← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 71

Sashe 9

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uwani ta taso a hannun Dada cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya, tun bayan tafiyar mahaifiyarta baba Mamman ya so a ba shi riƙon Uwani amma fir Dada ta hana shi, lokacin da Hajiya Saratu ta ji ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Shekarun Uwani goma sha huɗu a duniya kuma irin fitinannun yaran nan da suke fita zakka ko a cikin unguwa. Rashin ji, rashin tsoro, kafiya, naci, tsokana rashin yafiya sune halayen da suka mamaye Uwani har mutanen garin suka saka mata suna 'Uwani 'Yar Ƙashin Gwiwa' saboda hatsabibanci da rashin jin ta. Duk cikin gidan mai shanu Dada ce kaɗai ba ta ganin laifin Uwani, don haka ma duk wurin da ta shiga sai dai su bi ta da harara.

Jafar ma'aikacin ɗan sanda ne mai ɗauke da muƙamin ASP, shekarunsa talatin da biyu cif a duniya. Ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa matakin degree a jami'ar Bayero University. Miskili ne bai cika surutu ba, sai dai wani lokacin bauɗaɗɗan hali gare shi. Yana da kirki ga wanda suka fahimci juna sai dai wani lokacin yana da saurin fushi. Ba ya son raini ko kaɗan kuma yana da kykkyawar mu'amala da abokan aikinsa. Lokacin da ya fara aiki jihar Kaduna aka tura shi bayan wani lokaci ne ya samu sauyin aiki zuwa garin Katsina daga baya aka mayar da shi garin Lagos, ya kwana biyu a Lagos don bai cika zuwa hutu sosai ba. Ko da ya zo ma a gurguje yake kawo wa Dada ziyara shi ya sa Uwani ba ta wani san shi farin sani ba. Tana yawan jin labarin irin kulawar da Jafar ɗin ya dinga ba ta a lokacin da take yarinya, sai dai a wannan karon sam ba ta ga kalar mutumci a tattare da shi ba. Wannan hutun da Jafar ya samu kusan wata guda zai yi kafin ya koma, kuma ya ji labarin zuwan mahaifansa hutu da tariyarsu don haka shi ma ya yada zango a nan sashen Dada.

Mu Koma Labari

Tamkar sabuwar munafuka ko ɓarawon da yake sanɗa a daidai gaɓar da yake ɗaukar abin da ba na shi ba, haka Uwani ta shiga cikin ɗakin saɗaf-saɗaf tana tafe tana waige. Sai da ta kai ga ƙuryar ɗakin sannan ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya.

"Uban 'yan iyayi ashe ba ya cikin ɗakin, da tuni yana nan a naɗe a kan katifa kamar mai karyayyan ƙugu." Ta furta cikun salon kwaikwayon muryarsa. Motsin da ta ji a bayanta ne ya sa ta yi mutuwar tsaye, zuciyarta ta fara harbawa tamkar za ta bijirewa zama a ƙirjinta, cikinta ya shiga juyawa yayin da zazzafan gumi ya shiga keto mata. Caran zakaran da ta ji a bayanta ne ya sa ta sake sauke ajiyar zuciya, ta saki murmushi a fili sannan ta furta.

"Lawan wallahi ka cika binbinin tsiya, yanzu ɗakin Ofisa ma sai ka biyo ni. Idan kuwa ya kama mu wallahi sai ya kusa murɗe maka wuya." Tamkar zakaran ya san da shi take ya ci gaba da takawa yana tafe yana sakin kashi a tsaftataccan ɗakin da ya sha gyara ta ko ina sai zuba ƙamshi yake.

  Kafin Uwani ta ƙarasa kan katifar ɗakin tuni zakaranta da take kira da Lawan ya yi mata jagora zuwa kan luntsumemiyar katifar da ta sha gyara, a ɗame take da zanin gado kamar gadon sabuwar amaryar da za a kai ɗakin miji.

