← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 225

Sashe 124

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

kayan baccin Salwah ta bude ta dauko wata riga me mugun kyau dark peach me digo digon laces me shape din heart ba karamin kyau rigar ta mata ba, tanada gidan nonuwa wato breast cup aiko nonuwanta suka cika rigar taf taf harma suka bulluko ta saman rigar sbda nonuwan nata sunfi girman cup din bra din, iya cinyoyinrta rigar ta saya, color din rigar ya dace da skin dinta, Ta kamata sosai rigar ta mata kyaun da bakina baze iya misaltasa ba, ta saki sumar kannan nata wadda keta walwali har zuwa gadon bayanta, Salwah ta bita da ido ganin yadda rigar ta kameta ya bata mamaki sbda ita rigar ta mata yawa amma inka gnta kaga hilwah a zahiri zakasha Salwah tafi hilwah kiba sbda salwah nada garin jiki, ita kuma hilwah barawon jiki gareta. Shape ne hilwah tafi salwah ba jiki ba, ita jikinta dan dai-dai ne komi ta saka seya mata kyau sbda jikin nata daukar kaya garesa. Salwah ta gaza daurewa tace "rigarnan ta miki kyau wlhy, knga yadda ta amsheki kuwa..." Cewar Salwah. Hilwah tace na gode, ta karasa ga dressing mirror ta dauki perfume dinta ta feshe jikinta dashi, (akwai perfume dinta a nan dakin salwah, kuma akwai a dakinta na side din Ab'ilal.) Salwah nata binta da ido har ta gama fesa perfume din, ta karaso ta rabe gefen salwah ta haye kn gadon ta shige cikin duvet salwah dake zaune ta saki baki tace "duk wannan rigar da kk saka amma ki kwana a nan, ai wlhy ki tashi ki tafi side din Yah AB'ILAL..." Hilwah ta marairaice kwayar ido tace " korata kkyi kou? Shikenan bari in tashi .." Ta karashe mgnr tana yunkurawa ta tashi zaune, Salwah ta mayar da ita ta kwantar tace "Ah'a ni bn koreki ba my, ki koma ki kwanta nasan Amihh se tazo ta koreki, itade tafiso kiyita zama a side Dincan me cike da kunci...." Hilwah tayi murmushi a ranta tana tunanin ta yaya salwah tasan side din AB'ILAL na cike da kunci. "Ni de plx dea ko Amihh tazo kice nayi bacci dan ALLAH." Hilwah tayi mgnr da muryarta me cike da shegen ddh hadi da shagwaba da karyayyen harshenta, salwah data tashi ta dauko system dinta ta dawo Ta zauna ta kwalalo dara daran idonuwanta tace "kikace?'' Hilwah ta kara maimaita mata abinda tace. Salwah tace "Tab ba ruwana... Ni amihh da yah AB'ILAL tsoratani sukeyi, sun cika fada fada, yah ab'ilal ma ita ya biyo a fada, a.ma ya fita jaraba ..." Hilwah tayi Murmushi kawai. Tace ''ni de ki ce wa Amihh nayi bacci plx sister in kkyi min hk zan baki wani labari me ddh gobe..." Salwah uwar yan son labari cikin zakuwa tace "tom zan fadi, promise zaki bani lbrin?'' Hilwah tace "I Promise..." Salwah taji ddh sosai ta bude system dinta ta fara dubata Hilwah na kallonta, salwah na danna keyboard din system din tace "Dea in tambayeki wani abu?'' Ta karashe mgnr tana juyowa ta kalli Hilwah wadda ta daga mata kai alamar e . "promise me zaki gayamin koma meye plx?" Hilwah ta kara daga mata kai alamar eh. Salwah ta gyara zamanta sosai da zaman system din dake jikinta tace "Amma de ke ba bahaushia bace kou?'' Hilwah ta daga mata kai alamar Eh. Salwah tace "haba shiyasa hausarki ba irin tamu ba, amihh ba bahaushi bace amma ta iya hausa sosai itama datayi mgna zaka fahimci ba bahaushia bace, ita indians ce, ke wani yare ce?'' Hilwah tace "nima na mnta yarena....'' Salwah ta hade rai tace "bawani baza ki gayamin bane, amma de wata rana ai zamuje nida ke gidanku kou?'' Hilwah tayi jim ta zubawa salwah ido ba tare data bata amsa ba, a karshe ta sakar mata murmushi hadi da juyawa tace "gobe zan gaya miki E ko Ah'a..." Tana fadar hkn ta kudindine knta cikin duvet din tayi shiru kmr tayi bacci nan ko duniar tunani ta afka na iyayenta salwah ta sosa mata wani ciwo a zuciarta ada yadda take da iyayenta baza ka taba cewa wai zata iya tafiar 2days ba ta barsu sbda so da kauna, amma ynzu ita ce kusan shekara daya da rabi batasa iyayentaba a kwayar idonta , gashi ynzu ko picture babu, da shi take gani taji ddh. Salwah ta bita da ido kawai bata kara takurata ba da tambayar dukda tana cike da tsananin son sanin wacece ita, taci gaba da duba system dinta dake kn cinyarta.
Chapter 124 · 0% Book details