Sashe 43
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ya'yana suna jin yunwa don haka za su zo su sha." Jin haka ya sa Lado ya fashe da kuka ya ce, "Don Allah ka yi haƙuri, yau ni na zama uwar bunsurai kenan?." Baba Mustafa ya kalli Lado da mamaki ganin yana magana shi kaɗai kuma yana kuka shaɓe-shaɓe. Yana shirin yin magana sai ji suka yi Lado ya zabura yana fisgar riga yana faɗin.
"Jama'a ku taimaka mini bunsuru zai danne ni! Wayyo ƙirjini, ya fara kiciniyar shayar da su." Da sauri Baba Mustafa ya matsa wurin Lado, a lokacin Daddy ya ƙarasa.
Kici-kici haka Lado ya fara kokawa da bunsurin har ya kwayewa Lado riga, hannuwa biyu Lado ya sa ya dafe ƙirjinsa yana nan kwance ya hango wasu ƙananan bunsurai biyu sun yo kansa. Da ƙarfi 'ya'yan bunsuran suka bankaɗe hannuwan Lado suka kafa bakinsu a jikinsa. Lado na jin haka take numfashinsa ya ɗauke, yaraf ya faɗi a ƙasa sumamme.
Mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskokinsu, Dada ta riƙo hannun Daddy cike da tsoro ta ce, "Mamman ka ga abin da nake nuna maka, wai ka lura da Lado ko idanuna ne?" Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Na gani Dada, amma ban taɓa ganin haka a tattare da shi ba." Baba Mustafa ne ya ɗauki butar Lado da ke gefe ya yayyafa masa ruwa, a zabure Lado ya miƙe yana dafe ƙirji yana faɗin.
"Zuƙata suke yi, wallahi ga su nan suna zuƙe ni. Wayyo ƙirjina 'ya'yan bunsurai suna zuƙe ni..." Daddy ya riƙe hannuwansa yana tofa masa addu'a, a hankali Lado ya dawo cikin nutsuwarsa ya fara bin su da kallo. Ya sauke kansa yana kallon ƙirjinsa sai kawai ya fashe da kuka ya ce. "Daddy dubi ƙirjina, ni kam na saddaƙar rayuwata ta zo ƙarshe. Wai yau ni ne bunsurai suke tsotsa, Daddy me ya rage ni ma ai na zama bunsuru." Cikin tasuyawa Daddy ya ce. "Me ya faru Lado, gaya mini." Jim Lado ya yi ya ce, "Zan faɗa maka komai, wallahi duk abin nan da ya faru da mu daga ni har Mami ita ce sila. Hajiya ta cuce ni ta cuci rayuwata, wallahi ita ta kai ni ga halaka. Don Allah ku kira mini Uwani na nemi yafiyarta." Shiru duka suka yi suna mamakin kalaman Lado, Daddy ya ciro waya ya kira Malam mai Baƙara ya ce masa yana son ganinsa akwai aikin gaggawa da zai gudanar.
"Kai Lado, dube ni nan. Ka faɗa mini me ka shuka wa Uwani kai da Saratu da na ji kana neman yafiyarta?" Dada ta furta tana tsare shi da ido. Lado ya share ƙwalla ya ce. "Hajiya ce ta sa nake kashe kaji da zakarun Uwani da suke mutuwa, ta yi mini barazanar za ta sa a kore ni daga aiki idan ban aikata ba." Lokaci ɗaya su Daddy suka ɗauki salati.
Kiran sallar asuba a kunnen Uwani aka yi saboda tsabar ciwon jiki ko baccin kirki ba ta yi ba, bayan ta yi sallah ta yi azkar ta kwanta a gefen katifa nan take bacci ya yi awon gaba da ita. Sai a wannan lokacin Uwani ta samu bacci mai daɗi, tana cikin bacci sai ji ta yi an sheƙa mata ruwan sanyi a kanta. A firgice ta tashi tana dube-dube, Shukra da ke sanye da wata figigiyar rigar barci ta ce. "Wai Uwani ke wacce irin daƙiƙiya mai ƙwaƙwalwar kifi ce? Ina ce jiya na faɗa miki aiki kika zo ba hutu ba?" Ran Uwani ba ƙaramin ɓaci ya yi ba ta ce.
