← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 225

Sashe 126

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*Paid book....08136349646*
08/01/2022 脿 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 40***
Washe gari ta tashi tayi hidimar gidan, ta hada masa breakfast irin abincin larabawa , ita kadai ce tasan yadda ta hadasa rabi duk ganyayyaki ne ta ajiye masa a kn dinning table da ruwan zafi a flas 11:30am ta gama komi Ta zauna kan dinning din tayi breakfast dinta ta dauki plate din data gama ta nufa kiching dashi ta wanke ta kara tsaftace kiching din. Ta dawo falon ta kunna kaskon turaren wuta (burner) 10mnt yayi ta kashe nan da nan duk kamshi ya hargitse gidan da turaren sudania akwai da kamshi me shiga rai, yabi ya cika ko ina da ina da shu'umin kamshi, hatta da yan waje se sunji kamshin nan, har makwabta ma sbda dadin turaren. Komawa bedroom dinta tayi tana me yabawa da kamshin turaren wutar dmn ita ma'abociar kamshi ce nan dakin nata taji ya hargitse da kamshi tako ina da ina se kamshi yakeyi kai kace nan ma tasa masa turaren ne. Toilet ta fada ta sillo wanka daga ita se bathrobe ta koma ta kwanta kasan carpet da bathrobe din ta lullube jikinta da hijjabinta sbda bacci ne a kwayar idonta sosai jia ba wani baccin arziki tayi ba sbda tunanin maganar isknci da AB'ILAL din ya mata, ta jima tana juya kalmar karuwa da kalmar shi ba dan iska bane a zuciarta, duk dunia tana iya jure komi amma ta tsani a kirata da kalmar karuwa, ko kalmar yar iska, musammanma kalmar karuwa tafi tsaya mata a rai, harga ALLAH da guy din na ranta amma ynzu ta fara tunanin kmr be ranta amma bata tabbatar ba, ada ita da knta tasan tana sonshi, amma ynzu de sam baya ranta sede bata kiyayyarsa sosai a ranta sbda already sonshi ya riga daya kamata tin a hafuwar farko , data ganshi se taji faduwar gaba kuma na soyayya ne ba a tabayin namijin daya ke burgeta ba kmr shi, komi nasa kyau yake mata kuma gaskia ita tana bala'in son bakin namiji color dinsa har wani jan zuciarta yakeyi kawai de tana daurewa ne a knsa, amma ta fara yadda data kumu da sonsa a baya bnda yanzu . bata jima da kwanciar ba bacci me nauyi ya dauketa.

A bangaren gogan be wani samu bacci ba sbda jaraba dake cin zuciarsa ita ta taushe sha'awar dake ransa, a zahirin gaskia abin na Amihh ya fara wuce gona da iri a garesa. Seda yy sallar asubahi kana ya samu ya koma baccinsa mara ddh, ga haushi da takaicin abinda Alhasan yayi na yabon picture din hilwah ya dawo sabo fil a zuciarsa. 12:30pm ya tashi yayi wanka ya shirya cikin ka mnya, danyan yadi ne color me hsske, dinkin yar shara sun matukar amsarshi abinka dame kyau ba kaya ke masa kyau ba shi kema kayan kyau , i mean shi ke fito da kyaun kayan, sumarnan ta kansa ta kwanta luf luf dukda ba wani gyarata yakeyiba a yan kwanakinnan amma sam bata hargitsewa sbda a kwance take luf luf tin asali, inhar kaga ta hargitse to tabbas sede koshine ya hargitsata da hannunsa. Fitowa yayi falon gidan sanye da takalmi me mugun laushi irin na ajeboters, fitowarsa falon keda wiya wani irin kamshi ya dokeshi dmn tin jia yakejin wannan kamshin daya fito falon se yaji kamshin ya yawaita a hancinsa kmr yanzu akasa turaren wutar, ya fice a falon yana me kara shaqar kamshin falon hannunsa riqe da counter ya nufa masallacin dake wajen gidan. Tare sukayi sallarh azahar shida alhasan zuwansa kenan shine ya tsaya yayi sallarh a masallacin kofar gidan. A tare suka fito daga cikin masallacin, alhasan ya karaso ya bashi hannu suka gaisa se wani famar shan kamshi yakeyi da a farko ma kmr baze miko masa hannunsa su gaisan ba. Suka nufa gida a tare, direct side din Amihh suka nufa alhasan nata janshi da Surutu a kn ayyuknsu AB'ILAL ya wani basar kmr be gane me yake cewa, har suka isa falon amihh a kn kujerar 2ct gogan ya yada zango alhasan kuma ya yada nasa zangon a kn 1ct kwayar idonsa na kn AB'ILAL wnda keta wani kara shan kamshi, alhasan ya bude baki zeyi mgna, salwah ta fito daga bedroom dinta ta karaso inda suke da kmr zata juya data gnsu ta koma bedroom dinta inyaso ta fita ta dayar kofar sbda kiching takeson zuwa, alhasan ya zubo mata ido, dole ta karaso ta tsugunna ta gaidasu alhasan ne ya amsata da fara'arsa gogan kam be samu damar amsataba, sede ya kalleta yace ta hado masa coffee da soyayyen egg, salwah tace toh jiki na rawa ta tambayi alhasan shi me zata hado masa yace baya da bukatar komi," jiki na rawa salwah ta tashi ta nufa kiching ba jimawa ta hado masa coffee da egg and bread ta kawo masa ya amshi coffe din da plate din data soya masa egg din, yaki amsar ledae slide bread din dmn bashi yace ta kawo masa ba ita tayi shishigin hkn ta koma kiching jiki a sanyaye taci gaba da hidimar aikin hada abincin rana daman sallah ce ta shigar da ita dakin tama kusan gama hada abincin rnr ita da ma'aikatan gidan. Yau Amihh tin 7:am ta fita zuwa aiki ko breakfast batayi ba, kuma tace a kawo mata abincin rana shiyasa taketa sauri ta hada abincin ta bawa dan Ustaz yakai mata , ga scul zataje tanada lecture 3:pm. Cikin hanzari ta gama hada abincin Amihh ta hada a basket me mugun kyau se walwali yakeyi kmr diamond ta kira dan ustaz ta kofar kiching ta bashi tace ya kaiwa amihh asibitin 44, ya amsa ya wuce kana ta dawo taci gaba da kokarin hada musu nasu abincin na gida sbda abincin data hadawa Amihhn daban yake.
Chapter 126 · 0% Book details