Sashe 183
Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ido kana yace "anything Anty...." Ynzu daya gnta ne yama fara gane yunwar cikinsa. Hjya karama tace ok, kana ta juya zuwa kiching din, gogan ya kara gyara zama a kan kujerar da yake zaune, babban burinsa yaga fitowarta daga dakin data shiga, ya zubawa kofar dakin ido, hadi da daukar cup din coffee ya fara kai bakinsa, yana sha yana jinsa cikin zallar nishad'i shi yau fa yafi dan sarki mulki da sarauta da farin cikin ma duka,..yana zaune yana shan coffee din yanata kallon kofar dakin da take har ya gama shanye coffee din be sani ba, sbda zuciarsa ta lulaqa a farin ciki, hjya karama ta gama hada musu breakfast a kn dining, kasancewar yau tin 6;30am me gidanta ya bar gidan, yayi tafia zuwa abuja kawai ta kwanta ne tanata baccin hutu, AB'ILAL da hjya karama suka zauna a dinning din suna breakfast suna yar hira, shide kaf hnklinsa be kn hirar yana kn kofar dakin data shiga dukya kagara yaga ta fito, harde ya gaza daurewa ya dawo da dubansa kn hjya karama yace "Anty...wai nace yarinyar nan ita baza tayi breakfast bane?'' Hjya karama ta dago ta kalleshi tace "Wacce yarinya? Ko hilwah kake nufi?'' AB'ILAL ya daga mata kai alamar Eh. Hjya karama tayi murmishi tace "Wadannan ai basa Breakfast da wuri se yunwa ta kwakulesu sannan zaka gansu sun fito zuwa kiching..." AB'ILAL ya ajiye spoon din hannunsa yace "to ynzu bazata fito ba kenan daga dakin?'' Hjya karama ta kalleshi ta fahimci dan nata a gigice yake,kuma an isan ne a gigitasa, a zucia tace "Yaga kaya..." Amma a fili tace "dolensu su fito sbda zasuje makaranta...'' A bayyane AB'ILAL ya maimaitawa "makaranta kuma?'' Hjya karama ta daga masa kai, hadi da cewa "Ay yau sunada lecture..." AB'ILAL yaji abincin break din dake gaban nasa ma ya gunduresa wato mkrnta ma matarsa ke zuwa ba izininsa, can take fita mazan bnza na kallonta, makaranta kode yawo..." Duk a zuciarsa yake wadannan zantuttukn nan da nan ransa ya bace yabi ya canza fuska. "Daman suna zuwa mkrntar ne?'' Ya jefowa hjya karama tambayar. Hjya karama tace "A nna suna zuwa, ko ka mnta ne.. ai mafarin zuwansu gidannan ma dasukayi hutu ne aka basu,, a fari zasu koma tin kafin a koma hutun Anty maryam tace a barsu a nan din tukunna..." AB'ILAL yayi kasake yana sauraronta hadi da daura maganganunta amizanin tunaninsa, nan ya fahimci sbda shine Amihh tace kar su dawo gidan, sbda ta azabtar dashi,. "Duk zan fanshe ai naga hnya..." Ya fadi hakan a ransa,, salwah ce ta fito daga bedroom din sanye da kayan bacci, knta ko dankwali babu, AB'ILAL ya zubo Mata ido, ga tunaninsa ko hilwah dinsa ce, se yaga salwah ce, dauke knsa yy a knta tin a kallo daya da yayi mata... idanuwan salwah kuwa na sauka a knsa ta fahimci shi dinne a guje ta koma cikin dakin data fito, tana fadin "hilwah Knga yah AB'ILAL a gidannan kuwa..." A gigice take mgnr ta karaso kn bed da hilwah ke kwance, dmn Salwah ta fita ne ta hado musu breakfast a tray, sbda AB'ILAL yasa hilwah kn fitowa, ta rinka rokon salwah kn ta fita ta hado musu. Hilwah ta bita da ido, ganin yadda duk tabi ta firgice kmr taga azara ilu. "Bakiji me nace bane?'' Salwah ta kara fadi jikinta se rawa