← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 225

Sashe 83

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AB'ILAL bezo ya kawo key din motarba, ballema Amihh tasa ran yanada niyar yin kayan lefen data umurceshi dashi din, har kusan kwanaki biyun data bashi suka shude harda dauria Amma bataga gogan naku ba, ta Kira shi yaki dagawa kuma tanada tabbacin be bar gidan ba, sbda warning data masa tasan ko yanashan giyar waken suya ne baze bar gidan ba. 6:pm ta nufo side din nasa, ko a tafiyarta kasan matsifa na cinta ainun. Turo kofar falon tayi ta shigo idanuwanta suka sauka a kansa, sanye yake da jallabia dark coffee color ta amsheshi Ainun, ya dan kara fadawa sbda beci besha, zubo mata ido yayi a kwanaki biyun be fita ko ina daga masallaci se falon se kuma bedroom, bacci kuwa se barawo kullum da takaicin Auren da Amihh ta masa yake kwana kuma dashi yake tashi.. Kallo daya ya mata ya gano matsifa kwance bisa fuskarta Dan hk ya dauke kwayar idonsa a knta. Karasowa tayi ta tsaya kan kujerar 3ct dayake kwance, ta zuba masa idanuwanta masu cike da bala'i. "Barka da yammaci Amihh.." Itace kalmar data fito daga bakin AB'ILAL yayinda yaketa kallon gefe da kwayar idonshi. Murya cike da takaici hadi da zallar tsiya amihh ta fara mgna "wai shin ko baka san kwanakin dana baka sun shude bane banga saqo ba?'' AB'ILAL ya hade rai kmr zeyi kuka yace "Banasa a kawo miki car key dinba kkce a dawomin dashi... Gaskia ni Amihh wlhy bnson yarinyarnan, a barni in huta..." Hajiya maryam ta gallara masa harara fuskarnan tankam da takaici tace "kuma dole ka zauna da ita ba ko kuwa zaka mutu....." Takajci da tsantsar tsanarta suka kara rufeshi. Amihh taci gaba da mgna cikin warning "Muhammad ka kiyayeni, ka fita a idona kaji na gaya maka...'' Dagowa AB'ILAL yayi ya zubawa Amihh ido tana kiran zallar sunanshi abinda bata taba ba se yau, duk a sanadin yarinyarnan, se yaji ya kara tsanarta. A hasale Amihh taci gaba da mgna "gobe 6:am ta wuce koda da 5mnt ne baka kawo abinda na umurce ka ba wlhy sena bata mka rayuwarka har abadah...." A fusace ya amsa da "Gobe kuma?'' AB'ILAL yy narai narai da ido inside kamar ze fashe. Amihh ta daga masa kai alamar tabbatarwa "In kanason sanin wacece ni ka wuce goben plx .."_ tana gama fadar hkn ta juya ta fice a falon. saukowa kasa AB'ILAL yayi daga kan kujerar da yake, yana fadin ''ta yaya za ayi lefe daga dubai a gobe Amihh..." Yana mgnr ne a kurarren lokaci bayan ma ta fice a falon. Yasan bada wasa Amihh take masa ba ALLAH kadai yasan ma me zata masa in goben tayi ba a kawo abubuwan data umurtanba, kila ma ta tsine masa Abinda yafi tsoro kenan game da ita yasan zata iya komi a kn yarinyar nan, ciki hadda tsine masan, tinda tama furta masa hakan. Badan ransa yaso ba ya kira wani dasuke business dashi a dubai ya umurcesa daya hada masa lefe akwati dozing daya, da kayayyaki masu mutumci. Alhaji zubairu ya tambayi AB'ILAL din meye size din bra da pant. Wani uban dogon tsuki AB'ILAL yaja a hasale murya cikeda jaraba yace "kai kasansu ni bansansu ba... Kawai a hada kaya na mutumci nace bnson inga kwayar zarra na kaya marasa mutumci kayan hausawa za a saka bawai na arna ba.... " Alhaji zubairu yy Murmushi ya fahimci gogan nashi danyan kaine ke damunshi. "To shikenan yallabai...mgnr pant da bra din fa ko kar asasu?'' AB'ILAL ya kara jan guntun tsuki yace "banason isknci...karma ka kuskure kasa abu me kamanceceniya da wannan abubuwan daka fada..." Alhaji zubairu yy daria kasa kasa dmn yasan halin gogan, dan sun jima tare. "To shikenan sir..." Cewar zubairu. AB'ILAL yace "a hadasu da wuri plx gobe nakeso su iso in time..." Alhaji zubairu yace "okay sir...kace abun ya matso yaushe ne daurin Aure dole muzo..." Takaici ya kara rufe gogan yace "Mtws! Kasamin details dinka bnson shashanci...'" AB'ILAL ya karashe mgnr da kara jan tsuki cike da takaicin mgnr zubairu ya katse wayar. Zubairu na turo masa da account din ya Danna masa kudade masu nauyi a account din nasa. Washe gari 5:am akwatunan suka iso nigeria AB'ILAL yasa dan ustaz ya je ya dauko su daga airport, ya dawo ya sanar dashi ya dawo duk dan Ustaz ya natsu, ya shiga hayyacinsa. AB'ILAL ya umurcesa dayaje su kwashi akwatunan a Kai side din Amihh dan Ustaz jiki na rawa yace to hadi da juyawa ya fice a falon AB'ILAL din. Shida da silele da dan malam suka kwashi akwatunan suka kai su falon Amihh, tana zaune ita da hilwah da salwah sukaga anata shigowa da akwatuna falon. Amihh ta zubawa akwatunan ido tabbas ba karya sun hadu iya haduwa, kyaunsu na fitar hayyaci ne. Seda aka shigo da guda goma sha biyu duk bata ce komi ba. Hilwah da salwah suma sunata kallon ikon ALLAH. Su kansu akwatunan sunyi musu Ainun musammanma hilwah sbda peach ne akwatunan masu kyau color din datakeso kenan peach, kallo daya tama akwatunan taji sun shiga ranta. Dan ustaz na shirin ficewa a falon Amihh ta Kirashi ya dawo ya tsugunna nan kasa yace "naam ainifin Hajiya gani..." Hajiya Maryam daketa kallon akwatunan tace "shikenan Akwatunan?'' Dan Ustaz yace "Na'am shikenan hajiya....ai Ainifin shi alhaji me shiru shiru ne yace a kawo..." Hajiya Maryam taja kwafa tace "jeka ce masa yazo ku taho tare...." Dan Ustaz ya hau zare ido kmr wanda yy karya yace. "Wato ainifin hajiya nifa tsoronshi nkeji wlhy,,, kwana ki dayamin wata tsawa seda na kwana biyar ina zawohh ..." Salwah ta kwashe da dariya hilwah tayi Murmushi kawai,..dann Ustaz ya bita da ido daman tin shigowarshi yaketa binta da ido, shi besnma tana gidanba se yau sbda ba fita takeyi ba, , da alamun tambaya da mamaki a kn fuskar dan ustaz a kn meya kawo hilwah gidan gashi babu damar ya tambaya. Hajiya maryam data hade rai tace "Zakaje ka kirashin ne ko ah'a?" Dan ustaz ya mike jiki na rawa yana Fadin "latagadab! Hajiya bari inje in isar da saqonki..." Ya fice a falon. Koda Dan Ustaz yaje ya sanar da gogan ya masa bnza kmr beji saba, dan ustax ya fice jiki ba kwari beje ya sanar da Amihh komi ba sbda besan mezece ba. AB'ILAL kmr bazeje kiran nataba, se kuma yaje after magrib ya nufa