Sashe 121
Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Amihh da alhasan kusan tare suka shigo gidan 4:30pm motar alhasan ta fara shigowa gidan ta Amihh ta biyo bayan tashi, yy packing ya fito itama ta fito ya karasa ya amshe bag dinta dake hannunta ya rissina ya gaidata ta amsa cike da girmamawa, ta shiga tambayarsa ya aiki ya amsa da lafia lau, duk yabi ya kagu tayi gaba ya biyata a baya zuwa side dinta, duk yabi ya kagu yaga hilwah yau da ita ya wuni a ransa, tun dazu yakeso yaxo amma Aiki ya riqeshi, ayyuka sun masa yawa ss yanzu ma yakicewa yy yazo. Amihh ta tsaya tana karewa harabar gidan kallo nan taga motar AB'ILAL. "Mutumin naka ya dawo kenan?'' Amihh ta tayi alhasan da wannan mgnr. Tini alhasan ya fahimci AB'ILAL take nufi yace "Yaushe ya dawo?'' Hajiya maryam tace 'Bansani ba my son, wannan firgitaccen frnd din naka ai baya fadi in ze dawo kmr yadda inze tafi naya fadi wasu lokutan, ga motarshi nan na gani..." Ta karashe mgnrta tana bin motar AB'ILAL da kallo. Alhasan yabi motar da ido shima a zuciarsa yayi murmushi dmn yanata adduarh dawowar tasa sbda yanaso ya gnsa ya sanar dashi abnda ke cikinsa, ya kikkirashi amma yaki dagawa daman yasan da wuya ya dagan. Amihh tayi gaba zuwa side dinta alhasan ya biyo bayanta, suna tare suna yar hirar ab'ilal har suka karaso cikin falon, Amihh taci karo da car key a tsakar falon ta tsugunna ta dauka tana karewa key din kallo nan take ta fahimci car key din ab'ilal ne hkn ya bata tabbacin ya shigo side din, sargafe car key din tayi a inda aka tanada dan sargafe cars keys din gidan. Ta amshi bag dinta dake hannun alhasan da tini ya zauna a kn kujerar 2ct se rarraba ido yakeyi ya kosa yaga hilwah. Amihh ta nufa bedroom dinta tana fadinn"Bari inzo in kawo maka abinci nasan ku gwauraye bacin abinci kukeyi a kn lokaci ba..." Alhasan yy murmushi kawai yana me bin Amihh da ido harta shige bedroom dinta , kullum seta masa gorin gauraye very soon yasan gorin ya kusa karewa sbda ya samu matar Aure insha ALLAH, ga abu a gidanki amihh...." Alhasan ya fadi a ransa, har yana harko ankai masa hilwah a matsayin matarsa first night ya dirjeta son ransa. Yana nan zaune a falon salwah ta shigo suka gaisa ta nufa bedroom dinta, ta tadda hilwah kwance ta karaso ta wurtar da bag dinta a kasan carpet din dakin ta krso kn bed din ta rungumeta tana fadin "I miss You me rabin suna... Ykk ya jikin?'' Hilwah ta amsa da da sauki, ya scul? Salwsh bata kaiga amsawa ba, Amihh ta shigo dakin ta karaso tana me tambayar hilwah ya jikin ta amsa da da sauki, suka gaidata a tare ita da salwah. Amihh ta amsa kwayar idonta na kn kallon hilwah tace "cikin ynzu ya bar ciwon kwata kwata kou? Dake na wuni a raina love. '' Hilwah taji ddn kulawar amihh gareta ta Dagawa Amihh kai hadi da cewa E a kunya ce, Amihh taci gaba dacewa "to shikenan, tinda jiki yayi sauki seki koma side din Mijinki, in an gama abincin dare ki tafi dashi daga yau ban kuma baku abincina kema ki dafa a tukunyarki ki bawa mijinki kinga zaki samu la'adar aure sosai..." Hilwah da salwah suka bi amihh da ido tana mgnr, sam hilwah bataji ddn hkn ba, ita bataso ma ace AB'ILAL mijinta ne, mutumin da baya kaunarta ko kadan sam batajin ddn a danganata dashi, sbda mugune azzalumi. Salwah ma bataji dadin hkn ba, wani lokaci gani takeyi kmr amih nayin abinda be dace ba sede babu damar fada. Amihh ta juya ta fice a dakin ta riga ta karanto reaction din Hilwah na rashin son abinda ta zartar amma ta basar kawai a hk kuma dole ta hadasu a daki daya koda duk basu so ai shine Auren. Tana fita a dakin salwah ta juyo ta fuskanci hilwah, hilwah ta tashi zaune zucia bb ddh ko sunan side dinsa