Sashe 19
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina kucakar nan take?" A sanyaye Jafar ya nuna ɗaki, kamar Uwani ta san da ita take sai ga ta ta leƙo falon hannunta ɗauke da cinyar kaza tana ci.
"Ke don Ubanki ba a koya miki ladabin gaida manya ba ne?" Mami ta furta cike da tsana.
"Mami na ce miki ki daina zagin iyayena musamman mahaifina da yake lahira..." Jafar ya katse Uwani cikin tsawa. "Ke ba ki da hankali ne? Idan Mami na magana na sake jin bakinki sai na yi ƙasa-ƙasa da ke."
"Ka bar ta ba sai ta rama zagin da na mata ba, 'yar iskar yarinya marar mutumci. Ban da ƙaddara ko a mai aikin gidan Jafar za ki zo ne." Uwani ta kafe Mami da kallo, Mami ta mayar da kallonta wurin Jafar. "Kai kuma ka lura da kanka, atoh ka dai gane abin da nake nufi. Wallahi ko da wasa kada na ji ka tsaya sauraron yarinyar nan ballantana wani abu ya ratsa tsakaninku, don wannan tsinannan auren wallahi ko wata biyu ba na saka ran ya kai ba." Jafar ya ɗan tsuke fuska.
"Me kike faɗa ne Mami don Allah? Yarinyar da ko kallonta ba na son yi." Zuciyar Mami fes ta ce. "Shi kenan Son Allah Ya yi maka albarka. Ke kuma da ma gobe kina yin sallar asuba ki zo sashena ina son ganinki, shegiyar yarinya da ido kamar na mujiya." Uwani na tsaye ta ji zuciyarta babu daɗi. Wannan shi ne karo na farko da wani ya taɓa yi mata abin da ya bugi zuciyarta, tana nan tsaye ta sake jin muryar Mami a kanta.
"Don uwarki ba magana nake yi miki, 'yar iska yarinya tsohuwar kakarki ta sangarta ki kina iskanci kala-kala. Da ƙafarki sai kin bar gidan nan da ni kuke zancen." Uwani ta sauke ajiyar zuciya rai a ɓace ta furta.
"Mami wannan ce magana ta ƙarshe da zan gaya miki a kan zagin iyayena, zan jure komai amma ban da zaginsu. Dada ta daban ce a wurina amma matuƙar kika ci gaba da zaginsu ni ma..." Maganar Uwani ta katse sakamakon marin da Jafar ya sauke mata. Take idonta ya ciko da ƙwalla ta dube shi za ta yi magana ya katse ta.
"Uwata ba sa'arki ba ce..."
"Kenan ni iyayena ne sa'anninta? Wallahi ba zan jura ba..." Tas tass Mami ta sake É—auke fuskar Uwani da mari. "Na zagi Uwarki sai ki rama don ubanki."
Ban da ruwan hawaye babu abin da Uwani take yi, Mami ta gama ci mata mutumci sannan ta fice daga É—akin. Tsaki Jafar ya saki ya wuce ya É—auko bargo ya koma falo ya shimfiÉ—a ya kwanta zuciyarsa na suya, ta koma ta É—auko mayafinta ta yafa ta zo za ta fice. Da sauri Jafar ya fisgo ta fuska a haÉ—e ya ce.
"Gidan uban wa za ki a tsohon daren nan?"
"Gidan da na fito tun da nan ba gidan zinare ba ne." Uwani ta ba shi amsa a zafafe. Tana gama magana ta sake miƙewa za ta fita ya sha gabanta. "Wallahi ba don Daddy na gidan nan ba, da babu abin da zai sa na hana ki fita. Shashasha ƙazamar banza da wofi." Daga haka Jafar ya sa key ya rufe ƙofar. Uwani ta koma ciki rai a ɓace. A ƙasa ta zauna tana nazarin hanyar da za ta samarwa kanta mafita, don ta tabbata idan ta ce a haka za ta ci gaba da zama a gidan nan ba za ta sha ruwa ba. Kuma ita dai wannan ƙerarran gidan ba za ta so ta fita daga shi ba ko don ta dinga cin daɗi kuma ta gyara wa Mami zama.
Ƙurajen da suka fara tsattsafo mata a kai ne suka fara yi mata raɗaɗi, don haka ta ɗauko jakarta ta ciro farar hoda ta bursune kanta, fuskarta har zuwa wuyanta. Hamma ta fara saki tana gyangyaɗi ba shiri ta ɗauki fulo ita ma ta nufi falo. A lokacin da ta shiga falon Jafar har ya kashe fitilar falon ya yi bacci, a gefe ta yarda filonta ta kwanta ita ma nan take bacci ya yi awon gaba da ita.
Lokacin da dare ya tsala Jafar na cikin bacci juyin da zai yi sai jin mutum ya yi a kusa da shi, a tunaninsa Uwani ce don haka ya miƙa hannu sai ji ya yi ya shafo kan mutum da rantal da aski. A zabure ya tashi yana faɗin.
"Kwarto ne zai shigo mana gida." Ya ɗaga hannu da ƙarfin gaske ya ɗaka wa Uwani duka a baya a tunaninsa kwarto ne. Tun da ya san ban da haka babu abin da zai kawo namiji ya kwanta a kusa da shi. A zabure Uwani ta tashi tana susar baya, sai a lokacin Jafar ya kunna fitilar ɗakin. Cikin tashin hankali ya fara ja da baya ganin baƙuwar fuskar da ya gani fururu da hoda, a hankali Uwani ta fara tunkaro shi. Jafar ya fara ja baya yana faɗin.
