← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 71

Sashe 21

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tsohuwa mai ran ƙarfe." Dada ta saki murmushi ta furta. "Lallai Jafaru dare guda wai amarci ya ɓoye ka, ja'irin yaro da ana baka ka na ƙin karɓa..."
"Kin san Allah Dada zan kashe wayata." Jafar ya furta a taƙaice.

"Yoo kashe mana Jafaru, ai ubanka Mamman na nan. Ni ba zan aiki uwarka Saro ba saboda ba ganin mutumcina take ba. Amma wallahi ka kashe mini waya ban gaisa da Uwani ba sai na kira ubanka Mamman ya kawo mata waya." Jafar bai tanka ba ya miƙa wa Uwani waya.

"Dada ni dai gaskiya wurinki zan dawo, gidan nan babu daɗi ko kaɗan." Dada ta washe baki ta furta. "Haba Uwanita ai dama gidan aure kowa a sannu yake sabawa, lokacin da aka kawo Saratu uwar Jafaru ta haura wata biyu tana guduwa gida. Amma ba ga shi yanzu Saro ta murje tana zuba mulki ba, ke dai duk shawarwarin da na baki na riƙe miji ki riƙe su gam, kin san dai halin Jafaru da baƙin halin tsiya. Kar dai ki ɓata masa ya sa bakin bindiga ya harbe mini ke." Gaban Uwani ya faɗi, da sauri ta ce.

"Kuma sai ya harbe ni fa ko Dada?" Jafar da ke jin duk abin da suke faÉ—a ya kalli Uwani ganin lokaci É—aya ta firgice.

"Wallahi indai halin Jafaru da na sani ne tsaf zai harbe ki, yo ba Mamman ne ya haifo shi ba. Ai Allah kaɗai ya san haƙurin da Saro take yi da shi, ni ina zargin duk rashin mutumcin da take yi ma Mamman ne ya koya mata. Atoh kowa dai ya san mata na da alkunya, kuma idan kika ga mace ta canza daga mijinta ne. Ni dai yanzu duk wannan hirar da muke yi kada ki bari Jafaru ya ji, don sai ya sanar da Mamman. Ina zaman-zamana tun daga ƙuruciya ban taɓa sanin wurin Hukuma ba Mamman ya yi ƙarata. " Uwani ta ce.

"Dada wai ina na Madina ko cigiyata ba ya yi ne? Ina su Lawan kina dai kula da su ko?" Lokaci ɗaya Dada ta bushe da dariya sannan ta ce. "Na Madina fa ya tafi wurin wata Goggon su Sabi'u, ni ban san na Madina neman aure yake ba sai jiya, ashe shi ya sa kullin a cikin sayen turaren binta sudan yake. Ni dama na jima ina yi wa na Madina addu'ar Allah Ya damƙa shi hannu mata ta gari..."

"Dada zan yi amfani da wata na gaji da wannan hirar ta ku." Jafar Ya faɗa yana ƙoƙarin karɓar wayarsa. Daga can ɓangaren Dada ta ce. "Jafaruruna gaskiya na ji daɗin yadda na ji zamanku kai da Uwani, amma don Allah ka sayo mata waya ma dinga gaisawa idan kana gida." Jafar zai yi magana Dada ta katse shi.

"Kai gaskiya kar ma ka saya wa Uwani waya ka yi asarar kuÉ—inka, haka kawai kuna zaune lafiya ta haÉ—a lamba ta kira maka mutanen duniya. Kwanki da ta É—auki wayata sai ji na yi ta kira wani É—an yuniyon..."
"Shi kenan sai da safe Dada." Jafar ya katse ta yana karɓar wayar daga hannun Uwani. Dada ta saki murmushi ta ce. "Allah mai iko wai Jafaru ne yau yake zumuɗin kashe waya saboda ga mace a gefensa." Ɓacin ran kalaman Dada ya sa ya katse wayar ba tare da ya tanka mata ba.

Dare ne ya fara yi don haka Uwani ta gaji da kallon da take yi, É—aki ta shiga ta fara duba akwati domin ta É—auko rigar bacci ta saka. Tsulum ta ga Jafar ya shigo da sauri sai wani wuri-wuri yake yi.
"Malam ka fita zan sauya kaya." Uwani ta furta.

Banza ya yi mata don a yadda ta lura da Jafar kamar a tsorace yake, don haka ta ɗauki wata doguwar riga ta shige banɗaki. Sai da ta sauya kayan sannan ta koma ɗakin, tana shirin hawa kan gado ta ga ya jefa mata filo ƙasa.

"Ina zaki je?"
"Kwanciya zan yi." Ta amsa masa a taƙaice.

"Daga yau a nan ƙasa za ki dinga kwana idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci." Jafar ya yi maganar yana ɗaukan jallabiyarsa ya shiga banɗaki, sai da ya sauya kaya ya fito sannan ya haye gado ya kwanta. Uwani ta ɗauki filon ta koma can gefen gado tana shirin ajiye filo Jafar ya riƙo kunnenta da ƙarfi ya murɗe.

"Kin raina abin da na faɗa miki ne? To ki kwanta Allah Ya ba ki sa'a." Ya ƙarasa maganar yana murɗe mata kunne har sai da Uwani ta ɗan ƙwalla ƙara.

Babu yadda ta iya haka ta koma ƙasa ta yarda fulo ta kwanta, bayan wani lokaci gabaɗaya bacci ya yi awon gaba da su.

