Sashe 78
Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ya hade da me kyau. zuwanta gidan Amihh ta kula ita ba ma'abociyar son sa kaya masu nauyi bace, atamfofin da amihh ta dinka mata sunfi kala ashirin amma ko daya bata taba sawa ba, balle laces da amihh ta siya mata dinkakku duk bata ma kallesu ba, badan Amihh naso ba take barinta tanasa irin wadannan rigunan, sedan taga tafi sabawa dasu amma ita in a san samuntane hilwah tasa riga da zani na atamfa, amma sam taki sawa,,Amihh ta mata mgna kn ta saka tace toh kawai har ynzu bata saka ba, bata ma da niyar sawa. Tsura mata ido sosai Amihh tayi ganin batama san tana gurinba, gashinnan na kanta har gadon baya, akwai dan Mayafi karami a knta kalar red, dukda ta rufe knta ruf amma sumarta ta gaza zama a mayafin sbda tsananin yawanta, ya mata kadan, seda ta ballo ta fito waje. ta kurewa gu dya ido daga dukkann alamu tunani takeyi. "Hilwah!'' Amihh ta kira sunanta da muryarta me cike da narkakkiyar kaunar hilwah din. Firgigit hilwah ta dawo daga duniar tunanin data afka ta dawo da kwayar idonta kan Amihh wadda keta kallonta, a yanayin kallon da take mata ya bata tabbacin ta Dan jima a gurin tana kallonta. Tashi zaune tayi hadi da sakarwa Amihh murmushi "Amihh.." Ita ma ta kirata da muryarta me ddh, cikin karyayyen harshenta. Zaunawa Amihh tayi gefenta inda ta tashi, ta zuba mata ido ."tunanin me kikeyi sweetheart, matar AB'ILAL?'' Amihh ta jefo ma hilwah tambayar, hadi da mata kirari a karshe. Shiru hilwah tayi, hadi dayin kasa da knta jin kirarin da Amihh ta nata, se yau ma tasan sunan guy din AB'ILAL se maimaitawa takeyi a zuciar! "Tunanin me kkyi?'' Amihh ta kara tambayarta a karo na biyu. Ajiyar zucia hilwah ta sauke, tanaso tayi mgna amma tana shakkar Amih ko kunya zata ce oho. "Tunanin me kkyi sweetheart?'' Amihh ta kara jefo mata tambayarnan a karo na uku.. Hilwah tayi jim hadi da karayin kasa da knta murya cike da fargaba tace ''Amihh inaso inje gidannan in dauko wasu abubuwana..." Amihh taji jim tana kallon hilwah harta gama mgnar dimple dinta na kasan gemu se lotsawa yakeyi. "Zuwa gidan kk tunani kou?" Amihh ta tambayeta. girgiza mata kai hilwah tayi kawai... Amihh taci gaba da mgna ''banaso kije gidannan plx har abadan, knga ynzu kinada Aure bata yuwwa ma ki fita koda izinina ne sede inda izinin mijinki,... Me kkeso ki dauka a gidan?'' Amihh ta karashe mgnr da tambaya. Hilwah tace "abubuwana...." Amihh tace ''motar?'' Hilwah tayi shiru ita bama ta kawo motar ba a ranta, picture din mahaifiyarta shine abinda takeso ta dauka a farko se tab dinta, koda made bata dauka ba, ta siyo wani, sannan ta siya pad da take using ko ta samu wani sassaucin, dadin da dawa kuma tanaso ta dan shaqa koda cocaine dinta ne taji ddh, ko da ma bata sha codeine ba ko wiwi cocaine tafi tsaya mata a rai, jiya ma seda ta shiga toilet tayi kuka ma ishi sbda kewar kayan mayenta da tayi ba karamin shiga wani hali tayi ba, dukda tana cin abinci amma se faman rama takeyi. Kmr Amihh tasan me take tunani tace "Ko de kinaso ne kije kisha wadannan abubuwan danazo na samesu a dakinki ...wato kayan maye?" Shiru hilwah tayi ta kara kasa da knta kunya kmr zata nitse kasa, ita batamasan Amihh taga kyn maye ba a dakinta, se ynzu data fadi ta tuna da tama gama shansu ne ta kwanta a ranar. "Su kike tunani kou?'' Amihh ta kara tambayarta kur idanuwanta na knta. Hilwah ta girgiza mata kai kawai alamar ah'a Amihh taci gaba da mgna. "To shikenan inde ba shi kkeso kisha ba to ki hkra da tunanin xuwa gidannan plx?" Hilwah ta karayin shiru a rnta ba hk tasoba, ita de tanaso ta fita ko ba komi tade dauki tab dinta da pad dinta. "Kin hkra Knji ko?'' Cewar Amihh. Hilwah ta daga mata kai bata da yadda zatayi. Sosai Amihh taji dadin hkn tasan yarinyar na azabtuwa sbda sabo, Ka saba da abu a rabaka dashi na lokaci kankani babu dadih, dole ze tsaya maka a rai, ita tamaga hkrin hilwah koda yake ita din me hkri ce. "Kinci abinci?" Amihh ta kara tambayarta. Hilwah ta daga mata kai alamar Eh, dukda bata ci ba tasan in tace aah amihh zata matsa mata ne dole se taci ita kuma dmwar cikin rnta ta isheta, ko yunwa bataji...suna nan zaune amihh nata jan hilwah da hirah har salwah ta dawo ta samesu cikin farin ciki ta rungume hilwah nan suka hau murnan ganin juna, Amihh ta bisu da ido, zucia fal farin ciki. ga zuciarta salwah da hilwah bata bam-bam tasuba, kmr yadda takejin Salwah ga ranta haka takejin hilwah ga ranta, can can ma kuwa.