"Don Allah waye kai?" Uwani ta ci gaba da matsowa ganin ta tunkaro shi gadan-gadan ya sa Jafar ya zuba a guje ya fice daga É—akin yana faÉ—in.
"Wayyo Allahna." Ita ma Uwani ta rufa wa Jafar baya a guje tana gudu tana wani irin gurnani.
Daga yau zan tafi hutun sallah sai ranar Laraba (19/06/2024) zan ci gaba da posting In Shaa Allah.
Littafin Uwani 500 ne amma daga yau zuwa ranar Laraba 19/06/2024 duk wacce ta za biya za ta turo 400 ta wannan Acc É—in Aisha Adam 3090957579 First bank Evidance ta wannan number
07062062624 na rage muku 100 for Happy Sallah. Idan kuma littafi ya zama Complete 800 ne, mutanen Nijar su tuntuɓe ni.
Ina fatan 'yan uwa za a bi nama saffa-saffa don gujewa rikicewar ciki.😂
07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
SHAFI NA SHA ÆŠAYA
Ilahirin jikin Jafar ban da karkarwa babu abin da yake yi, iya ƙarfinsa ya taƙarƙare yana gudu tun don tun da ya zo duniya bai taɓa cin karo da hallitar da ta ba shi tsoro lokaci ɗaya kamarta ba. Tashin hankalinsa ya ninku sakamakon jin ƙofar da za ta sada shi da gareji ta datse ƙam ta ƙi buɗuwa, ganin haka ya sa Jafar ya maƙale wani dogon ƙarfen da ke jikin rumfar harabar wurin. Cangala ƙafa Uwani ta fara yi ta fara wata shaƙuwa da ƙarfi tana zaro ido waje ta tunkare shi. Hannu ta sa ta fisgo ƙafarsa ɗaya sannan ta ce.
"Sai mun fige wannan ƙafar taka kamar yadda ake figar kaji, sannan mu ɗauke ka mu tafi da kai dajin tsumbur. Tun da har muka buɗe maka idanu kana iya ganin mu sai mun tafi da kai." Jafar a ruɗe ya furta.
"Wayyo Mami, wai Daddy ba kwa ji na ne? Ku taimaka mini kada su fige ni." Uwani ta fara wani juya idanu tana buɗe baki kamar mai shirin kai cizo, sai da ta sake zaro ido waje sannan ta kai baki ta gasa wa Jafar cizo a ƙafa. Ta sa hannunta na hagu ta yaƙuso ƙwaurinsa, ta ci gaba ta fisgar ƙafar tana faɗin.
"ÆŠan tsita yau balangu za ka ci, sai mun babbake maka wannan cinyar guda É—aya mai kama da ta sauro ka cinye."
Cikin azaba ya fisge a nan Allah Ya ba shi nasara ya buɗe ƙofar, ganin ɗakin Lado mai gadi ya fi kusa da shi ya sa ya nufi wurin a guje yana tafe yana waige. Abin da ya ƙara ɗaga masa hankali, bai wuce yadda idan ya waiga yake ganin Uwani na sake tunkaro shi tana zaro harshe waje.
A wannan karon Uwani ta sauya salon tafiya a hankali take tafiya tana zaro harshe, ta sake karkatar da kai ƙasa kamar yadda zombie suke yi. Lado mai gadi da ke zaune a kan kujera cikin gyagyaɗi ya ji gudun Jafar, a zabure ya miƙe yana faɗin.
"Ranka shi daÉ—e lafiya kuwa?"
Jafar ko ta kan Lado bai bi ba ya banke shi ya faɗa ɗakinsa ji kake garam! Ya doko ƙofar ya rufe, dabass! Lado ya faɗi saboda bangazar da Jafar ya yi masa ya yunƙura yana kaɗe jikinsa ya furta.
"Allah na tuba wane dare ne jemage bai gani ba? Ai sai daren mutuwarsa. Ni akwai wani aljani ko ɗan fashi da zai razana ni, ni da tun ban fi shekara biyar a duniya ba Baffa ya fara kwana da ni a wurin gadi..." Maganar Lado ta maƙale sakamakon hango Uwani da ya yi tana tafe tana ƙaƙƙanbare hannu, 'yar ƙaramar sandarsa ya ɗauka zai tunkari Uwani tsoro ya fara kama shi. Lado ya fara waige hankali a tashe ya cewa Jafar.
"Yallaɓai! Wai mene ne ma ya karo ka daga cikin gidan ne." Muryar Jafar a can ƙuryar ɗaki ya ce. "Lado gamo na yi don Allah ka yi wani abu a kai."
Lado ya fara tunkarar Uwani gabansa na faɗuwa, sai da ya tafi gadan-gadan kamar zai iya taɓuka wani abu sai kawai ya zuba a guje ya fara doka ƙofar ɗakinsa. Jafar na jin an fara doka ƙofar ɗakin Lado wani abu ya sake tsarga masa, jiki na karkarwa ya ce.
"Lado ya ake ciki ne kar dai sun fi ƙarfinka kai ma?"
Lado da ke cikin tashin hankali ganin Uwani ta zo daf da shi ya fara fitsare wandonsa ba tare da ya sani ba. Uwani ta fisgi sandar hannunsa tana wage baki, ta zuba masa tana caccaka masa tsinin sandar a baya. Cikin tashin hankali Lado ya fashe da kuka ya furta.
"Yallaɓai don Allah ka taimaka mini, ni ma fa na shiga hannu." Jafar da ke cikin ɗakin jin Lado na kuka shi ma sai ya fashe da kuka don ya san tun da aka fi ƙarfin Lado shi ma yana nan ɗakin za su zo su cim masa.