← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 225

Sashe 117

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Amihh ta kira salwah tace su fita wajen compound kawai su jirashi, salwah tace to suka tsinke wayar. Suka fito farfajiyar gidan kafafuwan hilwah sanye da plat shoe dark peach irin aikin dake wuyanta, ba karamin amsarta takalmin yayi ba, kafarnan luguf luguf kmr a tsugunna a lasheta tass dan kyau. Suka fito suka tsaya babu gogan babu dalilinsa, salwah se faman tsuki takeyi, har suka gaji da tsayuwwa, salwah ta kawo musu kujera irin na hutawarnan suka zazzauna , hilwah kam tini knta ma ya fara ciwo, har kusan 30mnt suna zaune be fito ba, salwah ta kalli hilwah tace "ko de zamu koma ciki ne, yah AB'ILAL dan wulaknci ne yana can yana yauki da wuya ma in zezo wlhy, wannan Ai wulaknci ne...mtwss!" Ta karashe mgnr da jan guntun tsuki. Hilwah de knta na kasa tana wasa da zoben gold din hannunta ita knta abun ya bata mata rai, kuma ya tsaya mata a zucia. "Tashi mu koma ciki..." Salwah ta fadi hadi da jan hannun hilwah suka mike suna niyar fara tafia, suka tsinkayi tahowar gogan kmr baze taka kasa ba yafi mace yanga da iya tafia me daukar hnkli, kallo daya hilwah ta masa taji wani irin yanayi a jikinta dan hk tayi hnzarin dauke kwayar idonta a kansa. Salwah kam sbda tsoro ko cikakken kallo daya ma bata masa ba ta dauke knta. Dukda ya gansu amma ya basar kmr ba mutane ya gani ba, ya nufa motarsa ya bude ya shiga, salwah ta rako hilwah har bakin motar ta mata fatan dawowa lafia bata tsaya taga shigarta motarba ta koma cikin gidan. Zuciar hilwah na dukan uku uku sbda tsoronsa dake ranta, takai hannu ta bude handle din baya ta shiga kamshin turarensa hadi da Sanyin AC suka daketa seda ta lumshe ido, ta jawo murfin ta rufe knta na kasa ko kallon inda yake bata yiba, shiko gogan tin tana wajen sadda salwah ta rakota bakin motar, yake kallonta ta ciki, kasancewar bakin glashi ne da motar, kur ya kureta da ido seda ta shigo motar sannan ya koma kallonta a sace, kamshin turarensa ya cika masa zucia da hanci, rigar dake jikinta sosai yaketa kallonta a sace, rigar jikinta ta masa kyau sosai, se yaji a ransa beso tazo ba hijjabi ba, se kuma zuciarsa ta sanar dashi ai ta saba yawo a sirara sirara ma danma yanzu an samu arziki ta sitirta knta da jallabia. barin kallonta, yy, ya hade rai Ganin ta shiga baya ba karamin haushi ya bashi ba, wato ma ta maidasa dreva dinta, rannan nasa baki kirin ya juya motar ya fice a gidan,duk knta na kasa sam taki yadda ta dago knta ma ta kalleshi, shiko time to time yana dan satar kallonta ta cikin mirror, a hk har suka isa asibitin Yayi packing yaki fitowa, hilwah ta bude ta fita, ta tuna da sun taba zuwa asibitin ita da Amihh a ranar data daukota daga gidan dandi. A hnkli take takawa ta shiga cikin asibitin ta rasa ma ya zatayi, gashi ba waya hannunta kuma batasan ta ina zata fara neman Amihh ba a tamfatsetsen asibitin. Ta shiga asibitin ta hau aikin zagaye yayin da kowa keta aikin gabansa, hilwah ta kai 20mnt tana zagayen asibitin, kawai se ta tuna da sunan amihh data taba gani a rigarta ta likitoci wata rana data dawo daga aiki. DR MARYAM M.A shine sunan data tuna,na jikin rigar tata, godia tayi ma ALLAH domin ta gaji da zagaye sbda jikinta ba cikakken kwari.Ta tari wata nurse Christan, cikin harshen turanci ta tambayeta ina ne office din DR MARYAM M.A. nurse din ta mata jagora zuwa har office din Amihh ita a Zatonta ko hilwah yar Amihh ce. Hilwah ta mata Godia bayan ta rakota har cikin office din Amihh, nurse din ta juya ta fice a office din. Hajiya maryam tayi gaggawan