Sashe 215
Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
12:am firgigit tayi ta tashi daga nannuyan baccin daya figeta, ta tashi zaune hadi da salati ga ma'aiki S.A.W , ta mike da kayn bacci a jikinta, hk kawai taji a baccin kmr muryar hilwah na kwala mata kira, hkn ne yasata Tashi a firgice hk kawai taji a jikinta cewa ba lafia ba, zagaye ta shigayi a dakin tana me kirari ga mahacci hadi da krnto ayoyin alqur'ani me girma, sbda neman natsuwa, tafi karfin 30mnt a hkn kana ta Farajin natsuwa a ranta, ta nufa bed side ta dauki wayarta kirar Samsung ta shiga lalubar number din salwah tayi ringin hatta tsinke ba a daga ba lokacinma ita salwah tana bacci batasan inda knta yake ba,, amihh ta kara dealing number din taji shiru seda tayi ma salwar kira 4 ba a daga ba, dukda dare ne tasan tana bacci amma se taji hnklinta ya d'an tashi tin shekaran jiya takejin tunanin hilwah ya yawaita a ranta, kawai de taji a jikinta hilwah bata cikin koshin lafia A ranta takejin wani abu na faruwa,,dena kiran salwah tayi ta shiga kiran Anty karama miss call daya ta mata itama baga daga ba, duba time tayi, se ynzu taga rashin kyautawarta na kiranta da tayi a wannan daren sbda tasan tana tare da mijinta. Ajiye wayar tayi a inda ta dauketa, nan take taji a ranta kmr ta tafi gidan a wannan daren amma sede ba dama, ta koma ta zauna gefen bed, ta rafka tagumi tunani ya dabaibaye rayuwarta ta rasama yazata fassara abnda takeji a ranta, kawai de tanajin damuwar dake ran nata tana yawaita....tana zaunen tana duba time a hk har asuba ta shigo ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala tayi sallar ko addu'ur'i batayi ba ta shafa ji takeyi kmr hilwah na kwala mata kira ga fad'uwar gaba tana ciki, ga zullumi daya cikata. Car key dinta ta dauka ta zira slifas ta fice zuwa compound ta shiga motrta ta tayar ta fice a gidan da sanyin safia ko haske gari be gama yi ba, taso ta daure ta bari zuwa 8:am seta fitan amma ta gaza hakan, sbda yadda damuwarta ke yawaitar. Tafiyar 30mnt ta kaita gidan hjya karama tayi hon me gadi na lekowa yaga motarta ya bude mata duka gets din gidan ta shigo ko packing din kirki batayi ba ta fito, ita de burinta taga hilwah suyi 2eyes ko hankalinta ze kwanta. Ta tsaya jikin motarta ta jingina tana kallon sararin samania se ynzu ne garin ya fara haske, tafi karfin 10mnt a nan tsayen kana ta isa ga side din hjia karama, koda ta taba kofar,tajita a rufe, tayi knocking dai-dai ma'aikata na gyaran falon gidan, daya daga cikinsu ta leka taga wacece kana ta bude mata ta shigo suka karasa cikin falon gidan tana me tambayarta "yan gidan sun tashi..." Hajara me aiki tace "Aa'a Hajiya,.." Hjya maryam tace "zuwa karfe nawa suke tashi?'' Hajara tace "A toh hjya suna kai tara wani lokacin kuma basu kaiwa, wani lokacinma sufi hkn..." Dai-dai suka karaso cikin falon gidan, ma'ikatan suka gaida hjya maryam ta amsa cikin mutumci, amma sam bata cikin nutsuwarta. hjya maryam ta kalli hajara tace "jeki tasomin hilwah da salwah in gansu...'' Hajara tayi jim dan ita ta kwana biyu ma bataga hilwah ba, sede batasan ina take ba,, "jeki tasomunsu in gansu mna..." Hjya maryam ta katse mata tunaninta, firgigit