Sashe 64
Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
da kwalebanin codeine, da ledar cocaine hadi da nadin wiwi da aka gama dasu, dagani seda ta sha duk wadannan abubuwan dake gabanta kana ta kwanta baccin. Ganin kayan mayen a gabanta ba karamin kara tadama da hajiya maryam hnkali yayi ba, nan da nan kawai se kwallah, ta fara zirya kan kuncinta, taji a ranta akwai dalilin fadawar hilwah wannan halin kuma tayi alqawarin seta fiddota daga wannan mummunan halin da take ciki, kuma se ta mata gata ,gatan da dukkanin yah mace ke fatan samunsa a rayuwarta. kara Haska dakin ta shigayi komi na dakin tsaf kuma me kyau, a kn gado n taga Amal kwance itama se Aikin baccinta kawai takeyi, dukkaninsu basu jima da kwancia ba, hilwah ma seda tayi sallarh asubahi kana tasha kayan shaye shayenta ta kwanta, ko awa daya ba ayiba da bacci ya kwashesu. "Kinga hilwarh nan Hajiya..." Cewar kankana dake nunawa hajiya maryam hilwah ta dawo da haskenta kanta, tama rasa ya zatayi, ko tace ta rasa ma me takeji a rayuwarta da zuciarta. Karasawa hajiya maryam tayi kasan carpet din ta zauna ta dauki kayan mayen dake gaban hilwah ta hau karance karance tanajin knta na sara mata iya kar sarawa, yayin da zuciarta ke amsawa tamkar ana buga k'wallah. Kankana dake tsaye ya zubowa hajiya maryam ido ga tunaninshi tashin hilwah zatayi amma se yaga akasin hkn. Byn ta gama dudduba abubuwan ta mayar dasu inda suke , tayi tagumi kawai ta zubawa hilwah ido. Se kankana yaji tausan Hajiya maryam ya ratsashi me yafi wannan zafi uwa tazo taga yarta a gidan karuwai kuma da kayan maye A gabanta danma Allah yasa hilwah bame biye biye bace da se de hajiya maryam tazo ta iskota da namiji maybe ma ana tsaka da buga mata gwatso. "Mama se hkri fa, kaddara ce ki godewa ALLAH ma da yarki batabin maza bata bin mata...shaye shayen ne kawai..." Cewar kankana dake tsaye. Hajiya maryam ta dago ta kalleshi a ranta ta rasa shin gaskata mgnrshi zatayi ko yaya zatayi. Da kamar wuya de ta aminta da mgnr kankana 100% sbda zucia bata da kashi. Shiru kawai hajiya maryan tayi, ta dawo da kwatar idonta kan hilwah yayinda zuciarta ke bugu da karfi da karfi. Kankana yace "Hajiya ko zaki tasheta ne?" Hajiya maryam ta girgiza masa kai alamar ah'a. Kankana yayi jim yana kallon ikon Allah. Ya fara kokwanto Anya Hajiya maryam ba karya ta masa ba, kila ba mahaifiyar hilwah bace kode tanasone ta cutar da ita. Karasowa yayi ya zauna kusa da hilwah ya zuba mata ido shima gudun kada Hajiya maryam ta cutar da ita. "Hajiya zaki iya tafiya tinda kin ganta..." Cewar kankana, hajiya maryan tayi murrmushi kawai ba tare data bashi amsa ba, kuma bega almar ma zata tashi ba balle ta tafin ba, sema gyara zama data karayi. Duk abinda ke faruwa hilwah bata sani ba sbda baccin daya sureta me tsananin nisa ne.... Suna nan zaune sun zuba mata ido musammanma Amihh har kusan 10:am...A hnkli ta bude kwayar idanuwanta tar A kan hajiya maryam, gani tayi kmr a mafarki take ta kulle kwayar idonta ta kara budesu tar a kan hajiya maryam. Itama itan ta zubawa ido, bakinta ya gaza mgna. "Kin tashi?'' Cewar kankana daya ankare da tashin nata. Se a ynzu hilwah tasan ba mafarki takeyi ba, tabbas hajiya maryam ce a gabanta! zabura tayi ta tashi zaune still kwayar idonta na kan hajiya maryam wadda keta binta da wani irin kallo me wiyar fassaruwa.. Tabbas ba mafarki takeyi ba Amihh ce take gani a gabanta, to yaushe tazo? Kuma meya kawota? Babbar tambayar ma ya akayi tasan gidan?'' Sune tambayoyin dasuketa reto a k'ahon zuciar Hilwah. Kankana yabi hilwah da ido ganin yadda ta zabura ya bashi tabbacin tabbas matar mahaifiyar hilwah ce, ashe gaskia ta fada masa. Kasa hilwah tayi da knta tanajin wata iriyar kunya na ratsata ta rasa dalilin dayasa takejin kunyar. Hajiya maryam ta sauke ajiyar zucia tana karewa dakin kallo a zahiri a badini