side din nata, a falon ya tadda akwatinan shi bemaga kalarsu ba se ynzu, su knsu akwatunan ji yayi a ranshi ya tsanesu. Ba kowa a falon, duk sun shiga sallarh magrib din, da kmr ya juya ya fice a falon se kuma ya karasa ya zauna kn kujerar 2ct wani kamshi me mugun ddh da be saba jin irinsa ba se rashashi yakeyi, ba krmin ddh kmshin ya masa ba. Yana nan zaune Amihh ta fito daga dakinta da niyar taje kiching ta gnshi zaune a falon, fasa zuwa kicking din tayi ta nufo inda yake tana fadin "se ynzu aka sanar dakai kirannawa kenan..." AB'ILAL da be kalli ma inda take ba kasa yy da knsa yace "tin dazu aka gayamin, naje sallah ne..." "Hmmm.." Kawai Amihh tayi, takaicin Ab'ilal da iskncinsa kullum kara karuwa yakeyi. Karasawa tayi ta zauna kn kujerar 3ct AB'ILAL ya zamo kasa ya zauna. Ta bishi da ido "akwatuna dozing dayanan dana gani na menene?'' Itace tambayar da Amihh ta jefowa AB'ILAL, shiru AB'ILAL yayi danshi be ganema kn gindin tambayar tataba yaza ayi tace yayi abu yayi kuma tana tambayarsa, dande fa Amihh ce wlhy da tuni ya gama goge mata hadda, to ita dole sede ya lallaba. "Dan Kanwar ubanka bakai nake tambaya ba!'' Jim yy a wannan karon seda yaja aji kana yace "Amihh akwatin da kkce ayi nefa..." Hajiya maryam tayi kwafa hadi da girgiza kafa tana kallon akwatunan a wulaknci tace "wato sune wadannan? Dozing daya, na uban meye dozing dayannan,...uban me za ayi da akwati dozing daya,..." Ta fadi a hasale. AB'ILAL ya dago ya kalleta Wato tana nufin yy kadan danma an samu ya siya ma kenan. "Gaskia ni kudin dozing dayan gareni , ni banda kudin dazan siya fiye da hkn...Yanzu ma de gaskia Amihh da ace knsan nawa na kashe ne da baza kice hkn ba, ga kudin Air shipping..." Hajiya maryam ta bishi da ido yana mgnr da zallar isknci. "Kutmar ubanka kaida kudin daka kashe din!" Amihh ta malmalo masa ashar. Kasa yy da kansa ynajin takaicin zagin Data masa, duk dan kn lefen . "Koda kudin uban waye kaje ka nema ka kawo dozing uku!'' AB'ILAL ya dago ya kalli mahaifiyar tasa yayi narai narai kmr zeyi kuka, yace "Amihh bnda kudin gaskia ni bndashi, ayi hkri da wannan din dana temaka nayi!'' Hajiya maryam ta bishi da kallon takaici ji takeyi kmr ta tashi ta rufeshi da duka, abinda yasa ta daga masa kafa sbda a yanayin akwatunan ta gane tabbas dubai dinne. Kwafa taja a fusace kana tace "Bubbudemin kayan in gani..." Ta umurcesa, daman bata duba cikin akwatunan ba, tinda aka kawosu bata tabasu ba, dmn ta bari ne se a gabanshi ta musu daya bayan daya. AB'ILAL ya zaro ido kai kace mutuwa aka ce masa zeyi, ya yatsina fuska kmr zeyi Amai yana kallon akwatunan yace "Kayan mata nefa a ciki Amihh...gaskia ke da knki kinsan ni bana taba kayan mata, a kira Salwah ta bude miki ki ganin mana,,,." Yayi mgnr ko a jikinsa, zuciarsa fal da kyamar kayan hadi da kyankyami.

*Book din na kudi ne 08136349646*
08/01/2022 脿 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: *YAR DANDI CEH...* 馃吙锔�25
DEDICATED
TO
(MRS ASAL)
SAADATU BINTU ABDULLAHI鉁嶐煆�
Chapter 83 · 0% Book details