yakeyi. Hilwah tace ''naji mana, meye tou?'' Salwah ta hade rai tace "ni kike cewa meye to?byn knsan komi.." Hilwah ta mata bnza hadi da juya mata baya, salwah tace "to taso kije ki hado mana breakfast ni wlhy bnso ne mu hadu dashi kwata kwata, ke kam ay nasan kinji dadin ganinsa ma, komin bnza kwa hadu ku cika mna gida da ihu..." Hilwah dake jinta ta juyo da fuskarta ta harareta ta turo baki tace "ni wlhy ki bari bnso ..." Salwah ta harareta itama tace "Karkiso din,,ay gaskia na fadi ynzu yah AB'ILAL na ganinki ay mun bani...yama ganki ay ni nasani, shiyasa kika shigo kinata kamshin jikinsa, ashe har yan rungume rungume akayi, to ki tashi kije ki hado mna breakfast in ba hk ba sede duk mu wuni da yunwa, gashi 11:am ma munada class wlhy..." Hilwah data zubo mata ido ta hade rai, itama batajin zata iya fita falon nan, sbda wannan jarababben nonon danta kula se kallonsu yakeyi dmn sun mata nauyi 2days sbda ta kusanyin period, inde ta kusanyin period cika sukeyi sosai, kmr zasu fashe, sannan suna mata zafi dan hk sam bataso a tabasu a wannan datsin, ko kallonsu ma bataso ayi. "Kika wani zubomin ido..." Cewar salwah..hilwah ta yamutsa baki tace "Da kikace anyi rungume rungume ALLAH ya isa..." Salwah ta kyalkyale da Dariya dmn tasan seta mata raddi tace. "Au Allah Ya isa? Lallai knji hausa tinda knsan Allah ya isa.. To ba ayi rungume rungumen ba ina kk samo kamshin perfume din yah AB'ILAL?'' Hilwah tace "Ni ba ayi rungume rungume ba.. Ni wlhy sis ki bar zargina ni ba hk nake ba, dan kar ma kice bn dau shawararki ba..." Salwah tayi murmushi kana tace "sadda ma zaki watsar da shawarata waya sani, kuma fa ni madam bnce wai ki sabawa ALLAH ba, ta hnyar bijirewa mijinki, ko yaya nede ki masa izaya shima ay kema ya zalinceki, ki rama ni fa ba ruwana da wai yaya nane, dan yana yayana ay be dace naki bin gaskia ba, wlhi ya zalinceki, ga lokacinki kema yazo.. Sede kash ke kuma sanshi kikeyi nasani..." Hilwah tayi saurin amshewa da ''ni bnce ba..." Salwah tace "ko baki ce ba wlhy sanshi kikeyi,,, ki nuna masa ke macece plz, ynzu zakiji dadin ci masa mutumci, tinda ya kyallara ido ya ganki kubul kubul dinnan nasan ba bari zeyi ba duk ma kara rikicewa zeyi, ni nagama har rama yy... wlhy karki sake kiji tausansa, nasan Anty karama ita yar abi yarima ce asha kid'i,,, plz kija masa rai dan ALLAH, karki sakar masa ragamar rayuwarki dan ALLAH, nide ina kara jadda da miki ne, sbda ki sewa knki mutumci sosai a garesa, inkin ja daga baya seki saki..." Hilwah ta dagawa Salwah kai alamar tou, kana tace "Na gode...'' Salwah tace "ba godia ba ma'am tashi kije ki kawo mna breakfast plz, time dinmu nata tafia mu samu mu shirya mu fita da wuri.." Salwah ta karashe mgnrta hadi da duba agogon dake dakin dai-dai ya buga 10:2am. Hilwah ta marairaice "zazzabi nakeyi plz ki hado mana..." Salwah ta tashi hadi da cewa " ba wani zazzabi,,sede in zazzabin love kkyi tinda gashi knga mijinki yau hnkli ya kwanta..." Hilwah ta bita da ido ta dauki hijjabinta ta saka ta fice a dakin, ita kuma ta tashi ta fad'a toilet danyin wanka. Dai-dai ta fito daga wankan tana shiryawa salwah ta turo kofa ta shigo hannunta rike da tray ta ajiyeshi a