tayi tace toh, ta nufa corridor din dakin su salwah, ta taba Handle din dakin tajishi a rufe seta d'an bubbuga kusan 5mnt kana salwah ta tashi cikin magagin bacci tana me murzar ido, ta tambayi waye, hajara tace ''ni ce...." Salwah t nufo kofar dakin ta bude ta zubawa hajara ido , gaidata hajarar tayi salwah ta amsa, hajara tace "mamanku tazo, tace in kiraku keda hilwah..." Wata iriyar zabura salwah tayi gabanta ya yanke yayi wani irin mummunar faduwa tace "Wacece maman mu?'' A kid'ime tayi mgnr, hajara data kula da yanayin data shiga tace "Mamanku de Anty salwah, Wadda kuke cewa Amihh." "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Itace Kalmar data fito daga bakin salwah, hajara ta tsureta da ido ganin kid'imewar data shiga tayi yawa. "Ynzu Amihh tana falo ne?'' Hajara ta daga mata kai, seko salwah ta kra shiga wani sabon tashin hnklin wanda ke bayyane ya kasa boyuwa seda ya bayyana a kn fuskarta. "Hummm!'' Ta sauke ajiyar zucia hadi daci gaba da jefowa hajara tambayoyi "mommy ta fito falon ne?'' Hajara tace ''aa'ah bata tashba, itama Amihh datazo ta tambayi duk kun tashi nace mata aa"a shine tace in taso mata ke da hjya hilwah...." Zaro ido salwah tayi jin ta ambato sunan hilwah, ta koma cikin dakin a gigice ita ta rasa ma me zatayi ta jawo wayarta taga miss calls din mahaifiyar tata, duba time tayi taga tsakiyar dare ta kirata, jikin salwah fa ya hau rawa nan take ta farajin wani irin ciwon ciki, sbda tsabar kid'ima, jikinta ya fara bata kode ta gano hilwah bata gidan ne,,typing message tayi ta in box ta turawa hjya karama, kana ta fad'a toilet sbda yadda cikinta ya kara hautsinewa, tana tsugunnawa a kn toilet seat kawai se zawo,, ta gama ta fito dai-dai taji ana kara buga kofar, ta isa ta bude taga hajara ce, ta kalleta tana kokarin mgnr ta amsheta da "Meya faru?'' Hajara tace "hjya tace in kara kiranku, da tace zata karaso cikin dakin nace mata ynzu zaku fito..." Salwah ta karajin cikinta ya duri wani sabon ruwan,ga wata izayar murd'awa da cikin Nata keyi, tanada tabbacin wani zawon ne ya tarur mata. "Kice ina zuwa..." Ta koma cikin dakin, ta kara fadawa toilet ta sake wani zawon, kana ta fito ta dauko hijjabi ta saka a kn kyn baccin jikinta, hnklinta a tashe yake , ta fito daga dakin zuwa corridor, ta karaso falon knta na kasa yayinda gabanta ke faduwa, amihh dake tsaye tin tini ta kasa zama ta zubo mata ido tin fitoowarta falon ta duba bynta bataga hilwah ba byn ita, itan takeson gani "Ke ina hilwah take?'' Hjya maryam ta fadi idanuwanta na kn salwah, wata sabuwar kid'ima salwah ta shiga, ta karaso ta tsugunna ta gaida amihh. "Ina....ina...kwana..." Ta gaidata a kid'ime hkn ke kara tabbatarwa da Amihh ba lafia, rashin gaskia ta bayyana a gun Salwah. "Ba gaisuwa na tambayeki ba, ina hilwah na tambayeki ..kirawomin hilwah ni ita nakeson gani..." A wannan karon Hantar cikin salwah ce ta kad'a, ta gaza mikewa daga tsugunnen datayi data mike ma Amihh gaisuwa a zucia tace "Ya Allah ka fitar dani!'' Hjya maryam ta kara daka mata tsawa "Dan dangin ubanki bada ke nake mgna ba.. Wai yaushe ne na zama sa'ar wasarki ne salwah..." Ta tsure Salwah da ido, Wadda tsawar ta Amihh ta matukar