bataso a kira sbda aikin datakeyi masa kmr jaka, ga wulaknci danma last time basu hadu ba dashi, amma ita ko kallonta yy firgita takeyi sbda ta riga ta fahimci kallon kiyayya yake mata. "Ni wlhy bnjin dadin Abinda Amihh keyi sam...wai se tayi ta cewa ki koma side dinsa kiyi me to, abinnan naci min rai, shi ko mugun ba Allah bane a ransa..." Cewar salwah. Hilwah Ta bita da ido kawai ba tare data ce komi ba, amma a zuciarta itama batason hkn. Salwah ta basar da mgnr ta chanza wata "Wata Amina abdulkhadir tazo class dina ta tambayeni ina kk? Meyasa bakizo ba?nace mata baki da lafia ne, tace in bata lmbarki nace mata ai baki da waya, na bata lmbata tace zata kirani ta gaidaki...kin ganeta?" hilwah tace "Allah sarki mmn meema ce ai tanada kirki sosai..."salwah tace "Ai nagani tanada kirki kam, dukta damu dataga bata ganki ba tace 3 times tana zuwa neman class dina da kyar ta samu sbda batasan sunana ba, da kyar ta gane wlhy, tanada kirki kam, bari ma in kira miki ita..." Hilwah tace "Ah'a ki bari de zuwa gobe dea, maybe ynzu tana busy sbds iyalinta..." Salwah tace "eh hkne kam Ai matar Aure ce kou?'' Hilwah ta daga mata kai alamar Eh. Cikin zolaya Salwah tace "kmr ke kenan matar yah ab'ilal..."_ hilwah ta hade rai ta harari Salwah da sigar wasa, kwashewa da daria salwah tayi, daga hk ta mike tana fadin "karfa kwayar idonki ta fadi kasa madam M.A..."tana gama fadar hkn ta fada toilet, hilwah ta koma ta kwanta zucua fal takaici, da Salwah tasan irin yadda taji zafin kalmar wai matar yah AB'ILAL da bata fadar mata ita ba.... After magrib Alhasan ya bar gidan ganin bega hilwah ba shi ga zatonsa ko bata nan ne, sbda be taba zuwa yaga be gnta ba se yau, dukse yaji gidan be masa ddh ba , dukda be jimaba Amma se yaga kmr yayi awannin da sukafi tamanin a gidan sbda be gnta ba, ALLAH ALLAH ya rinkayi ya bar gidan , Amihh nace masa ya tsaya yaci abinci yace aah, ana jiransa ne, kawai ya fice a gidan ba tare dayaje side din AB'ILAL ba, sbda baya hayyacinsa .
8:30pm Amihh tazo ta tasa knta zuwa side din AB'ILAL ba da tray din abincisu a hannun hilwah ta nufo side din, amihh bata rakota ba sbda tanaso ta duba wasu ayyuknta dasuka mata yasa duk knta yayi nauyi a 2days dinnan, marasa lafia masu rikitarma sun mata yawa, Gashi tanaso ta koma scul dan ci gaba da karo ilmi, duk da shekarunta sun tafi amma taji a ranta tanason komawa mkrnta ko ba komi ta temaki nata, inma ta ajiye aiki, kuma ga asibitinta dake kano danma can akwai kwararrun likitoci dan hk bata da fargaba.
Tana shigowa falon side din nasa taga bata ga kowa ba a falon, ta nufa dinning are ta ajiye tray din hannunta ta nufa bedroom dinta cikin sauri sauri, ta mayar da kofar dakin ta rufe, , abincinma knci tayi ta koma tabi lafia kasan Carpet ta kwanta ko zata kwanta a kn bed din seta tuna da warning dinsa gareta kn carpet dinma dan bata da yadda zatayi ne take kwancia a knsa sbda sanyin kasan tiles ya illatata Danma Allah ya jibanceta tsuliarta bata dauka ba, mikewa tayi ta nufa toilet sbda jin pad din dake jikinta ya dameta sbda jiqewar da yayi ita ga zatonta period dinta ne yayi batan kai ya zubo yau, dubawa tayi taga bashi bane zallar ruwanta ne kawai cire pad din tayi ta zubar dashi a kwandon sharar dake toilet din, ta hada ruwa me zafi tayi wanka, ta fito ta shirya cikin riga da wando marasa nauyi na bacci ta koma ta kwanta nan kasan carpet din ta lulluba da hijjabinta tana me tunano rashin mutumcin AB'ILAL ko side din ta nufo seta tuna da wulakntatan da yakeyi abinda bata tabayi ba a rayuwarta seda ya sata a side dinsa, ga cin mutumci harda mari, gs kwanan waje daya batta tayi, Wannan abu yafi komi tsaya mata a rai.