← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 225

Sashe 22

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

zucia."inka kara mgna a falon nan, sena taso na hada kanka da bango! Ka fitarmin a gidana kawai banason jin komi daga wannan bakin naka mara tsarki..." A hasale ta karashe mgnr tata daji kasan ta kai last a bacin rai. Zaro idanuwa AB'ILAL yayi cikin tashin hnkli yace "Auwal hubb yanzu Bakina ne ..." Hajiya Maryam ta daga masa hannu alamar dakatarwa babu ko me kama da wasa a tattare da ita, "Inka kara mgna zuciarka da gangar jikinka duk se sun baci a gidan nan kaji na gaya maka!" Ta fadi da dishashshiyar muryarta me cike da kuna da haushin AB'ILAL. Ba tare dayace komi ba ya maida dayar kafarshi waje kmr ze fita se kuma yace "mommy Dan ALLAH ki bata hkri.. " yy mgnr idonshi na kn hajiya Juwairriyya daga masa kai kawai tayi alamar to ta masa Alama da hannu cewa ya wuce juyawa yayi jiki babu kwari, sam bayajin dadin yadda Auwal hubb ke masa, ya gaza sabo da halinta musammanma in An mata lefi. Kwafa hajiya maryam tayi a hasale ta daura kafa daya kan daya ta hau karkadata dagani kasan a hasale take dmn yau tin safe basu gidan ita da hajia maryam suna can gun dubiyar Hameedah a asibiti, sosai Hajiya Aisha taci musu mutumci ta zagesu Tas duk zafin Hajiya maryam bata tanka mataba tasan danta ne yajawo mata, nan duk yan uwan hajiya Maryam suka shigar mata suka zagesu tas kmr zogaleh, hakuri kawai hajiya Juwairriyya ke basu ita kam hajiya maryam shiru kawai tayi abin na cinta inside, shine abinda ya kara bata mata rai da AB'ILAL. Dasuka bar gidan direct suka kara nufar office din mahaifin hameedah suka bashi hkri dmn already Mijin Hajiya Juwairriyya ya sameshi ya bashi hakuri ya nuna ba komi. suma suka kara zuwa dan bashi hkrin, ya nuna musu ba komi ya hkra AB'ILAL yaci darajarsu amma da yaso ya nuna masa cewar yar halak ya tabo. Amma ya hkra, ya kira iyayensa suzo su amshi komi dasuka kawo shi baze bawa yarshi wanda besan darajar diya mace ba. Ya labartawa Hajiya maryam da Hajiya Juwairriyya hakan. Karshen kalmar Mahaifij hameedah tayima hajiya maryam zafi amma tayi hkri ta shanyema ranta, tin safe se ynzu shigowarsu gidan kenan AB'ILAL shima ya shigo. Ajiyar zucia hajiya maryam ta sauke a hasale takai dubanta ga Salwah wadda kanta ke kasa gabanta nata dukan uku uku dan tasan karshenta itama se an dawo kanta an zazzaga mata ruwan bala'in da batasan dalilinsaba itade kawai ta tari aradune da kah. Aiko tasan itama zatasha wulaknci kilama nata yafi na yah AB'ILAL dmn haka Amihh take kasa mata baki tana fada se ta dawo kan wanda yasa mata bakin da tijara. "Ke kuma! Yaushe na zama tsarar wasanki da har ina mgna zaki sakomin baki?" Hajiya maryam tayi mgnr cikin zafi still idonta na kan Salwah wadda tini hantar cikinta ta kada da tsantsar tsoro da firgici a dunia tana tsoron Amihh saboda babu sauki a lamarinta.. Hajiya maryam ta kara jan kwafa idonta na kn salwah wadda knta ke kasa wayar dake hannuntama tini ta sullube ta fadi kasa jin irin kwafar da Amihh tayi. "Wannan ya zama na farko kuma na karshe, in ina mgna kika kara sakomin baki se wanda yake gidan yari ya fiki Jin dadin gidan duniarnan, zan nuna miki cewar ke karamar mara kunya ce, har yaushe raini ya ratsa tsakanina dake da har zaki bude baki kiyi mgna ina mgna, to ahir dinki, akuyarki ta kiyayi ramatah, ni ba sa'arh dangin ubanki bane da har zaki rinka mgna ina mgna, daga yau in ina mgna kina guri kikayi ko motsine in ina mgna, sekinyi nadamar rayuwarki...tashi ki bar falon nan dan dangin babanki!" Ta karashe mgnr da karfi har tana zabura kmr zata mike tsaye. Jikin salwah ya kara daukar rawa sbda tsabar firgici da tsoro da kyar ta iya miqewa tsaye jikinta na tsumah ta duka ta dauki wayarta data fadi kasa, takalmin dake kafarta daya ne, dayan na nan kasan kujerar data tashi ,amma bata tsaya saka dayan takalminba da takalmi daya a kafarta ta raba ta hanyar hajiya Juwairriyya ta wuce a tsorace, ta hanyar kujerar da Amihh take ya kamata tabi Amma ta gaza bi saboda tsoro. a guje ta karasa ficewa a falon dan gani takeyi kmr Amihh zata biyota a baya ne ta rufeta da duka, tana shiga Bedroom dinta ta kulleshi da key, nan kasan dakin ta zube tana kuka wasu lokutan tana ganin kmr batayi dacen uwaba, sede taji frnds dinta a school suna lbrin yadda iyayensu ke musu amma ita kam babu bakin mgna , kasancewar ita da uwarta sun zama kmr annabi musa da fir'auna sam basa zama a inuwa daya, a kullum in tasa goshinta a kasa se tayi adduarh itama ALLAH ya nuna mata randa Amihh zata jawota a jiki ta tambayeta damuwarta ta gaya mata kilama ta lallasheta , sannan ta dena kerarta a zamanin nan in uwarka bata jaka a jiki ba waze jaka kaji sanyi, in baka samu sakewa da uwarkaba ina zakasa ranka kaji sanyi, da wannan tunanin a zuciar Salwah ta kara fashewa da kuka me tsuma zuciar me sauraroh, tanajin can cikin kasan zuciarta na mata kuna hadi da radadi.
Chapter 22 · 0% Book details