"Lawan ina ka baro Fanteka, uwar 'ya'ya na san tana cen tana yawo ita da 'ya'yan iya." Uwani ta yi maganar kamar da mutum ɗan'uwanta take yi. A saƙale ta hango uniform ɗinsa na kayan 'yan sanda masu bulun riga da baƙin wando. Da sauri ta janyo ta hau kwaɓe kayanta kafin wani lokaci tuni ta saka a jikinta, sai da ta gama soshe kanta da ya cukurkuɗe sannan ta kafa baƙar hularsa a kanta. Cikin ƙwambo ta fara taku ɗaiɗai sannan ta cake a wuri ɗaya.

"Ba na son hayani matsa daga kaina, ƙazama mai kwarkwata." Ta yi maganar cikin kwaikwayar maganar Jafar, tana faɗin irin maganganun da yake faɗa mata.  Ta jima a tsaye tana surutanta sannan ta ƙarasa gaban mudubin da ke can gefenta, kamar a mafarki haka ta hange shi tsaye ƙyam kamar wanda ya haɗiyi falwaya. Fuska a haɗe kwatankwacin ta fusataccan bujumin sa. Nan take yawun bakinta ya ƙafe, ƙafafuwanta suka ɗauki rawa ƙirjinta ya shiga harbawa. Sai dai dakiya da ƙarfin zuciyar Uwani ya sa ta basar kamar ba ta gan shi ba.

"Iya iya iya." Ta ji 'ya'yan kazarta na faɗa yayin da zakaran da ya gama kasaye ɗakin ya fara cara, da sauri kazar ta tunkaro ɗakin da niyyar shiga a fusace Jafar ya sa ƙafa ya yi ball da ita. Wata azababbiyar ƙara Uwani ta ƙwalla kamar da ita Jafar ya yi ball, ta fara tafiya wandon uniform ɗin yana zamo mata.

"Innalillahi kashe mini fantake za ka yi..." Uwani ta yi maganar tana shirin fita daga É—akin, yayin da Lawan (Zakaranta) ya firgice yana tsalle-tsalle a É—akin, yana jefo masa kwalaben turare.

"Gidan uban wa za ki?"Jafar ya wurga mata tambaya rai a ɓace.
"Ina da gidan da ya wuce ɗakin Dada..." Jafar ya katse maganarta ta hanyar bige bakinta da ƙarfi.

"Wallahi na ba ki nan da minti goma ki gyara mini ɗakin nan, sannan ki yi gaggawar cire mini uniform tun ranki bai ɓaci ba. Kuma idan kin gama zan gauraya da ke."

"Sai ka fita na canza kaya."
Sororo ya yi yana kallon Uwani don bai san lokacin da ta raina shi ba. Yana shirin sauke yatsunsa biyar a fuskarta wandon uniform ɗin ya zamo mata, gajeren wandon da ke jikinta ya bayyana. Fari ne amma dauɗa da jirwaye sun sa ya dafe saboda ƙazanta. A ƙazance ya kawar da kai gefe haɗe da tofar da yawu.

"Ka san dai kallon tsiraici haramun ne, ka fita na sauya kaya. Kuma ni dai ba 'yar iska ba ce..."
"Idan ba ki rufe mini baki ba wallahi sai na haɗa miki jini da majina a wurin nan. Sakarya fuska kamar ta aljanu, daga yau ko wani ne ya aiko ki ɗakin nan ba za ki ƙara marmarin shigowa ba." Tun da Jafar ya fara magana Uwani take kallonsa sheƙeƙe tun daga sama har zuwa yatsu biyar na ƙafarsa. Ba ta yi aune ba ta ji ya zuba mata rankwashin da ya sa ta gagara gane muhallin da take tsaye. Cikin sauri ta fisge hular kanta, ta zame dogon wandon uniform ɗinsa da ke jikinta.