"Amma me ya sa ba za ki iya tashina da hannunki ba har sai kin sheƙa mini ruwa?" Shukra ta matsa gaban Uwani cikin isa ta ce, "Zo ki rama, na ce ki zo ki rama idan ban karairaya ki ba." Uwani ta yi ƙwafa ba tare da ta tanka mata, don ta ɗaga mata ƙafa ne saboda cikin da ke jikinta. A yadda ta fusata gani take idan ta rufe ta da duka mai ƙwatarta sai Allah.
Fita Uwani ta yi ta ɗauko moper ta goge wurin, ta saka wani ɗan kwalin kayanta ta tsane ruwan kan katifar sannan ta nufi kitchen. Tana cikin kitchen ta ji fitowar Salim, saboda takaici da ya leƙa kitchen ɗin ko ƙurarsa ba ta kalla ba.
"Uwani ba ki ga Baby ba, ba shi da arziƙin da za ki gaida shi ne.?" Shukra ta furta a gadarance.
"Aiki ne ya kawo ni ba gaisuwa ba." Uwani ta faɗa fuska a haɗe, ta ci gaba da tattara kayan kitchen ɗin duk da gidan ba wani datti ya yi ba. Shukra ta riƙe baki ganin Uwani ta yarfa ta a gaban Salim, Salim ya jinjina kai ya ce.
"Baby wannan mai aikin Mamin lallai tana haƙuri da ita, har ta samu sukunin faɗa wa 'yan gida magana?" Shukra ta yi ƙwafa za ta yi magana Uwani ta katse ta da cewar.
"Me zan dafa da safe ko yanzun ma Baby ne yake sayo muku abin breakfast?" Shukra ta jinjina kai ranta na suya ta ce, "Tuwo nake sha'awa da miyar agushi..."
"Ba zan iya tuwo a farar safiyar nan ba saboda ina da school ƙarfe takwas." Uwani ta katse Shukra sannan ta ɗora da cewa. "Ki faɗa mini abin da zan iya sarrafawa kafin na fita, idan ba haka ba zan haɗa iya cikina." Shukra sororo ta yi tana kallon Uwani don yanzu ba ƙaramin mamaki take ba ta ba. Miƙewa Shukra ta yi ta naɗe hijabin da ta sako ta nufi wurin da Uwani ke tsaye, ba ta tanka mata ba kawai ta ɗauke fuskarta da mari. Uwani ta dafe gefen kumatunta tana shirin yin magana Shukra ta sauke mata wani marin a ɗayan kumatun ta ce.
"Kafin ki bar gidan nan sai na sauke miki iskancin da ke kanki..." Taaasss Uwani ta ɗauke kumatun Shukra da mari wanda ya yi sanadiyar maƙalewar maganar da take yi, Shukra ta saki baki tana kallon Uwani ba ta yi aune ba ta ji Uwani ta sake ɗauke fuskarta da mari. A fusace Salim ya ƙarasa ya ɗauke Uwani da wani azababban mari, Uwani ta yi gefe Salim ya fisgi wata wayar caja a gefe ya shiga zabga mata da ƙarfi.
Sosai Uwani take jin dukan na shigarta, ganin ba shi da niyyar daina dukanta ya sa ta ƙwalla wata irin ƙara sai kuma ta faɗi ƙasa yarafff.
