarta ba, Anyi zamanin da duk fadin dunia babu wanda yakai jon dukiya, ga kudi ga mata iri daban daban matan nasa sunfi dozing dari, sede duk cikinsu yafison mahaifiyr jon wadda ake cewa Princess jel , jon ya kasance be haihuwa seda ya tsufa dukuf sannan ya samu haihuwa daga jel dalilin dayasa yake sonta kenan, ta haifa mata danda namiji , sarki yayi Murna a ranar haihuwarsa yasa mata suna king beda wani suna se king, , king ya tashi cikin soyayyar mahaifinsa da zallar mulki da izza , mutane na girmamasa hkn ya samo nasaba ne daga girmama iyayensa da akeyi har haknma ya sabawa ubangiji kasancewar sa shi beda addini. Tare da king muka tashi amma ni na kasance dane ga baiwa se Allah ya hada jinina da King komi tare mukeyi, nasan komi na king komi yake ciki na sani be boyemin komi, a hk har mahaifinsa ya rasu byn doguwar jinya, krmn hauka jama鈥檃n gari sukayi sbda sunji dadin mulkin jon matsalarsa daya da beda addini amma yanada adalci ga talaka . King kam kusan zarewa yayi, ba Jimawa da rasuwar mahaifinsa Allah ya dau ran mahaifiyara, mulki ya zamana a hanun king iyayensa sun mutu sun bar masa dukiya na fitar hankali d gigitar lissafi. King ya tashi cikin gatar kudi da dukiya sede ba iyaye, yagaji mahaifinsa a mulki sede adalcinsa kadan ne, naman mutane shine abncinsa, sam ransa babu imani ko miskala zarratin, ba ruwansa da mace, yafi tsanar mace a kn Komi. Muna tare dukiarsa se habbaka takeyi ya shahara a mulki ya dawo ya shahara a kswanci ya rike mukamai iirii daban daban a kasar amuka. King yanada 30yrs sam ba ruwansa da mace , a haka wata rana kswanci ya kaimu kasar Larabawa, king ya hadu da mahaifiyr hilwah, yana ganinta Allah ya jarabceshi da zallar sonta a bakin titi muka gnta cikin shigar isilama wato na musulunci Allah yasawa yarinyar zallar kyau a lokacin bata wuce 15yrs ba. A hmkli a hnkli seda jon ya shawo kn wannan kyakyawar yarinyar me suna rukayya,, yace ze aureta ta gabatar dashi ga iyayenta sbda knkntar shekarunta bata damu da kasancewar king mara addini ba, sbda Bala鈥檌n sonshi da Allah ya jarabceta dashi. Iyayen rukayya wadanda duk musulmai ne suka ki aminta da aurawa yar su da king sbda beda addini, rukayya taki fahimtar me suke nufi ta bijire musu byn taci duka a kn ta rabu da king taki rabuwa dashi, a karshe ta kwashe komi nata ta gudu ta bi jon rnr aka daura musu aure irin yadda suke nasu auren kasancewarsa mara addini kawai yace ya aureta ne a baki, ya gina mata gida da zallar gold rukayya batasan hk yake da kudi ba se a lokacin sbda ita ba kudinsa takeso ba shi din takeso, can ta bar mahaifiyarta da mahaifinta da kuncin rashinta mahaifinta kam tini ma ya cireta a jerin yayansa daya haifa da cikinsa, mahaifinta balara be ne mahaifiyarta kuma ba indian ce.