gigitata, se zare ido takeyi kai kace ita ce yayanta dake can cikin gindi yana nitso. "Bada ke nake mgna ba!!!'' Amihh ta kuma daga mata tsawa, salwah ta zabura a Wannan karon FIYE da tunanin me karatu tace "bata nan....'' Batasan sadda kalmar ta fito daga bakinta ba. Hjya maryam ta tsureta da ido kai kace tsalle daya zatayi ta watsa mata mari, ranta ya kara zuwa wuya yayinda hnklinta ya kara ninkuwa a tashi, "wato ta gudu shine baku gayamin ba. " shine hasashenta. Salwah ta girgiza mata kai ba tare datayi mgna ba, wani irin mari hjya maryam ta daurawa salwah a matukar zafafe dmn ga bacin rai a tattare sa ita.. dafe kunci salwah tayi, ta faahe da kuka hadi da kara gigita a hk wai tin Amihh ma batasan ina hilwah take ba ta daura mata wannan gigitaccen marin, ina maga ta sani. Amihh ta kara daga hannu zata zubawa salwah wani marin na biyu anty karama ta shigo falon zani a hannu taga sakon salwah shiyasa ta iso falon, a gurguje dan tasan hjya maryam bata da sauki , a gigice hjya karama take tana takowa tana gyara zaninta wanda ke hannu ya gaza dauruwar mata,, shigowarta falon ya dktr da Amihh daga watsawa salwah mari na biyun. "Ke karama ina hilwah?'' Amihh ta jefowa hjya karama tmbyr hadi da tsureta da ido, hjya karama ta karajin tashin hnkli dari bisa miliyon, ta karaso inda Amihh ke tsaye,,ta nade haddu , hjya karama ta rasa ma ta ina zata fara, ta bude baki zatayi mgnr amihh data kureta da ido ta dktr da ita hadi da cewa "Wai me kukemin boye boye be? Boye boyen yasa na mari salwah, ku gayamin kawai in yarinyarnan guduwa tayi, ko wani abun ne ya sameta? Ni naji a jikina wani abu na faruwa da ita!'' Ta karashe mgnr tana me dafe gefen knta wanda ke mata barazanar tarwatsewa sbda dmwa. Salwah dake dafe da kunci har ynzu zafin marin shigarta yakeyi,, suka kalli juna ita da hjya karama. Ajiyar zucia karama ta sauke ta ynke shawarar ta gayawa hjyar gaskia,ta kula tana cikin wani yanayi. "Hilwah batanan...." Cewar hjy karama da seda ta dake ta fad'i hakan. Gaban Hjya maryam ya yanke ya fadi jin kalmar data fito daga bakin hjya karama ta zuba mata ido yayinda zuciarta kmr zata fashe zuwa wannan lokacin. "Dan Allah karama ki gayamin gaskia pls, kunsa zuciata a zullumi..." Yadda tayi mgnr seda ya basu tausai, hjya karama batasan sadda tace "ki kwamtar da hnklinki anty maryam, wlhy tana gun AB'ILAL mijinta AB'ILAL..." Hjya maryam ta zaro ido jin Kalmar data fito daga bakin karama jima takeyi kmr gizo mgnr ke mata. Salwah seda ta sauke ajiyar zucia bataso hjta karama ta fadi ba fatsal sbda ita Amihh ba a mata shigar sauri da mgna,, amma kuma sede tasan basu da mafita se a fadi gaskiar kawai. "Kmrya tana gun AB'ILAL?'' Amihh ta tambaya tana me tsure hjya karama da ido cikin mamaki da rashin fahimta. Hjya karama da tini jikinta ya fara daukar rawa kawai de tana dakiya ne taci gaba dacewa "A wlhy, bnsan ya tafi da ita ba anty maryam sede naga sakonsa wai suna kano..." "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Itace kalmar data fito daga bakin amihh taja da baya ta zauna kan kujerar dake daf da ita, ta dafe kanta sbda azabar zafin da taji yanai mata, nan take idanuwanta sukayi jawur,, kusan