tsakiyar falon ta juyo ta fuskanci hilwah dakesa doguwar rigar abaya kalar onions. Baki sake salwah tace ''Ke knga bross ya wani hakimce a falo, se hira sukeyi shida Anty karama, itama yar taya bera bari, daga gani ma beda niyar tafia...wai knsan dana gaidasa ya ya amsa..." Hilwah ta girgiza mata kai alamar Ah'a. Salwah ta kwashe da daria "danace ina kwana yaya..ya wani kalleni up and down..." Ta kwatantawa hilwah yadda ya kalletan kana taci gaba dacewa ''bayan ya gama min kallon, na gadara ya kauda kai, ya wani amsa da "Lafiya.." Ta karashe mgnr hadi da kwaikwayon yadda AB'ILAL ke mgna cikin sanyi-sanyi, hilwah batasan sadda ta kwashe da dariya ba, hadi da cewa "Sis bakiji..." Salwah tace "Ba wani bnji...mijinne naki akwai gadara, kmr dan sarkin sudan...waifa cewa yayi wani lafiya.." Ta karashe hadi da kara kwaikwayonsa, duk suka kwashe da Dariya a tare...Hilwah hadda rike ciki gaskia ta tabbatar salwah Bataji, dabadan Amihh da yah AB'ILAL suna tsaye a knta ba, da ba karamin tabara zatayi ba. ''Madam yah abii, muyi muyi mu karasa breakfast mu fice a gidannan, ni wlhy duk gidan ma ya gundureni in muka fita bazamu dawo ba ko an tashi se muje shan ice cream, damun daidaici time din da dole de ya tafi semu dawo..."cewar salwah. Hilwah tace "Toh..." Sam ita bame matsala bace se yadda akayi da ita, suka karasa suka zube a kasan carpet suka fara breakfast, sunacin karin kumallon nasu, salwah nata kara bawa hilwah lbrin yadda AB'ILAL ya amsa mata gaisuwa a gadarance kmr dan sarki, se daria sukeyi har suka gama suna cikin nishadi. Salwah ta fad'a bathroom tayi wanka shap-shap ta fito ta shirya Cikin riga da zani se hijjabi zumbulele ta zumbula, hilwah kam daman tini ta gama shiryawa, ta yane knta da dankwalin jallabiar wanda ya amshi fuskarta sosai abinka da farar mace alkyabbar mata, rigar ma ta amsheta Ainun tako ina komi nata dam dam, dukda rigar bame kwancia jiki bace amma ita tabi ta lafe mata a jiki, daga yanayin jikin nata ne, ko hijjabi ta zumbula seya bayyana surarta da kirar jikinta. Feshe jikinta tayi da perfume dinta me mugun ddh, ta saka plat shoe dinta, hadi da ratayar bag dinta, salwah ma ta dauki tata bag ta zira plat shoe dinta suka fito daga dakin zuwa falon,, jin an taba handle din fitowa daga dakin yasashi zubowa kofar dakin ido sosai dmn tin tini kwayoyin idanuwansa na kn kofar dakin, hjya karama dake zaune tanata masa hira, tanawa bnza ne domin beji kuma be fahimta, kwata kwata ma hnklinsa be gun...yaga fitowarsu hilwah ta fara fitowa kmr maye ya kureta da ido, se ynzu yake ganin ainihin kyaun nata ashe kadan ya gani, duk kara gigicewa yayi kmr ze zaburo ya rungumota, ya gaza ma kallon nata a boye, nan take kowa ya fahimci kallonta yakeyi, anty karama ta fahimci hkn balle salwah uwar yansa ido. Karasowa sukayi falon, hjya karama data juyo itama ta zuno musu ido ganin kallon da ab'ilal ke musu yasata ankarewa ta zubo musu ido itama. Ta washe baki hadi da cewa "kaga yayan Amihh, fararen mata Alkyabbun mata,...ga uwar gidan abii nan kuma fitilar idon Alhaji abii na ta'alah..." Hjta karama ta karashe hadi da satar kallon AB'ILAL, Kunya ta rufe hilwah, salwah se washe baki takeyi...