← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 225

Sashe 110

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A bangaren hilwah Ba karamin jin dadin baccin tayi ba at the end, amma a fari baccin be mata ddh ba. se juyi kawai takeyi a tsakiyar carpet din, bata tashi ba se karfe daya saura. ta tashi tana miqar gajiya da ciwon jiki dake addabarta, ta sauke ajiyar zucia hadi da miqewa tsaye ta nufa toilet a daddafe mazaunanta se ciwo suke mata sbda kwanan zaunen datayi se yanzu abun ke tambayarta. Wanka ta karayi da ruwan dumi sosai ta sake gasa jikinta, ta fito daure da alwala azahar kirjinta daure da bathrobe peach , ta karaso bakin mirror ta shafa versiline shi take shafawa dukda ga wasu creams sunfi kala ashirin amma bata shafasu sbda babu wanda take using a ciki shiyasa take shafa normal verselin kawai. Shiryawa tayi cikin wata riga dark green me stone a saman wuyanta sosai rigar ta dameta daf tako ina ta cika taf taf, kasannan nata kmr ze fashe a cikn rigar dake jikinta, ta feshe jikinta da turarrukan dake gaban mirror din wanda sukafi Kala hamsin, duk abinda takeyi cikin dauria takeyi amma batajin ddhn jikinta, side din inda ya maretanma ya kumbura. karasa tayi ta nufa inda aka tanada danyin sallah, ta zumbula hijjabi ta tada sallarh azahar din, tanajin knta na mata nauyi. A daddafe ta samu ta gama sallarh ta cire hijjabin jikinta ta shiga aikin gyaran dakin, tana gyaran taga mgnin da Salwah ta ajiye mata Ta dauka ta ajiyeshi a bedside, Da kyar take iya gyaran tanayi tana hutawa harta gama ta fito falon ta shiga gyaransa sbda gudun karta kara masa lefin daze Kai hannunsa jikinta, tasan in batayi aikinba ta shiga uku kila ma ya mata rashin mutumcin Dayafi na jiya daya mata ya barta waje ta kwana kuma ya hada mata da mari, a gaggauce ta gyara falon, ta nufa dakunan ta musu mopping kawai sbda basuyi datti ba, duk gyaran datakeyi bata sauri sbda rashin kwarewa. ta nufa saman ta Upstairs din ta gyarashi, kana ta dawo kasan, ta tsaya bakin kofar dakinsa so takeyi ta shiga domin ta gyara masa kmr yadda ya umurceta, Amma tana tsoron kar azo yana ciki harga ALLAH mugun tsoronsa takeji, data gnsa se gabanta ya yanke ya fadi, kmr yadda takejin tsoron mutuwarta hk take tsoronshi, jingina bayanta tayi da kofar dakin, tanajin zuciarta na fat fat, tunani tunani zuciar tata ta shiga yi, a ynzu tsoronshi takeji sosai abnda ya mata jia ya kara firgitata, tashi tayi daga jikin kofar data jingina, ta Kai hannu ta bude handle din dakin kmr zata bude se kuma ta fasa, ta fara sallahma a kofar dakin, seda tayi sallahma biyu uku kana ta bude Handle din dakin a hnkli zucia fal fargaba ta bude kofar dakin knta na kasa da sallama a bakinta ta shigo dakin, duk a tsorace take knta ma kasa tayi dashi ss kmr a ce arr ta arta a guje hk takejin ranta, bayan ta shigo dakin ta kasa rufe kofar taja ta tsaya still hannunta na riqe da murfin kofar, Sanyin Ac hadi da kamshin turarensa suka shiga ratsata ba krmin ddh kamshin dakin ya mata ba, seda ta lumshe kwayar idonta ta budesu a kasan tiles din dakin, hatta da tiles din dakin special one ne, dago kwayar idonta tayi ta zubawa kan bed din dakin ido, ajiyar zucia ta sauke me tattare da natsuwa, dagani be dakin, ganin bathrobe din da ya cire da yayi wanka tayi a kasan dakin dagani wanka yayi ya fita, ko ina a dan hargitse ranar nan batawa dakin kallon tsaf ba se yanzu ne ta samu damar yima dakin kallon tsaf, komi na dakin perfect ne, kmr yadda me dakin