← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 225

Sashe 77

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kimanin kwana biyu kenan da zuwan AB'ILAL gidan, tinda ya fita Amihh bata sake ganinshi ba dukda tana damuwa Amma hkn besa ta nemeshi ba ko da ta waya ne, a wannan karon so takeyi ta nuna masa tabbas ita ta haifeshi bashi ya haifeta ba. Bayan tayi sallar azahar tana zaune nan kan dadduma, ta tashi ta karasa bakin bed dinta ta zauna, ta dauki wayarta dake kan gadon, ta shiga dealing number din hajiya Juwairriyya bugu daya ta daga, daga bngarenta ta fara mgna cike da kewar hajiya maryam. "Hajiya wainshin kina kasar nan?'' Hajiya maryam tayi murmushi da iyakarshi yaqe ne, kana tace "Assallamu Alayki..." Hajiya Juwairriyya tayi yar dariya kana ta amsa "Wa'alaykissalam, na mnta ashe bamu nemawa juna aminci ba,,to ya kike aminiata? Kwana biyu kin boye nima kuma na boye..." Hajiya maryam tayi yar daria ita ma kana tace "yauwa ynzu kikayi mgna, amma da kince ina kasar ne, bayan nida ke duk bama kasar...." Dariya sosai hajiya Juwairriyya tayi Tana nazarin dariyar maryam da klmnta tasan basu kai kai ciki ba. "Bari hajiya Ai alhaji ne ke gida yana hutu wlhy bani da katafus, ..." Cewar Hajiya Juwairriyya. Hajiya maryam ta kara Murmushi tace "masha ALLAH, Allah de ya Kara dankon soyayya da nisan kwana..." Hajiya Juwairriyya ta amsa da Ameen..." Duk sukayi jim na wasu yan daqiqu, kana hajiya Juwairriyya taci gaba da mgna. "Ashe Alhaji karami na nan kd kou? " Hajiya maryam ta sauke ajiyar zucia tace "eh yana nan kd hajiya Juwairriyya, lamarin yaron nan yana damuna hajiya, abin nasa se adduarh , kwata kwata yaronnan beda mutumci,.." Hajiya Juwairriyya ta sauke ajiyar zucia dmn tasan a can damuwar hjya maryam take, tace "Ai ni nasan dajin wannan murya taki da abinda ke damunki hajiya, meya faru?" Hajiya maryam ta sauke numfashi kana ta fara mgna "Hajiya yaronnan kwata-kwata beda ladabi beda biyayya, Gashi nan de a tsaye ko rankwafawa beyi! ALLAH wadaran halin wannan yaron,.." Ta karashe mgnr da muryar takaici. Hajiya Juwairriyya tayi shiru tana sauraren hajiya maryam dajin hkn se tayi tunanin AB'ILAL ya kara wata tsiyar ne. tayi gyaran murya kana ta dauka da cewa "me yayi na rashin Ladabi hajiya?" Hajiya Maryam ta kwashe lbrin komi na auren data ma AB'ILAL A,to,Z ta shaidawa hajiya Juwairriyya, amna bnda na inda taga hilwah, wato gidan karuwai, sam bata gaya mata wannanba, tadece mata hilwah marainiya ce daga gidan marayu. Hajiya juwairiyya dake a zaune Amma seda ta tashi tsaye byn hajiya maryam ta gama shaida mata komi. "What! Tashin hnkli!" Sune Kalmar dasuka fito daga bakin Hajiya Juwairriyya. "Kai hajiya abin naki yayi tsauri a wannan karon dole yaronnan ya tubure, haba hajiya ki rinka Sara kina duban bakin gatari mna..." Cewar hajiya Juwairriyya. Cikin sanyin murya hajiya maryam ta amshe da "me nayi na rashin duban bakin gatari a wannan karon hajiya Juwairriyya?'' Cikin fada hajiya Juwairriyya ta dauka da "gaskia kin tauyewa yaronnan hakkinshi, haba maryam, auren dole kenan fa kika masa,.." Hajiya maryam ta amshe da ''na musu de hajiya, ai bashi kadai nayi mawa ba ita ma yarinyar nayi mata Ai ita ma aka cuta, amma knga ita tamin biyayya, gashi dan ciki na ya gaza min, shiyasa bahaushe yace da d'a da dukiya ba a musu mugunta duk da rnr su, d'anda ka