sallarmar patient din dake gabanta, tace a dakatar da wasu, kafin ta gama uzurinta. Amihh ta taso daga kn kujerarta ta karaso inda hilwah take fuskarta dauke da fara'arh da murmushi, ta zauna gefen hilwah, kasancewar kujerar 2ct ce, office din babban office ne irin na mnyan likitoci da akeji dasu a asibitin. Hilwah ta gaida Amihh ta amsa zucia fal kaunarta ta tambayeta ina AB'ILAL din, hilwah tace yana motar. Takaici ya kara rufe zuciar Amihh taso ace ya iso office din nata, da yau se yasha wulaknci a gunta. Kinci abinci?'' Amihh ta tambayi hilwah. Daga mata kai hilwah tayi alamar eh , Amihh tace 'Ok. .." Ta tashi ta dauko allurar dazatayi mata tana me duba time 10:44 ake nema, jan allurar Amihh tayi tana takaicin AB'ILAL. Ta karaso tace hilwah ta tashi ta juya ta mata allurar. Tashi tayi hadi dayin narai narai da ido kmr zatayi kuka, dmn da kyar amihh ke mata allurar sbda batason allura.lallabata Amihh ta shigayi, da kyar ta tsaya aka mata allurar harda hawaye a hk ma dan Amihh bata da zafin Allura ne kwata kwata. Amihh ta rungumeta a jikinta bayan ta mata allurar ta shiga bubbuga mata baya tana me bata hkri. "Sorry sweet hk zaki haihu kuwa anya? Ko de se CS za ayi ne? Uhm? To ki hkri knji sweetheart..." Amihh ta fadi hadi da rungumota jikinta sosai, se faman hawaye takeyi. Amihh ta rarrasheta sosai da kyar ta samu ta hkra ta goge mata hawayenta, ta dan zauna na 10mnt kama amih ta rakota har wajen cikin asibitin dai-dai kofar dazata fita daga asibitin amihh ta batta sbda wani dr dayazo ya jata zuwa duba wani a emergency. Hilwah ta fito farfajiyar asibitin a zatonta ko bazataga motar tashi ba sbda jimawar da tayi seta ganta ajiyar zucia ta sauke ta fara tafia a compound din zuwa inda motar take, wani babban mutum da tin shigarta ya ganta ya zauna yana jiranta tin dazu, ya biyota ta karaso bakin motar tana niyar shiga ya dakatar da ita cikin isar mata da aminci wato sallama ta dakata daga kai hannunta motar ta juyo ta amsa sallar tasa hadi da zuba masa sexy eyes dinta, babban mutum ne dagani nera ta zauna a kalla ze Kai 65yrs baki neshi kirin but yanada kyau, danyar shaddace a jikinsa royal blue se kyalli takeyi dagani me tsada ce. AB'ILAL dake cikin motar ya cika fam fam kmr ze fashe sbda yadda taje ta jima a cikin asibitin byn tasan yana nan yana jiran yana kallonta tin fitowarta daga cikin asibitin har zuwa ta karaso bakin motar, motumin ya biyota nan ransa ya kara bace, kmr ze hadiye zucia ya mutu sbda takaici ya zuba musu ido yanaji a ransa kmr ya fita ya shakure wuyan guy din sbda haushinsa da yaji yanaji a ransa, tsabar bacin rai ko ganinsuma ya denayi sosai, Wato a asibitinma se tayi karuwancin....'ya fadi a bayyane cikinn hasala. Daga wajen mutumin yaci gaba da mgna yana washe baki kmr yaga wawan zama tin dazu daya gnta yace shi ai yayi matar Aure. Hilwah de ta bishi da ido kawai. "Sannu beautiful! Ni sunana Alhaji Ibrahim sani, na ganki kuma knyi min,...ko zan iya samun lmbr wayarki sbda naga ynzu kina sauri ne...amma Allah yayi halit...." Alhaji Ibrahim ya gaza karasawa sbda ganin AB'ILAL ya bude motar dreva seat ya fito fuskarnan tashi baki kirin kmr baqin maciji mesa, ya zagayo inda hilwah da Alhaji ibrahim suke zucia kmr zata fashe... Tin fitowarsa a motar Hilwah ta dawo da kwayar idonta knsa, gabanta ya yanke ya fadi ganin irin bakikirin din da fuskarsa tayi, se uban huci yakeyi kmr ze tarwatse, nan take jikinta ya hau kakkarwa.... Hnklin Alhaji ibrahim ya kara tashi gabansa yayi mummunar faduwa ganin yadda fuskar AB'ILAL din keta kara baki kirin kuma Gashi yana tinkarosa.
Chapter 117 · 0% Book details