Kallon juna suka shiga yi tsakanin Shukra da Salim, a tsorace Salim ya ce. "Ko suma ta yi?" Idanun Shukra suka ciko da ƙwalla ta ce, "Idan Uwani ta mutu a gidan nan na shiga uku, wallahi babu abin da zai hana Daddy bai maka ni a wurin hukuma ba." Uwani ta yi fakare tana sauraronsu, Salim da ƙirjinsa ke bugawa ya ce. "Ba kin ce 'yar aiki ba ce?" Shukra da hawaye bibbiyu ya fara zuba ta ce. "Wallahi ba 'yar aiki ba ce matar Ya Jafar ce, cousin sister ɗina ce." A razane Salim ya ce. "Matar Ya Jafar fa?"
Shukra ta ƙara gyaɗa kai hankali a tashe, wata irin dariya suka ji Uwani ta ƙyaƙyace da ita Sai kuma ta miƙe tsaye tana ƙwanbare hannuwa tana zare idanu. Salim ne ya fara ja da baya ita ma Shukra ta fara matsawa a tsorace har suka fito falo, da ƙarfi Uwani ta fisgo labulen falon ta yi wurin su Salim ta hau ranƙwala musu ƙarfen labule. Sai kuma ta wurgar da shi ta fara tafiya da baya-baya ta ce. "Yau kun shiga dubu ɗari uku, domin kun tsokalo wa kanku tsuliyar dodo. Kun taɓo mana Hakima dole a yi muku babban hukunci. Salim da tuni jikinsa yake karkawa ya ce.
"Don Allah ku yi haƙuri wallahi tsautsayi ne."
Uwani ta waiga da sauri tana zaro ido waje ta nuna shi da yatsa ta ce, "Tun da kai ka fara magana ya zama wajibi mu fara hukunta ka. Hukuzufu fisge masa ƙafa ɗaya ka wurga wa Shugabar mayun fararen aljanu ta cinye." Jin haka ya sa Salim ya buga ihu ya tsallako gaban Uwani ba tare da ya sani ba. Uwani ta fakaici Salim ta ranƙwala masa cokali a kansa, cikin azaba ya fasa kuka ganin haka Uwani ta faɗa kitchen ta ɗauko robar yaji. Tana fitowa ta ga suna rige-rige za su shiga ɗaki, da sauri Uwani ta ce.
"Idan kun shiga ma ba ɓuya kuka yi ba Ɗan bulluƙutu yana nan yana jiranku, shi da ma sare gaɓoɓin jiki yake yi." Cak suka tsaya, Shukra na kuka ta ce. "Don Allah ku yi mana rai wallahi ba za mu sake taɓa ta ba." Uwani ba ta kula ta ba ta miƙa wa Salim robar yajin da cokali ta ce. "Ɗan guzum ya ce ka sha cokali goma idan ba haka ba kuma zai gwagwaɗa maka, wato ya yi maka tsarki da shi."
Salima yana ji yana gani ya ɗebi cokali ɗaya ya tura a baki, ai kuwa sai ga ido, hanci da baki na zuba. Cikin hawaye ya tsugunna a gaban Uwani ya ce, "Don girman Allah ku yi haƙuri mun yi nadama."
Uwani ta tafi da gudu ta danne kusurwar bango tana faɗin, "A'a 'yar fincin kada ki fito, ki taimaka ki yi haƙuri wannan naman da kika samu a sannu za ki gana da shi, amma ki bari mai girma ya gama hukunta su." Ta wurga wa Salim wani kallo take ya sake dumbuzar yajin da cokalin ya cusa a baki. Lokaci ɗaya Salim ya ɓarke da kuka ya ce.
"Wallahi ni kam Shukra kin cuce ni." Shukra za ta yi magana Uwani ta ce. "Za ka yi wa matarka mari ashirin ƙwarara idan kuma ba za ka yi mata ba za mu sa aljanin da ya fi mu girman hannu ya yi mata saba'in." Jin haka ya sa Shukra ta ƙarasa gaban Salim ta ce, "Don Allah ku bari shi ya yi mini da kansa." Salim ya dubi fuskar Shukra, sai da ya lailayata da hannunsa ya share hawaye ya ce.