haifa seya gaza mka abu se na wani ya maka cikin mutumci..." Hajiyar Juwairriyya ta amshe da ''ba wannan mgnr hajiya, ko be miki biyayya ba a wannan datsin beda lefi sam beda lefi...ai abinda zakiyi la'akari shi namiji ne ita kuma macece mace tafi namiji hkri a wannan fannin , kiyayyar namiji tafi ta mace zafi, gaskia ni de hajiya bnso kikayi wannan hadin ba, sbda knsan halin mutuminki da zafin kai, mata masu ji da knsu ma bebi ta knsu ba, balle wadda ke gidan marayuba, wadda bata da nasabah...." Mgnr Hajiya Juwairriyya ta karshe ba karamin dukan Hajiya Maryam tayi ba, kmr ita aka jifa da kalmar, cikin rashin jin ddh hajiya maryam ta dauka dacewa "tanada nasaba mana hajiya...." Hajiya Juwairriyya ta amshe da ''nasaba a ina? Bayan bakisan uwartaba bakisan ubanta ba,,,wannan ma duk ba problem bane, nasan aikin alheri kkyi hajiya maryam, Amma gaskia da baki kaiga zuwa wannan stage dinba, yayi tsauri da yawa gaskia ...kina shawara dani a komi naki amma a wannan stage din baki sakoni bama a zancan naki, kawai knyi gamin kanki,..." Hajiya maryam tayi shiru tana nazarin kalaman hajiya juwairiyya ita sam basu shigetaba, infect ma bata fahimci inda zancenta ya dosaba, tadesan son kai ne ke dawainiya da juwairiyyar sbda tanason AB'ILAL batason abinda ze dameshi shi yasa take ta wadannan zantuttukan. "Hajiya rayuwarta da ta bayar saboda ni yarinyarnan? Shin ina da abinda zan biyata dashi?'' Cewar hajiya maryam Hajiya Juwairriyya ta dafe knta kana ta fara magana. "Kin iyawa wani adalci hajiya amma baki iyawa naki adalci ba, a nan fa naki kk cuta kuma baki kyauta ba, dakin saka mata ta wata hanyar bata wannan hanyar ba..." Hajiya maryam tayi murmushi kawai kana ta amshe da "a wannan fannin nawan nama adalci na shiga haqqin baiwar Allah.." Hajiya Juwairriyya tace "meyasa kkce haka?'' Hajiya maryam ta ci gaba da cewa "Ai hakan nema,...ynzu duk yadda zan miki bayani bazaki fahimta ba sbda son zucia na dawainiyya daku keda danki.. " hajiya Juwairriyya tayi yar Dariya kana tace "shikenan Hajiya munji son zuciar ne ke dawainiyya damu , ande cucemu kawai..." Hajiya maryam tayi murmushi tace "very soon se bakinku ya mutu hajiya, wlhy gata nama yaronnan amma a zahirin gaskia ai yarinyar nan aka cuta..." Hajiya Juwairriyya ta tabe baki kmr tana gaban hajiya maryam tace "saboda duk jikin yarinyar da danyar gold aka yita Kou?'' Hajiya naryam tayi murmushi tace "wannan ai tafi gold hajiya, kede ki bari ki gnta...kun tsinci dami a kalah... " Hajiya Juwairriyya tayi murmushi itama tace "anya damin da muka tsinta na gaske ne, ina tantama? bade tarin dusa bane a ciki kou?'' Hajiya maryam ta danyi shiru tana nazarin hausar hajiya Juwairriyya na wasu yan dakiku , seda ta fahimceta tas kana tace "Hmmm...Hajiya kenan, ALLAH ya rabaku da son kai.." Hajiya Juwairriyya tace "Ai kowa nason knshi hajiya,...ni wlhy tinda kk fara gayamin mgnr nan tunanin halin da yaronnan ze shiga kawai nakeyi..." Hajiyar maryam tayi shiru kana tace "Au bama tunani rashin mutumcin da yayi ba kikeyi ...Hajiya wannan yaron wani lokaci se in rinka ganin kmr an chanza min shine dana haifeshi a asibiti .." Ta karashe mgnr murta cike da takaicin AB'ILAL. Hajiya Juwairriyya tace "meyasa kikace haka hajiya maryan?'' Hajiya maryam ta sauke nannauyar ajitar zucia kana tace "yaronnan beda kunya kwata kwata, beda tsoro, knsan cewa