← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 71

Sashe 67

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 idan littafi ya kammala 800 ne.🫠

#Ummou Aslam Bint Adam🌚
Murmushi Jafar ya saki jin kalaman Dada ya waiga wurin Dada sai kuma ya haÉ—e fuska yana faÉ—in. "Dada wai dama kin shigo ne?"
Dada ta riƙe baki ganin har lokacin Jafar na riƙe da Uwani ta ce, "Ina za ka san na shigo kana nan kana hurewa 'yar mutane kunne. Yanzu wannan wacce irin jarabar duniya ce Jafaru yarinya ko sati biyu ba ta yi da haihuwa ba, za ka saka ta a lungu kana naniƙa?" Jafar ya sake tsuke fuska ya ce.

"Wai Dada me ma ya shigo da ke alhalin kin ji miji da mata ne a ciki. Yanzu kuma idan kika gano wa idonki ki ce wa Ubangiji me?" Takaici ya sake rufe Dada ta kai wa Jafar duka a baya tana faÉ—in.

"Don ƙaniyarka ka zo ɗakina ƙiri-ƙiri ka ce mini na gane wa idona. Wallahi bari Mamman ya zo ba zan iya ba, na lura Jafaru so kake ka kai ni wuta ban shirya ba. Yanzu idon na ganowa idona tsiraici na ce wa Ubangiji me?" Dada ta ƙarasa maganar tana kallon Uwani da ta yi luf a jikin Jafar.
"Munafuka ashe dama kallona kawai kike Uwani, shi ya sa kika ɗaukar fushi da ni idan na kori Jafaru. To ki je don kanki wallahi indai Jafaru ne ina zaune za ki sake kwaso wani cikin." Ganin su duka biyun sun yi wa Dada shiru ya sa rai a ɓace ta juya tana kuka za ta fita, da sauri Jafar ya ƙarasa ya rungumo Dada ya dawo da ita suka zauna.

"Haba Dada me ya sa kike haka ne? Yanzu laifi ne don na zo ganin matata? Ke da kanki fa kin san laifin mai ƙoƙarin tarwatsa sunnar Ma'aiki." Shiru Dada ta yi tana nazari sannan ta ce.
"Ni fa duk ba wannan ba, Allah Ya sani tsoro kake ba ni Jafaru, haka kawai ka zo ka sake ƙunsa wa 'yar mutane ciki a ɗakina ina na kama?" Murmushi Jafar ya yi ganin ya fara cin galaba a kan Dada sannan ya ci gaba da yi mata daɗin baki.

Satin Uwani biyu da haihuwa aka yi taron suna, saboda aikin da aka yi mata. Ita da jaririnta sun yi kyau gwanin birgewa, su Aunty sai shige da fice take. Jafar ma bakinsa har kunne don ya lura Dada ta gama huce fushinta, tun da har ya ji tana maganar Uwani za ta koma bayan ta yi kwana araba'in. Auta amarya tun sassafe ita da Shukra suka dira garin Kura, Dada ba ƙaramin mamakin sauƙin kan Shukra take ba. Madina kuwa sai da ta biya ta wurin Mami wurin azahar sannan suka ƙarasa, Mami ta yi ƙoƙari matuƙa wurin haɗa kayan barka don shi kansa Jafar bai taɓa tsammani daga gare ta ba, musamman yadda ya san ta ɗauki karan tsana ta ɗora wa Uwani.
Taro ya yi taro gwanin birgewa, dangin mahaifiyar Uwani su kansu sun yi rawar gani wurin haɗo mata sha tara ta arziƙi. An ci an sha an yi hotunan cikin farinciki, facalolin Mami sai mamakin sauyin halin Mami suke yi da sauƙin kanta. A haka har aka yi taro aka gama kowa ya watse, gida ya rage sai tsirarun baƙin da suka zo daga nesa.

Abin duniya ne ya haɗe wa Safna sakamakon ganin yadda Jafar ya yi watsi da ita, tun tana sa ran ganin ya biyo gidansu ya zo biko ya mayar da ita har zuciyarta ta fara wasu-wasin kiransa a waya. Momynta ce take tausarta amma duk da haka ciwon son Jafar da shi take kwana take tashi, lokaci ɗaya Safna ta zabge ta yi wata irin rama. Ta shiga tariyo abubuwan da suka faru a zamantakewar aurensu da Jafar, haka kawai take zama ta ci kuka ta more idan abin ya dame ta. A cikin hakan ne ta fara rashin lafiya da ciwon kai mai zafi, zuwansu asibiti likita ya tabbatar wa da Mommynta hawan jini ya kamata kuma ciwon zuciya na barazanar kama ta. Hankalin iyayenta ba ƙaramin tashi ya yi ba sakamakon ita kaɗai gare su, a wannan lokacin ne kuma Mummynta ta ta yanke shawarar kiran Mami domin su sasanta, saboda Safna ko ta kira Jafara ba ya ɗauka. Idan kuma baƙuwar lamba ta sa ta kira shi da ya ɗaga idan ya ji muryarta ce sai ya katse. Wannan ta sa mahaifinta ya shirya ƙafa da ƙafa ya je ya samu Daddy, sai da ya gama zayyano jawabi cike da mamaki ya ce.