Cikin dare Uwani ta ji sanyi ya dame ta ga bargon na su Jafar ya ɗauka ya rufa da shi, cikin sanɗa ta ɗauki filo ta koma can gefen gado ta janyo bargon ta rufa. A wannan karon ma Jafar yana juyowa cikin bacci ya ji ya sake shafo ƙwaryar molo, Uwani da ke bacci jin ana shafa ƙwaryar molon kanta ya sa ta buɗe ido. Da yake ƙeyarta ce ke kallon fuskar Jafar sai ta maƙe murya ta ce.

"Kada ka motsa, idan ka yi yunƙurin guduwa sai na tsinke ƙafafuwanka." Jafar na jin haka sai kawai ya taƙarƙare ya rushe da kuka, ya fara biya duk wata addu'a da ke bakinsa. Sun ɗan jima a haka suka ji an fara kiran assalatu, Uwani ta fara wani gurnani tana wani bubbuga hannuwa sannan ta ce. "A yanzu za ka iya fita ka je ka yi sallah." Tun ba ta rufe baki ba Jafar ya buga tsalle ya fice a guje, yana fita ya ci karo da Daddy jikinsa na rawa ya furta. "Daddy wallahi gidan nan da aljanu Allah ba zan ƙara kwana a ciki ba." Ganin yadda jikin Jafar ke rawa ya sa Daddy ya riƙe shi gam a jikinsa, riƙe hannunsa ya yi suka fara tunkarar sashensu. Da sauri Jafar ya fara kiciniyar fisge hannunsa ya ce. "Daddy ina za mu shiga?" Daddy ya saki murmushi irin na manya ya ce. "Trust me son, ka san dai ba zan cutar da kai ba." Shiru Jafar ya yi suna tafe gabansa na faɗuwa har suka shiga, cikin shammata Uwani ba ta yi tsammani ba suka yi ido huɗu da Daddy. Cikin tashin hankali Uwani ta zaro ido, ta kai hannu ta dafe kanta.

Na ce kin turo kuɗin littafinki kuwa? Yau promo ɗin zai ƙare💃🏻 faka-faka ki turo 400 Aisha Adam First bank shedar biya ta wannan lambar 07062062624 idan yau ta wuce za ki turo 500 maza hanzarta kada a yi babu ke🫠

07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

SHAFI NA SHA BIYU

Ganin yadda Uwani ta tsorata ya sa Daddy É—an kawar da kansa, duk da a falo suka ci karo da ita za ta fito. A fili Uwani ta sauke ajiyar zuciya, ta sauke hannunta daga kanta don kaÉ—an ya rage asirinta bai tonu ba. Saboda ta É—aura É—an kwalinta a kanta kenan su Daddy suka shiga.

"Barka da asuba Daddy." Uwani ta furta.
"Barka dai Uwani me yake faruwa ne?" Daddy ya tambaye ta yana kallon yanayinta. Sai da ta saci kallon Jafar sannan ta ce.
"Wallahi Daddy ban sani ba, ina cikin banÉ—aki na ji ihun Ya Jafar, fitowar da na yi kenan zan bi shi na ga abin da yake faruwa." Ganin yadda Uwani ta rattabo bayani kamar ba ta san abin da yake faruwa ba ya sa Daddy ya aminta da ita, don haka ya furta.

"Ki É—auko hijabinki ki taho sashen Maminku." Daga haka Daddy ya juya, Jafar ya yi saurin bin bayansa.

"Ka sako kayanka mana Jafar." Daddy ya katse shi. Sai a lokacin Jafar ya lura daga shi sai singlet da gajeren wando.
"Uwani miƙo mini kayana." Uwani ta wuce ɗakin tana ƙumshe dariyarta ganin yadda Jafar ya tsure lokaci ɗaya. Tana miƙa masa kayan ya yi sauri ya sa, yana cikin saka riga Uwani ta janyo hijabinta za ta fita da sauri Jafar ya fisgo hannunta ya ce.

"Ina za ki tafi ki bar ni, ki jira ni mana na gama shiryawa. "A wannan karon sai da dariya ta ƙwacewa Uwani ta ce.
"Wai don Allah a wurin training ba a fitar da masu tsoro da marasa tsoro ne a cikin aikinku ne?" Jafar ya wurga mata harara.

Sai bayan da suka yi breakfast sannan Daddy ya kira Jafar, Uwani da Mami sannan ya fara magana.
"Dalilin da ya sa na tara ku bisa wata matsala da ke faruwa daga jiya zuwa yau, a baya ban yi niyyar sanar da 'yan uwana ba amma yanzu..."

"Daddyn yara babu fa buƙatar a tsaya ɓata lokaci, raba wannan auren shi ne mafi amfani a gare mu. Ina ji ina gani sheɗanu ba za su kashe mini ɗa ba, wannan yarinyar ba alkairi ba ce a wurinmu face annoba." Shiru Dadday ya yi yana sauraron Mami har ta gama. Sannan ya ɗora da cewa.

"Ka buɗe kunenka da kyau ka saurari abin da zan sanar da kai Jafar." Daddy ya furta rai a ɓace. Jafar ya gyaɗa masa kai, Daddy ya ci gaba.
"Ga Uwani nan ni da 'yan uwana da kuma mahaifiyarmu mun damƙa maka ita amana, wallahi ko bayan raina idan ka rabu da ita ban yafe maka ba." A hargitse Jafar ya ɗago, Mami na jin haka sai kawai ta rushe da kuka ta fice daga falon.

"Dama Daddy cewa na yi zan koma Lagos, saboda gidan nan ba ni da nutsuwa da shi." Jafar ya yi magana yana satar kallon mahaifinsa. Daddy ya jinjina kai ya ce.
Chapter 21 · 0% Book details