kuma zuciarta cike take da tunani tunani, dawo da kwayar idonta tayi kn hilwah wadda knta ke kasa zuwa ynzu ma ji takeyi kmr ta fashe da kuka. "Tashi mu tafi...." Shine abinda ya fito daga bakin hajiya maryam. Gaban hilwah da kankana suka yanke suka fadi a lokaci daya. Hilwah ta gaza motsi. "Tashi mu tafi nace..." Hajiya maryam ta kara maimaitawa a karo na biyu. Ba musu hilwah ta mike tsaye ta dauki hijjabinta dake nan kasan da wayarta ta saka hijjabin a jikinta jikin ta na rawa, haka kawai takeji a ranta komi hajiya maryam tace ta Aikata inhar be fitar da ita daga addinin isilamah zata Aikata sam bazata iya musu da itaba. Hajiya maryam ta mike tsaye ta kalli hilwah tace "mu tafi..." Kankana dake tsaye shima ya hau zare ido, ya bude baki da niyar yayi mgna hajiya maryam ta dakatar dashi sbda kadama yayi mgna yasa hilwah ta bijire mata, taji ddn yadda hilwah tabi mgnrta babu musu. Hannunta riqe da wayarta data dauka a nan kasan ta saka slifas dinta dake tsakar dakin, a jiki a sanyaye tanufa hanyar fita, kankana ya bude baki yace "Uwar dakina tafiya zakiyi?" Ba tare data tanka masa ba ta fice a dakin, ji tayi gabaki daya bakinta ya mutu, hajiya maryam ta nufa hanyar fita daga dakin, kankana na kokarin biyota ta juyo tace "Dan Allah karka biyo mu plx....kuma insha Allahu hilwah ita d gidannan har abadan, kuma da kuke ciki ALLAH ya iyakance muku.." Tana gama fadar hkn ta fice a dakin. Kankana ya tsaya nan tsaye ya daskare, se ynzu yake nadamar nunawa hajiya maryam dakin da yayi, dana sani ta shiga reto a kwakwalwarsa! wani irn ihu yayi me dauke da karad'i ya duba inda amal ke kwance se baccinta takeyi batasanma meke going ba. Karasawa yy bakin bed din ya hauba bubbugata a gigice yana fadin na shiga uku gatana ya kare a bariki! Gatana ya kare a bariki!!'' A gigice Amal ta tashi babu salati babu sallallami fadi takeyi hilwah! Hilwah! Meya faru?" Kankana ya kara kurma ihun dayasata dawowa hayyacinta ta toshe kunnuwanta yayinda kwayar idonta ke kan kankana, hade rai tayi ta cire hannunta a kunnenta tana fadin "wani irin iskan ci ne wannan..." Kankana dake a gigice yace "Mahaifiyar hilwah ce tazo ta tafi da ita...wlhy ta ce bazata kara dawowaba! Wayyo Allah na shiga uku!!" Kankana ya ke wadannan zantuttukan kmr mahaukaci nan take Amal ta gigice tana me tambayarshi wace hilwah! Kankana yace hilwah mana data sani! Ai a gigice ta diro daga kan bed din ta hau rarraba ido a dakin kankana yace mu bisu zasu tafi!" Amal dake a gigice itama tace "mu bisu ina?" Ba tare da kankana ya kara mgna ba yaja hannun Amal suka fice a dakin,.. aiko alamar au hilwah basu gani a compound din cikin hnzari ds gudu gudu suka fito wajen get din, dai-dai hajiya maryam taja motarta suka bar gurin...Kankana ya nunawa Amal motar a daburce yana fadin "ga motar can ...shikenan! Shikenan!Allah sarki uwar dakina!" Kankana ya karashe mgnr da muryarsa ta gardawa nan kasa ya zube yana kuka share share da hawayensa, wlhy ko sadda akace ubansa ya mutu beyi kukan da yakeyi yanzu ba, Amal tabi bayan motar data jima da bacewa da ido, daskarewa tayi a nan tsaye zucia babu dadih, kuka takeso tayi amma ta kasa, tsabar tashin hnkli data shiga ya shahara, ya wuce ma ta masa kuka, ta dawo da kwayar idonta kan kankana daketa sharar kuka tabbas abun babba ne tinda har kankana ke kuka da hawayensa!.....tsugunnawa Amal tayi nan kasan ta jawo knkana jikinta ta shiga bashi hkri hadi da rarrashi, da kyar ta samu ya sassauta kukansa, amma be bar hawaye ba. zuwa lokacin mutane yan gulma duksun cika gurin wasu daga gidan dandi wasu kuma wucewa sukazo yi shine suka tsaya su karas da gulma (like mommy R and olivia). se tambayar amal sukeyi meke faruwa, ko bi ta knsu batayi ba, taja hannun kankana suka koma cikin gidan, har lokacin kankana be bar kwalla ba, ita ma Amal kwallar takeyi me mugun zafi.