Sashe 104
Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Da salwah ta fito falon bataga AB'ILAL ba seda tayi hamdala a ranta, ta nufa kiching ta dauko trea me kyau da plt ta dawo ta hadawa Amihh abincin a kn trea din kana ta nufa dakinta, bata gnta ba tana bathroom tana wanka, taji dadinn hkn, ajiye trea din salwah tayi a kn dan karamin table dake dakin, kana ta juya ta fice a dakin, ta koma kiching din ta dauko wani trea din ta hado musu nasu abincin da abun sha kana ta nufa bedroom dinta, tsugunne ta samu hilwah a kasa a gun kayan data Zubosu kasa har lokacin se ninninke kayan takeyi bata gama ba, salwah ta ajiye trea din hannunta a kasan carpet din tsakiyar dakin, ta karaso inda hilwah ke tsugunnen tana fadin ''wai gyara min kayan kkeyi ngde me rabin suna, barshi muci abinci... " ta karashe mgnr hadi da kallon kayan da hilwah ta ninke dake gefenta, ita ta gaxa tantance sune aka ninken ko kuma sune a yamutsen, dawo da kwayar idonta tayi kn doguwar riga dake hannun hilwah tana ninkewa nan take Salwah ta fahimci bata iya ninkin ba, Murmushi tayi hadi da amsar rigar daga hannun hilwah ta wullar da ita nan kasan, ta kamo hannunta hilwah ta tashi tsaye suka karaso nan kan carpet din suka zauna. a plt daya suka zuba, sakwara ce da miyar vegetables irin wanda ab'ilal yaci. Suka faraci hilwah taji dadinsa sosai bata taba ci ba a tsawon rayuwarta se yau, amma ya zama favorite dinta sbda ya Mata ddh sosai....nan side din Amihh ta kasance ranar suna tare da salwah a bedroom dinta karshema suka dawo falo da Amihh suka fara hira Amihh ke basu lbri sanda tana budurwa a can kasarsu yadda suke rayuwarsu, Salwah se aikin bin amihh takeyi da ido tasan saboda Hilwah ne Amihh ke bada lbrinnan, sbda tsawon zamanta da Amihh bata taba bata lbri makamancin wannan ba se yau. Suna tare har 10:am Amihh tace hilwah ta tashi ta tafi side dinsu ita da mijinta, gaban hilwah ya yanke ya fadi, tace "Amihh zan kwana a nan..." hajiya maryam tace "Ah'a bata yuwwa jeki side din Mijinki,..tukunna ma dazakizo nan kin tambayeshi?'' Hilwah ta girgiza mata Kai alamar ah'a. amihh ta hade rai kana tace "to karki kara knji kou? Ai knyi karatun addini kinsan be dace ba ki fita daga gidanki ba tare da izinin mijinkiba, daga yau ki rinka tambayarsa, ko baku mgna ne?'' Hilwah tayi kasa da knta hadi dayin shiru. Amihh ta zuba mata ido hadi da nazartarta. "Ko kuma de shine be miki mgna kou?'' Cewar Amihh. Nanma shirun Hilwah tayi. Amihh tace "shikenan nasan hkri zakiyitayi a zamanki da yaronnan, kiyi hkrin knji? Amma in yy miki wani abu ki sanar Dani karki damu da matsayinsa na d'ana na cikina, zan hukuntasa knji ko? Kema diyatace, Allah de ya dai-daice tsakaninku.." Salwah dake gefe ta amsa da Ameen, hilwah de batace komi ba. "Tashi ki tafi seda safe..."_ cewar Amihh. Hilwah tace toh hadi da mikewa tacema Amihh da Salwah seda safe, sukace ALLAH kaimu, harta nufa kofar fita Amihh ta bita da ido se taji ta bata tausayi, tacema Salwah ta tashi ta rakata zuwa compound seta dawo...Salwah tace to hadi da mikewa ta biyo hilwah wadda ta jima da ficewa a falon, biyota tayi ta rakota , befi taku daya biyu ba hilwah ta karasa side din nasa Salwah ta masa sallama ta juya ta koma side din Amihh tana waiwayonta itama tana waiwayonta, har salwah ta karasa shigewa falon Amihh, Kana hilwah taci gaba da tafiya zuwa side nasa, ta isa takai hannu ga murfin kofar falon ta murd'a ta jita a datse, hkn ya bata tabbacin ansa key ne ta ciki, kara murd'awa tayi dan kara tabbatarwa a datsen take nan ko ta tabbatr da a datse take,cire hannunta tayi a kn handle din kofar ta tsaya ta zubawa kofar ido a