"Yaron nan ashe raina mini hankali ya yi da ya ce mini ya je wurin Safna sun gama daidaitawa? Alhaji ka yi haƙuri, kuma a gaskiya ya kamata ku sake lura da irin tarbiyyar Safna. Ba wai don Uwani tana 'yar ɗan uwana ba, wallahi da ace wata aka yi wa haka iyayenta ba za su amince ba. Kuma duk lalacewa mahaifiyar mijinta ai mahaifiyarta ce. Zan yi ƙoƙarin ganin na shawo kan Jafar ya mayar da ita, amma kuma matuƙar za ta dawo da halayenta magana ta gaskiya ba kowanne miji ne zai zauna da ita ba." Jinjina kai Mahaifin Safna ya yi don shi kansa ya fahimci kuskuren da suka tafka dangane da tarbiyyar Safna, soyayyarta ce ta rufe musu ido ya sa idan ta yi wani abin ba sa iya tsawatar masa. Sai da ya yi wa Daddy godiya sosai sannan suka yi sallama ya wuce gida. Bayan tafiyar mahaifin Safna ne Daddy ya kira Jafar ya ce yana son ganinsa cikin gaggawa. Lokacin da ya ƙarasa gida Daddy ya yi masa faɗa sosai sannan ya ce masa ya dawo da Safna.

"Daddy ka yi haƙuri amma gaskiya ni na gama zama da Safna, ba zan iya zama da matar da take neman illata iyalina ba kuma tana cin zarafin iyayena ba." Shiru Daddy ya yi sannan ya ce.
"Ya kamata ka ba ta dama a wannan karon tun da na tabbata a yanzu ta gane laifinta."
"Ko zan dawo da ita Daddy ba yanzu ba, sai nan da wani lokacin In Shaa Allahu." Amsa masa Daddy ya yi sannan ya sallame shi.

Wanka ya karɓi Uwani ba ƙaramin kyau ta yi ba, ta yi haske sosai ita da Hibban ba ƙaramin kulawa suke samu. Jafar kusan kullin yana hanyar Kura, wani abin da yake yi a kanta da Hibban a gaban mutane har kunya Uwani take ji.
Sannu a hankali kwanaki suka shuÉ—e har ta yi arba'in, kuma a wannan lokacin tuni an gyara wa Uwani sashenta da ke gidan Jafar saboda tariyarta.
Duk yadda Jafar ya dage a kan shi zai kai Uwani yawon arba'in ƙin yarda Dada ta yi, haka Dada ta fara saka su Baba Mustafa da Baba Yunusa suka dinga kai ta wurare suna dawo da ita. Wata unguwar kuma da babu nisa sai su tafi tare da Dada, duk inda suka je sai an yaba yadda Hibban ya yi ƙiba kamar ba jaririn kwana arba'in ba.

Dada da Aunty ne suka yi wa Uwani duk wani abu da ya shafi ɓangaren gyaran jiki na mata, kuma a wata ranar Asabar ne aka raka ta ɗakinta. Uwani har da kukanta lokacin da su Dada za su tafi. Baki sake Dada ta dubi Uwani ta furta.
"Wallahi idan ba ki rufe mini ba ki ba Uwani sai na dalla miki mari, kinibaye mu za ki yi wa bariki ki cuce mu muna zaune ƙalau? Wani sabon munafurcin kika tarko Uwani, ina ce haka Jafaru zai bi ki har ɗakina ya gama matse ki har idan na kore shi ki dinga gaba da ni. Amma shi ne yanzu za ki ɓarke mana da kuka, uban me za ki yi wa kuka to?" Uwani ta tura baki ta ce.

"Dada wallahi zan yi missing É—inku?"

Dada ta yamutsa fuska ta ce, "Au dama musun É—in har tsofaffi ake faÉ—awa? Wani abu ne haka?" Aunty ta yi dariya ta ce.
"Dada tana nufin fa za ta yi kewar mu." Jin haka ya sa Dada ta É—auki Salati tana tafa hannu sannan ta ce.
"Wai dama musun ɗin kewa kenan? Shi ya sa kullin Jafaru ya zo sai na ga Uwani ta maƙale kafaɗa kamar keken ɗinki tana cewa ta yi musun ɗinsa, wallahi ke dai an yi baƙar munafuka. Ashe ke kike yaudaro Jafaru ki ribato shi nake ganin laifin yaro, saboda lalacewar zamani Abuwa shi ma fa haka za ki ji Jafaru yana kashe murya idan yana yi mata magana. Ke ni wani lokacin ko maganarsu ba na ji a ɗaki sai dai fa na ji ƙusur-ƙusur, kuma idan na faɗa ɗakin su ga laifina. Don Allah mene ne laifina don na duba na ga halin da suke ciki tun da Uwani dai amanar Allah ce a hannuna." Aunty ban da dariya babu abin da take yi, kunyar duniya ya cika Uwani. Horn ɗin Daddy suka ji a ƙofar gida ya sa suka yi wa Uwani sallama suka fita, har bakin gate ta raka su tana shirin tura ƙofa Jafar ya kawo kai hannunwansa ɗauke da ledoji guda biyu.

Ledar hannunsa ɗaya ta karɓa, ya sakalo ta suka wuce cikin gida yana jin farincikin da ko da aurensa da Safna bai yi zumuɗin ranar ba.
Suna shiga falo Jafar ya wuce kitchen ya ɗauko plates ya fara juye sayayyar da ya yo musu, Hibban ne ya fara motsi Uwani ta ɗauke shi. Jafar ya karɓe shi ya fara jijjjiga shi, jin ya ƙi daina kuka ya sa ta karɓe shi ta ba shi ya sha. Bacci ya koma sannan ta kwantar da shi ta tofe shi da addu'o'i, tana ɗagowa Jafar ya rungomta ya haɗa ta da bango. Iska ya hura mata a fuska cikin shauƙi ya furta.

"Ban san da wanne suna ya dace na kira wannan ranar ba, amma Allah Ya sani zuciyata na cike da kewa da matsanancin farinciki." Shiru Uwani ta yi ta ɗan sunkuyar da kai ƙasa don haka kawai take jin nauyin Jafar, ɗago da fuskarta ya yi ya kashe mata ido ɗaya ya ce.
Chapter 67 · 0% Book details