yayi seya saketa a rnr da nace masa na masa Aure...kinga haukan da yayitamin ne wai hajiya?'' Hajiya Juwairriyya ta amshe da ''kin taboshi ne hajiya..." Hajiya Maryam ta girgiza kai kawai tace "ALLAH ya shirya...amma akwai Aiki babba..." Hajiya Juwairriyya ta amshe da "Ameen ..aike kk jawo mna Aikin,...in de bame yuwwa bace ya sawaqewa yarinyar kawai. " Hajiya maryam tayi wani shu'umin Murmushi kana tace "idan gaf mutanen garin kano da kaduna da katsina, dangin ubansa ne, ya saki yarinyarnan sena ci masa mutunci a nigerian ma gabaki daya ...ko a zucia ya saketa ni dashi har abadan, dan na gaya masa ma ya nemi wata uwar bade niba..." "Tashin hnkli!'' Ita ce kalmar data fito daga bakin hajiya Juwairriyya, tayi kasak'e tana nazarin klman Hajiya maryam kana tace "Hajiya ki rinka bi a hnkali plx..." Hajiya maryam tace "in ba hkn na masa ba baza mu dai-dai taba,..nake gaya miki ma da yanzu lbri yasha bam-bam..." Hajiya Juwairriyya tace "Hmmm,,to shikenan ALLAH yasa ace kwara da Akayi..." Hajiya maryam ta amshe da "Ameen.." Cikin farin ciki. Hajiya Juwairriyya tace "to ynzu ya akayi da Amarya da angon namu?'' Hajiya maryam tace "kamar yaya?'' Hajiya Juwairriyya tace "mgnr tarewar Amaryar ? A wani gidan zasu tare? Kd ko nan kano?'' Hajiyar Maryam ta zaro ido jin hajiya ta ambaci kano tace "ta ina zan bashi ita suzo kano? Wannan yaron daba imani a ransa .. Ai a nan gidan ma zata zauna har inga gudun ruwansa, wannan yaron beda hnkli, innaga me yuwwa ce, se ta koma side dinsa na nan gidan, amma ynzuma ba wannan mgnr tukunna..." Hajiya Juwairriyya tayi murmushi danta kula hajiyar najin wannan amarya a can kasan zuciarta tace "Ai shikenan kede burinki ya cika, ALLAH de Yasa Alheri dan Alfarmar Annabi..." A tare suka karasa da S.A.W... "Ina salwah nah? Kota koma ne?'' Hajiya juwairiyya ta tambaya. Hajiya Maryam tace "ina ai bata koma ba, tana ma scul, ai ynzu an samu abokiya ba amason rabuwa da juna, shigowar yarinyarnan rayuwata alheri ce .." Maryam Ta karashe mgnr zucia da farin ciki. Hajiya Juwairriyya tayi murmushi kana tace "Wai! Sunan wani film na hausa daga temako... Daga temako seki wanke yaronki tas tas ki hadasu Aure ..." Hajiya maryam tayi Murmushi sbda mgnr ta hajiya abar a murmusa ce tace "ko kuma na wanke yar mutane na hadasu ba, inda badan ni bama Ai yarinyarnan tafi karfin ajinsa..." Hajiya juwairiyya tayi wata iriyar guda, Da bata masan ta iyataba se yau, kawai ta bar hajiya Maryam da gudar bata ce mata komi ba,a ranta tana so taga wannan yarinya me sa'ar auren AB'ILAL a lokaci kankani....daga hk suka juya akalar hirarsu zuwa wata siffar ...Daga bisani sukayi sallahma, sunayin sallamar hajiya Juwairriyya tayi dealing number din AB'ILAL, be daga ba, daman taso ne ta masa natsiha kn abinda ya faru, dabe daga ba seta barshi, ta bisu da adduarh kawai..... Bayan sun gama wayar hajiya maryam ta mike ta fito falon gidan, a kan kujerar 3ct ta samu hilwah kwance kewar Salwah duk tabi ta addabeta, da a bedroom take shine ta dawo falon duk ta kagu salwah ta dawo, time to time seta kalli kofar shigowa falo. Karasowa Amihh tayi ta tsaya ta zuba mata ido sanye take da doguwar riga mara nauyi me launin layi layi red and golden hannun rigar hannun best ne ba karamin kyau rigar ta mata ba, dukda bata kwanta a jikintaba amma ta amsheta abu me kyau
Chapter 77 · 0% Book details