← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 71

Sashe 47

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dady har bakin gate ya raka Malam mai Baƙara sannan ya ɗauko sadaka mai kauri ya ba shi, yana shirin rufe ƙofa ya ga Adaidaita sahu ya sauke su Shukra ita da Salim. Kallon su ya yi duk a hargitse ko takalma babu a ƙafarsu, Shukra na ganin Daddy ta faɗa jikinsa ta fashe da kuka.
"Salim lafiya me ya faru? Ina Uwanin wani abu ne ya same ta?" Daddy ya tambaya a rikice.

"Alhaji ku ba ni kuɗina zan wuce." Mai Adaidaita sahun ya faɗa. Daddy ne ya zaro kuɗi ya miƙa masa, ya riƙe hannun Shukra suka shiga ciki Salim na biye da su fuskarsa duk ta yi zumu-zumu.

Suna shiga É—akin gaba É—aya aka bi su da kallo, sai a lokacin Daddy ya ce wa Lado ya fita ya zauna a waje. Har suka zauna kuka Shukra take, Baba Mustafa ya dubi Salim ya ce.
"Kai Salim lafiya me yake faruwa muka gan ku haka." Salim ya shafo gefen bakinsa da ya kumbure suntum ya ce. "Aljanun wannan yarinyar Uwani ne suka yi mana duka."
Da sauri Jafar ya ɗago kafin kowa ya yi magana ya ce. "Uwani kuma? Me ya kai Uwani gidanka?" Jafar ya faɗa rai a ɓace.
Daddy ne ya faÉ—a masa abin da Mami ta gaya masa dangane da rashin lafiyar Shukra da kuma tafiyar Uwani.

"Dama Uwani na da aljanu? An ya kuwa Shukra haka kawai Uwani za ta tayar da iska? Na tabbata ruwa ba ya tsami banza, dole akwai dalili." Daddy ya yi maganar yana kafe su Salim da kallo.

"Salim ne ya mare ta." Shukra ta faÉ—a, da sauri shi ma Salim ya ce. "Muka dai mare ta kema ba mari biyu kika yi mata ba?"
"To ƙarfina da naka ɗaya ne? Ai marinka ya fi nawa, kuma kai ma mari biyun ai ka yi mata..." A zafafe Jafar ya katse Shukra da faɗin.

"Ya isa! Don tsabar rashin mutumci matar tawa ce wani ƙato zai sa hannu ya mara? Kana da hankali kuwa Salim, wallahi sai na nuna maka kai ƙaramin ɗan iska ne gobe ba za ka sake aikata makamancin haka ba. Kuma daga yau ban lamunce Uwani ta sake zuwa gidan kowa ba tare da an sanar da ni ba." Saboda tsabar ɓacin rai Jafar ya manta da su Daddy da ke gabansa, daga Baba Mustafa, Daddy, Dada da Aunty ba ƙaramin daɗi suka ji ba ganin yadda hakan ya ɓata ran Jafar. Ban da Mami da ta yi sororo tana mamakin wai yau Jafar ne a gabanta yake iƙirarin Uwani matarsa ce, har a kan an mare yake tayar da jijiyoyin wuya.

Baba Mustafa ya dafa Jafar ganin jikinsa na rawa ya ce, "Zauna Jafar." A daƙile ya zauna yana huci zuciyarsa na ɗaci.

"Yanzu ina Uwanin take?" Daddy ya tambaya. Cikin haÉ—in baki a sanyaye suka ce.
"Mun baro ta a gida." Don yadda Jafar ya birkice musu ba ƙaramin tsorata suka yi ba. Jafar na jin amsar da suka bayar ya miƙe yana faɗin, Daddy ina key ɗin motarka zan je na ɗauko ta." Daddy ya ɗauko key ya miƙa masa don shi kansa ransa a ɓace yake, ya tabbata kuma duk wannan abin da ya samu sake ne daga wurin Mami tun farko.