Jafar na nan tsaye ya ji tuuush! Lawan ya jefo sabuwar kwalbar turarensa, a firgice yake miƙa wuya yana cara haɗe da ci gaba da taka kayan da ke saman mudubin. A zuciye Jafara ya jefa masa takalmin kanbas ɗinsa. Firgitar da Lawan ya yi har cikin ran Uwani don haka cikin ɓacin rai ta ce, "Allah dai ba ya zalinci yana kallon baƙaƙen azzuluman duniya masu baƙaƙen kaya." A fusace Jafar ya yo kanta rai a ɓace, ganin haka ya sa Uwani ta zuba a guje kai tsaye ta wuce sashen Dada Jafar ya rufa mata baya. A daidai lokacin da Jafar ya nufi sashen Dada shi kuma malam na Madina ya kawo kai, cikin rashin sani Jafar ya bangaje shi kaɗan ya rage gemunsa ya taɓa ƙasa.

"Jafaru! Kai Jafaru kana ji ka angije ni kamar ka angije dabba? Wallahi duk laifin Kulu ne ni take nunawa 'ya'ya da jikoki sun fi ɗan uwa." Ya ci gaba da tafiya har bakin ƙofar Dada yana kiran sunanta.
"Kulu! Kulu kina ina ne..." Cikin sauri Malam na Madina ya datse ragowar kalaman bakinsa jin furucin da Jafar ke faÉ—a.

  "Wallahi tun wuri ki wuce mu je ɗakina don har kan katifa..." Uwani ta yi farat ta katse shi.
"Amma dai ai ka bari na saka kayana yaya Jafaru, wallahi na fita a haka ka san dai mutanen gidan nan kowa sai ya san abin da yake faruwa." Jafar ya yi ƙwafa yana shirin ba ta amsa daga can waje ya ji muryar Malam na Madina yana sallallami.

"Yanzu Jafaru dama munafurcin da kuke aikatawa kenan? Shi ya sa saboda sauri har ka angije ni ko waige na ba ka yi ba. Ba da ni ba, wallahi ba zan zauna ana aikata alfasha ina kallo ba, lokaci ɗaya Ubangiji ya halakar da mu." Sai da Jafar ya fito daga ɗakin Dada ya samu Malam na Madina da ke bin shi da ƙazantaccan kallo.

Ficewa ya yi daga sashen Dada ya faɗa ɗakinsa, akwatin kayansa ya janyo ƙiiiiii yana kokawar fito da ita Dada ta sako kai ciki. Jin motsin ya yi yawa ya sa ta fara mita.

"Waɗannan dabbobi na Uwani yadda kasan tare aka shayar da su saboda duk hatsabibancinsu iri ɗaya ne..." Ganin Malam na Madina ya janyo akwatinsa ƙiiii ya sa Dada sakin baki, "Wai Muda ne a wurin nan ko Usumanu?" Ta wurga masa tambaya tana ɗan ƙanƙance ido. Sai da Malam na Madina ya fito sannan ya ce.

"Ki yafe ni Kulu don kar na tafi da haƙƙin wani a kaina."

Baki sake Dada ta ce, "Yaya wani abin aka yi maka ne?" Malam na Madina ya share ƙwallar idonsa, ta waiga wurin da Jafar yake tsaye a bakin ƙofa ya jefa masa mugun kallo sannan ya furta.

"Ubangiji aka yi wa laifi, ni dai tsakanina da mutanen gidan idan na ce an yi mini wani abu na ɗauki haƙƙinsu. Amma ni kam ba zan zauna ina ji ina gani a dinga saɓon Allah ba, gara na mutu salin-alin da a tashi idanuwa su bada shaidar baɗala ranar Lahira." Malam na Madina na gama magana ya fara jan akwatinsa ƙiiiii, da sauri Dada ta sha gabansa don tuni hankalinta ya tashi idonta ya fara ciko da ƙwalla. A duniya idan akwai abin ta tsana shi ne a ɓata ran Malam na Madina.

Jafar ya kafe Malam da kallo yana jin kamar ya ƙarasa ya shaƙe shi ko ya rufe shi da duka.
"A duniyar nan dai Yaya ka san mu biyu kaɗai muka rage, kuma kai ne uwata kai ne ubana kai nake gani na huce rashin su marigayi, (Iyayensu) don Allah ka faɗa mini abin da yake faruwa."Dada ta yi maganar tana share ƙwalla.
Chapter 9 · 0% Book details