← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 225

Sashe 46

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

maryam dake zaune kn gadon bedroom din Juwairriyya tana facin Dinta, itama zaune take kan tamtsetsen gadon nata tana fuskantar ta tace "eah wlhy hajiya wai in koma kaduna..." Hajiya Juwairriyya tayi shiru na wasu yan daqiqu taba wasu nazarirruka kana tace " To hajiya ke me kk ce masa?" Hajiya Maryam tace "Mefa? Ce masa nayi ban amince ba, to hajiya in koma kd inyi ke a can, kai! Ni nafi ganewa kano, da in koma kd kwara in koma indian in hakura da nigeria dukda kuwa sabon da nayi da ita..." Hajiya Juwairriyya tayi murmushi irin nasu na manyan mata masu ji da knsu kana tace "Inde Komawar taki kd shine Alheri ALLAH ya tabbatr..." Hajiya karyam da idonta ke kn Juwairriyya ta yatsina fuska tace "Adduarh de kikayi, amma ni a ganina, meye alheri a komawata kd? In tafi in bar aiyuka na? ina!" Hajiya Juwairriyya ta numfasa tana sauraron kawarta harta kai aya kana tace "In Alheri ne ke kiranki se kiga kin bar komi naki kin koma kd..." Murmushi kawai hajiya maryam ta saki wanda be kai zuciaba, ita sam bata da ra'ayin komawa kd har abadan tafiso ta mutu a birneta a kano ta dabo tumbin giwah ga mata ga nera. "Hajiya wai ya wajen mutumin ne?'' Ceqar hajiya Juwairriyya data kauda shirun dasukayi da wannan Tmbyr. Hajiya Maryam tace "wani mutumin kenan?" Tayi mgnr fuskarta dauke da alamar rashin fahimta. Hajiya juwairiyya fa dan harereta ta sigar wasa kana tace "mutumin ne yau kk nuna kmr baki wani ganeshi ba, AB'ILAL mana, kunyi waya..." Hajiya maryam ta yamutsa fuska tace "rabani da mara kunyar nan,.." Hajiya juwairiyya tayi yar daria yynda haqoran makkanta suka bayyana tace "kunyi waya kuwa? Ko ya dawo gida ne?" Hajiya maryam ta kara hade rai kai kace ab'ilal ne gababta tace "Ya dawo yamin ne? Waya kuwa kullun seya kirani, ke ni jiyama daya isheni kashe wayar nayi na ajiyeta na qosa da bura ubar yaron nan,.ina nan ina nazari a knsa so nakeyi kawai in samu me hnkli wlhy sede yaji na daura masa Aure inga tsiya da wasali wlhi sede ya mutu dan dangin ubansa...." Ta karashe mgnr cikin tsiwa. Hajiya Juwairriyya data zubawa maryam ido tayi murmushi tace "Tabdijan! ai karma ki soma hajiya, domin kuwa bakwa kwashe lafia ba keda Alhaji karami, yo ina ma ze yadda inba de so kkeyi yayita azabtar da yar mutane ba...wlhy hajia bashiba a zamanin nan koma waye baze yadda ba, hajiya ai ba ama namiji auren dole, yaran yanzu fa muke binsu basu ke binmu ba,...aike kici gaba da gode Allah hajiya yayanki na miki biyayya, musammanma Salwah danshi wannan alhaji babana idonshi a tsakar kai yake, amma shima yana iya qoqarinsa hajiya plx karki kuresa, gani ni me kwara daya tal, ina yake min irin biyayyar nan da naki ke miki ke a ganinki yau na isa in ma Alhasan auren dole a garin kano?'' Hajiya maryam tayi shiru kawai tana sauraron hajiya Juwairriyya ba tare data ce komi ba. Hajiya Juwairriyya taci gaba da mgna "Wlhy hajiya ke knki kinsan bn isaba in ma Alhasan Auren dole a garin kano,.. ina masa mgna a kn yy auren Amma ko ga jikinsa, be dauka bama balle ya aikata.." Hajiya maryam ta amshe mgnr da "Ai kwarashi hajiya shiru shiru yake...amma ni wannan yaron da beda ta ido hajiya nifa wani lokacin tsoro yaronnan yake bani...." Hajiya Juwairriyya tayi yar dariya kana tace "ke kike ganin hk hajiya maryam,..." Hajiya maryam ta kara amshewa da "Au ni nake ganin haka?" Hajiya Juwairriyya tayi murmishi tace "Kwarai kuwa, shifa nature dinsa ne hk, shi komi kawai seya fada, sannan beda tsoro, naga ai hk mahaifinsa shima yake Allah ya jikan rai, sam sam beda tsoro ubangiji de ya masa rahama..." Hajiya maryam ta amshe da "Ameen..." Hadi da miqewa tsaye ta dauki mayafinta ta yafa ta dauko handbag dinta ta riqe, hajiya Juwairriyya ta bita da ido tace "wai bade tafiya zakiyi ba?'' Hajiya maryam tace "Tafiya zanyi kam..ai ba na zaunaba har alhaji ya dawo..." Hajiya Juwairriyya ta kalli agogon dake manne da dakin tace "ai an kusa sallarh magrib, ki tsaya ayi sallah mna..." Hajiya maryam tace "Bkm zan tafi innaje gida nayi sallar...." Hajiya juwairiyya ta tashi tsaye itama hadi da cewa "Kai hajiya kin maida Alhaji kmr sirikinki duk tsawon shekarun nan kun kasa sabawa..." Hajiya maryam tayi murmushi kawai....har bakin mota hajiya Juwairriyya ta rako hajiya maryam suka kara sallahma kana hajiya maryam ta shiga motarta tajata ta fice a gidan ta hau hanyar zuwa nata gidan, zuciarta cike da uban tunani tunani rabi a kn AB'ILAL rabi kuma a kn mgnr komawarta kd, da maganganun dasuka tattauna da hajiya juwairiyya...can can kasan ranta kuma tana kewar AB'ILAL tanaso tasan ko yana ina ne, amma batajin zata iya kiransa ko shi inya kirata ta daga, sbda tanaso ta horasa a kan lefinsa horo me tsanani ta yadda inta daura masa aure da wadda takeso baze kara maimaita iskncin da yakeyi ba, a zahirin gaskia maryam tafi son AB'ILAL fiyeda yadda takeson salwah dan hk in tace bata azabtuwa da rashin ganinsa tayi karya.
Chapter 46 · 0% Book details