Uwani sai bayan wani lokaci ta farka, ta kwashe kwanikan da ta kai su kitchen. Brush ta sake yi sannan ta fara haÉ—a kayanta tana murmushi, don ta san duk inda su Shukra suke yanzu sun kai wa su Daddy rahoton abin da ya faru.

Wayarta ta ɗauko ta ga misscall rututu, gaba ɗaya na Jafar ya fi yawa. Haka kawai ta ji gabanta ya faɗi, tana shirin kiransa ta ji bugun gida kamar za a ɓalle ƙofar. Ta window ta leƙa bayan Gali ya buɗe masa ta hango shi ya shiga cikin gidan. Zaro ido ta yi tana mamaki, da sauri ta buɗe ƙofa ta fita a lokacin har ya fara ƙwala mata kira. Turus ta yi a gabansa tana mamakin yaushe ya zo garin, ya ƙarasa gabanta a hankali ta ce. "Ya Jafar kaine da gaske, don Allah yaushe ka zo garin?" Ƙura mata ido ya yi ya ga fuskarta ta ɗan kumbura, ga kumburun mari ga kuma na baccin da ta yi. Bai amsa mata ba ya saka hannunsa ya shafa gefen fuskarta.

"Wuce mu tafi." Ya furta mata a taƙaice.
"Bari na É—auko jaka ta." Uwani ta yi maganar tana juyawa, a gaggauce ta É—auko jakarta da duk wani tarkacenta ta fito. Gali ya bi ta da ido yana mamakin yadda ta sauya lokaci É—aya kamar ba ita ce ta biyo masu gidan da gudu ba.

Uwani na shiga mota Jafar ya dube ta ya ce, "Uban waye ya ba ki umarnin zuwa gidan Shukra?"
"Mami ce." Uwani ta yi maganar tana É—auke kai gefe.

"Ba Mami ba daga yau ko Daddy ne ya ce ki tafi wani wurin ba ki sanar da ni ba wallahi sai na ɓata miki rai. Mami ce take aurenki ko ni?" Uwani ta taɓe baki ta ce.

"Ni fa kada ka sauke mini kwandon faɗa a kaina, atoh. Ba babarka ba ce, tun da ita ta haife ka kuma ita ta ce na zo gidan 'yarta sai na wani bi ta kanka. Wai ni Ya Jafar ma me ya kawo ka lokaci ɗaya?" Jafar bai amsa mata ba ya ci gaba da kallon titi. Uwani ta sake taɓe baki ta ce.

"Wallahi duk wannan shan ƙamshin da kake yi mini matsayinmu ya kusa zuwa ɗaya, ai saura bai fi shekara ɗaya da rabi mu yi candy ba. Idan na zama 'yar sanda sai mu dinga hura wa juna hanci." Uwani haka ta yi ta zuba ba tare da Jafar ya tanka mata ba har suka zo gida.

Faɗa sosai Daddy ya yi wa su Shukra, sannan ya sake jaddada maganar Jafar a kan koda wasa kada a sake tura Uwani wani wurin ba tare da izinin mijinta ba. Ya kuma ba wa Uwani haƙuri a kan abin da ya faru, shi kansa Jafar sai da Daddy ya haƙurƙurtar da shi sannan ya haƙura.
Daga haka kuma ya ce su tashi su tafi, ko Auta ba za ta je ta yi mata aiki ba. Idan har mai taya ta aikin suke buƙata sai dai Salim ya ɗauko mata mai aiki.

Shukra tana kuka haka ta saka ƙafa ta fita ita da Salim, da za su tafi gida ma sai Daddy ne ya ba su kuɗin mota. Lado ya ba wa Salim takalminsa ita kuma ta saka na Mami.