zuciarta tana shawara ne ta buga ne ko yaya zatayi?'' Tasan bata da wata mafita bace ta buga kofar, amma kuma tana tsoro sbda tasan gogan ne ya rufe kofar...seda ta kusa 30mnt a tsaye a bakin kofar tana nazari hadi da shawarwari a zuciarta, daga bisani ta yankewa knta shawarar kawai tayi knocking kofar falon, zuciarta na dukan uku uku takai hannu ta fara knocking kofar a hnkli a hnkli.... Yana zaune a falon sanye da kayan bacci masu mugun kyau riga da wando kalar sky blue masu mugun laushi da tsantsi, falon babu yalwar haske ya juya hasken zuwa na dare tin dawowarsa dazu ya zauna a falon sallah kawai ke tashinsa, yana jiran shigowarta ne yaci qaniarta amma yaji shiru, har zuwa daren Wato ynzu da yake zaune bisa 3ct system dinsa na jikinsa yana sarrafata, shine yake jiyo karar knocking din kofar falon, yasan itace murmushin mugunta yayi yau ya shirya cin kaniarta sosai sbda barin side din da tayi bata gyara gidanba, sannan yanada wanki yaso ya whlr da ita ss yau Amma bata zauna side dinba kmr ta sani, a ranshi ma yana zargin ko ta gayawa Amihh abinda ya mata jiya... Yanajinta tanata knocking din yayi bnza kmr be jita ba, tin tana knocking din a hnkli har ta komayi da dan karfi, Yanaji amma yayi mata bnza har kusan 1hour tana bugun kofar tanayi tana hutawa har tayi 1h din, yanaji se aikin gabansa yakeyi wato controlling system din dake kn jikinsa.... Daga wajen data gaji da bugun har ta yanke shawarar ta koma side din Amihh, se kuma tayi wani tunani, kawai ta zube nan kasa ta zauna zaman dirshen sbda ta gaji, har kafafuwanta sun sage, ajiyar zucia ta sauke bayan ta zauna kasan, ta sauke numfashi me cike da gajiyawa, a zuciarta duk tunaninta ko yayi bacci ne beji ba, bin gidan ta shigayi da ido tako ina haske fayau amma babu gilmawar mutum, seda ta danji tsoro a ranta, danma taga haske ne fayau kmr rana hkn yasata sassauta tsoron dake ranta. jingina knta tayi da bayan kofar shiga falon, ta sauke ajiyar zucia hk kawai taji a ranta ko zata kwana a wajen bazata koma side din Amihh ba, hk kawai ta yankewa knta shawarar hkn ba tare da wani kwakwaran daliliba. Seda tayi 30mnt a zaunen tana tunani tunani ga azababben bacci a idanuwanta, kana ta tashi taci gaba da buga kofar falon duk yana jinta a tunaninsa dayaji shirun yasha ko ta tafi side din Amihh ne, seda ya taso ya leqo ta jikin kofar ya gnta zaune a kasa, ya koma ya zauna yana me dariar mugunta a ranshi, duba time yayi yaga 12:3am, shine taci gaba da buga kofar falon, yayi mata bnza, wannan karonma seda tayi 1h zuwa lokacin ana neman 1:4am kana ta koma ta zauna tanajin wani irin bacci me mugun gigitaccen karfi yanata kawowa kwayar idonta hari, jingina knta tayi da kofar falon, ta mikar da kafafuwanta a kasan nan da nan bacci me nauyi yayi awon gaba da ita, harda ajiyar zucia da numfarfashin jin dadin baccin takeyi, nan fa sauro suka ce salamu alaykum yah uktih hilwah, daman an jima ba ayi feshi ba a gidan, dan hk sauron suka fara cizonta tako ina, amma ina batasanma sunayi ba, a cikin baccin de take dan kaiwa duk gurin da sauron ke ciwo duka da daya hannunta, kafafuwanta kuwa nan sauron sukafi cizo da wuyanta, sede tayita motsa kafafuwan nata sbda cizon sauron nauyin bacci ya hanata tashi, hatta farar fuskarta me ratsin red red sauron basu bari ba sun samu lafiyayyen jini nan suka hau bidirinsu, tako ina cizo suketa kai mata, abinka da farar fata kuma jikin laushi kmr na jarirai, duk inda sauron suka ciza se yayi red kuma se yayi kurji...
*sorry for the yesterday...ciwon kai ....*
*2days ba editing ayi hkri plx....*
*sorry for the yesterday...ciwon kai ....*
*2days ba editing ayi hkri plx....*