yake perfect, tsarin dakin ya hadu iya haduwa, adon furnitures dinsa royal blue ne, komi de acan acan, hatta da AC dake dakin daban ce, zubawa AC dake dakin ido tayi, nan ta shiga wani tunanin da ban, lumshe kwayar idonta tayi ta budesu a kn Bedside dinsa na left, ta sauke ajiyar zucia ta zubawa dankareren agogonsa dake kn bedside din ido, ajiyar zucia ta sauke a gaggauce ta shiga aikin gyara dakin da sauri sauri gudun kada yazo ya taddata, a dakin, ta nufa bathroom dinsa ta wanke masa ko ina daman ko ina tsaf yake, dukda kuwa ba a gyarawa inba ita ta gyaranba, ya dakatar da duk ma'aikatan dake aikin side dinsa sbda ga me Aiki ya samu a cewarsa. Tayi shara tayi mopping da sinadarai masu kamshi, duk bata iya ayyukunnan ba a rayuwarta a sanadiar zamanta a side dinsa gashi ta iya dolen dole. Tana gamawa ta fice a dakin taja ta rufe se uban haki takeyi ga yunwa na cinta ga gajiya again ga rashin jin ddhn jikinta da batayi, kuma ga azababben zazzabi datakeji yana zuwar mata har cikin kwayar idonta duk sanadin saurayen dasuka cijeta ne. Fitowarta daga dakin tana shirin nufar kofar dakinta salwah ta turo kofar falon ta shigo hannunta rike da trea, se ynxu ne ta samu ta samu knta daga hannun muguncan wuraren 4:2pm ake nema ynzu. salwah ta bi hilwah da ido ganin kmr daga dakin yah AB'ILAL ta fito, taja ta tsaya ta dakata ma daga shigowa tsakiyar falon, ta zuba mata ido sosai kwayar idonta dauke da alamar tambaya, hilwah ma idon ta zuba mata. Salwah ta juya bayanta ta kalli bakin kofa, gudun kada AB'ILAL ya shigo sbda ta barshi falon Amihh ya gama ma cin abincin ya koma ma falo ya zauna yanata aikin iyayi. Cikin hanzari salwah ta karaso ta kamo hannun hilwah suka karasa bedroom din Salwah, a kasan carpet suka yada zango. Salwah ta ajiye trea din hannunta a tsakiyarsu ta zubawa hilwah ido fuskarta dauke da tambayiyi a kn ganinta datayi a jikin kofar dakin AB'ILAL dagani ko ba a gaya mata ba tasan daga dakinsa hilwah ta fito. hilwah tayi kasa da knta tana wasa da zoben gold din dake hannunta na hagu a yatsanta wanda dagashi se karamin yatsa, Amihh ce tasa Mata zoben. nan take salwah taga kurajen cizon sauran har a hannayen hilwah a hk ma duk sun rarrage dande ma abinka da farin mutum ne, mamaki ya cika zuciar salwah takai hannu kan hannun Salwah ta shiga shafar hannun hilwah mamaki ya kara rufeta tambayar dake ranta ta gushe. "me rabin suna wai wannan wani irin sauro ne ya cijeki haka?" Ta karashe mgnr kwayar idonta na isa ga wuyan hilwah, nanma ta kara ganin jajayen kurajen cizon sauron. "Wannan wani irin sauro ne ya cike ki plx? Sekace kn kwana a waje..." Ta girgiza mata kai Kawai. Salwah taja tsukin da batasanma tajashi ba halin hilwah yana mugun kular da ita yana bata mata rai sosai. "Kuma wai se kkje dakinsa yau, wai memaya kaiki dakin yah AB'ILAL din? Ya dakeki jia amma yau kin koma dakinsa, salan yazo ya sameki ya miki rashin mutumci,..har ynzu ma bakisan halin yah Ab'ilal bane, beda mutumci wlhy, ni Shiyasa tin a farko bnso hadinku dashi ba wlhy,da Amihh tayi shawara dani da ban yadda ta hadaki da yah AB'ILAL ba beda kirki, ga mugun hali, se mugunta fal ran,.." Ringing din wayarta ya hanata karasa abinda tayi niya. Zaro wayar tayi daga aljihun doguwar rigar dake jikinta, taga number Amihh ta bayyana a kn wayarta da sunanta baro baro wato Auwal Hubb, jiki na rawa ta daga wayar ta kara a kunne, ta masa sallahma cikin ladabi.

*ba editing....ayi hkri...*
Chapter 110 · 0% Book details