Miƙewa Jafar ya yi zai wuce sashensu, Aunty ta yi wa Uwani wani kallo da sauri ta tashi tana murmushi ƙasa-ƙasa don ta fahimci abin da take nufi. Da sauri ta je kusa da Jafar, ta saƙalo shi da hannu tana faɗin. "Wai Ya Jafar wacce tsarabar ka kawo mini? Ni fa ka san ciki na sa a gaba." Su Daddy murmushi suka yi, Dada cikin jin daɗi ta ce. "Oh Allah ka nuna mini ranar da zan ga 'ya'yan Jafaru da Uwani." Cikin sauri Aunty ta amsa da Amin. Wani malolon baƙin ciki ya turniƙe zuciyar Mami, tana raya sabon matakin da za ta ɗauka na wargaza tsakanin su, don ba ta fatan ta ga ranar da Uwani za ta haife jinin Jafar.

Kamar wani sa'anta haka Uwani take tafe tana sake saƙale shi sai kuma ta buga tsalle idan ta yi magana ɗaya biyu. Bai tanka mata ba har sai da suka shiga ya zauna a gajiya, a gefen kujerarsa ta zauna ta yi shiru ta ce. " Wai sai magana nake Ya Jafar ka yi banza da ni."

Kan kujerar da ya ke kai ya dawo da ita sannan ya shiga shafa fuskarta ya ce. "Ai ke ce ba ki iya tarba ba, dama haka sauran mutane suke yi wa mazajensu? Ko haka kika ga Aunty tana yi wa Daddy?" Da sauri Uwani ta rufe baki tana dariya ta ce, "Kambalastin ka ga yadda Aunty take ji da Daddy, yasin ko kunyarmu ba ta ji wani lokacin." Jafar ya saki murmushi ya ce. "To kin gani, ke kuma da kin gan ni sai dai ki tambayi tsaraba. Wai ma Uwani kina abin arziƙi a makaranta?" Uwani ta ɗan ɗaure fuska don ba ta san raini ta ce. "To Ya Jafar ka ɗauka asarar kuɗin tara Daddy yake yi? Bari ka ji in faɗa maka, to yanzu ni ce assistance monitor a class ɗinmu." Ya ji daɗi sosai a ransa sai ya basar ya ce. "Ke za a ba wa assistance monitor waye shaida?" Uwani ta tashi ta riƙe ƙugu sannan ta ce. "Ka tambayi Daddy mana, ai shi yake karɓo result ɗinmu." Jinjina kai ya yi sannan ya ce. "To zauna muyi magana." Jin yadda Jafar ya yi magana ya sa gaban Uwani ya faɗi don har ga Allah ta yi tsammanin maganar aurensa da Safna zai yi mata.

"Wannan zuwan da na yi na zo yin wasu cike-cike ne, sannan kuma na zo mu yi sallama da ku. Sakamakon In shaa Allah next week za mu wuce ƙasar Sudan, kasancewar sunana yana cikin jerin ma'aikatan da za a aika daga nan ƙasa Najeriya zuwa ƙasar Sudan. Domin kwantar da tarzomar da ke tashi a cikin ƙasar." Jin haka ya sa Uwani ta zaro ido waje, Jafar ya yi murmushi ya ci gaba da cewa. "Kin san aikinmu dama ya gaji yawo, don haka ina fatan za ki taya ni da addu'a. Saboda yanayin hatsarin wurin da za mu fuskanta, kuma dama tafiya ƙarin ilimi ce sannan duk abin da ya faru da bawa rubuce yake a cikin kundun ƙaddararsa." Jafar na zuwa nan a zancensa sai gani ya yi Uwani ta rushe da matsanancin kuka.

Littafin kuÉ—i ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624

#Ummou Aslam Bint Adam🌚

Kukanta yake ji har cikin ransa, ya janyo ta jikinsa a hankali ta sauke ajiyar zuciya yana buga bayanta cikin wata irin murya ya furta.
"Kukan kuma na mene ne?" Hawaye bibbiyu suka ci gaba da shatata daga idanun Uwani, ya saka hannu ya goge mata yana mamakin kukanta.
Chapter 47 · 0% Book details