Sashe 41
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kin san shi dama arziƙi kashi ne taka shi ake Aunty Shukra, ni ban yi mamaki ba don babu a ɗakin mahaifiyata. Idan ban manta ba Dada ce mini ta yi da kuɗinta ta saya wa Mami samiru, wai ko iya kwanon silba aka kawo ta da su..."
A hassale Shukra ta ɗago ta ce. "Don uwarki magana za ki faɗa mini?" Uwani ta saki murmushi sannan ta miƙe tsaye ta saɓi jakarta ta furta.
"Kina buƙatar hutu Aunty Shukra kin san mai ciki ba ta buƙatar hayaniya, ni yanzu ina ne ɗakin da zan zauna na kai jakata?" Baƙin ciki ya mamaye zuciyar Shukra ganin Uwani na niyyar mayar da ita marar hankali, sai da ta yi ƙwafa ta ce. "Ga shi nan yana kallonki."
Uwani ta ɗauki jakarta tana tafe tana kallon falon a yamutse sannan ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, tana shiga wani zarnin fitsari ya doko hancinta. Ga dai ɗakin daga katifa sai ƙaramin mudubi da banɗaki, amma a mamakinta wanne irin zarni ne haka ita shukra da ba yara gare ta ba. Daga can wurin ƙofar banɗakin take jiyo warin na fitowa, ta sa hannu ta toshe hancinta ta tunkarin banɗakin. A yamutse ta dawo falo ta ce, "Aunty Shukra baƙi kika yi ne suka yi miki fitsarin kwance ne a ɗakin can?" Shukra ba ta tanka mata ba, ganin ba ta da niyyar tanka mata ya sa Uwani ta miƙe ta shiga ta sauya kaya, wata doguwar riga ta saka mara nauyi ta ɗora hula a kanta. Ɗakin Shukra ta shiga ta fara bin ɗakin da kallon mamaki a yamutse, saboda tsantsar shirgi da wari-warin da yake yi.
Mami da Auta na zuwa gida Auta ta wuce ɗakinta cikin fushi, Mami har ta gota ɗakin Lado sai ta dawo tana bin garken Uwani da kallon tsana. Ƙwanƙwasa ƙofarsa ta yi, a sanyaye Lado ya amsa yana zuro kai ta windo. Ganin Mami ya sa ya saki ajiyar zuciya ya ɗan washe baki.
"Hajiya barka da shigowa." Da ido take bin lado ganin wata irin rama da ya yi lokaci ɗaya don ko jiya da ta gan shi bai zuge haka ba, malolon fuskarsa ta kalla ta ce. "Lado me ya faru da kai haka? Na ga fuskarka duk a daddauje yau kuwa ka ma ci abinci kuwa?" Lado sai da ya saci kallon ƙirjinsa don kada Mami ta fahimci halin da yake ciki ya wayance da cewar.
"Hajiya abin duniya ne ya ishe ni." Lado ya É—an waiga yana hange-hange zai yi magana Mami ta ce.
"Ban gane abin duniya ne ya ishe ka ba, shi ya sa duk ka yi zumu-zumu kamar zakaran mayu?" Lado ya yi ƙasa da murya ya ci gaba.
"Hajiya a kanki ne fa abin yake shirin faruwa, dama É—azu ma na so yi miki magana sai jin fitarki kawai na yi. Dalilin da ya sa ma jiya na kasa kashe É—aya daga cikin awakin yarinyar can Uwani kenan." Mami cikin damuwa ta ce. "Ina jin ka Lado ci gaba."
"Hajiya jiya cikin dare na fita ina cikin garken Uwani na hango wata kamar Aunty wato kishiyarki, a can ta tsaya babu kaya tana ambatar sunanki tana wanka da wani irin ruwa. Hankalina ya tashi sosai Hajiya shi ya sa na gagara sukuni kin gan ni yau ko abinci ban ci ba, ni dai yanzu ki zo da daddare wurin biyu daren ki gane wa idonki don na ji ta ce aikin na kwana uku za ta yi. Kin ga sai a tona mata asiri a gaban kowa." Lado ya ƙarasa maganar yana nazartar Mami, ajiyar zuciya ta sauke ta furta.
"Kuma fa ka yi magana Lado, dama yau Daddyn yara zai dawo. Amma Abuwa an yi tsinanniya ni za ta sabauta? Yanzu Lado me na tsare mata a gidan nan?" Lado ya ɗan waiga don gudun kada wani ya ji zancen da suke yi asirinsa ya tonu ya ce, "Hajiya ki yi ƙasa-ƙasa kada ta ji ta gane shirinmu." Mami ta gyaɗa kai sannan ta ce. "Ita ma waccan shegiyar yarinyar dole ta daina wannan kiwon, ka tabbatar ka ƙara sayo shinkafar ɓeran nan." Lado ya jinjina kai sannan Mami ta wuce sashenta jiki a sanyaye, lokacin da ta shiga falo Aunty na zauna. Aunty na ganinta ta shiga tambayarta me jiki amma Mami ko ƙurarta ba ta kalla ba.
Uwani zagewa ta yi sosai ta hau yin gyaran ɗakin Shukra, ba ƙaramar jinjina wa Shukra ta yi a ɓangaren ƙazanta ba. Kayan wanki ma sai da ta ɗaure ya kai ƙulli uku, bayan ta gama ɗakin Shukra ta koma ɗakin da ta ajiye jakarta nan ma ta hau gyara shi sannan ta koma kitchen. Kwanukan da ta gani busassu har da waɗanda idan aka ce sun kusa sati a haka ba za a musa ba, sai da Uwani ta jiƙa su sannan ta wanke su suka fita.
Uwani na gama gyarawa ta kunna turaren wuta Shukra na kwance tana kallonta, lokaci ɗaya gidan ta ɗauki ƙamshi ita kanta Shukra yanayin ya birge ta. Bayan ta gama a wahalce ta faɗa kan kujera ta ce, "Me za a dafa Aunty Shukra?" A yatsine Shukra ta dube ta.
"Ki je ki É—ebi shinkafa ki dafa daidai ke, ni dama ba girki nake ba Baby zai taho mana da abinci." Uwani ta kalli Shukra kamar ta tanka mata sai kuma ta tashi, firji ta buÉ—e ta É—ebo kayan miya ta É—an jajjaga sannan ta yi miyar jajjage da farar shinkafa. Cikin galabaita Uwani ta sake zama za ta ci abinci Shukra ta furta.
"Kin wanke mini kayan ne da za ki zauna cin abinci? Wai ko kin É—auka ci ne ya kawo ki? Aiki kika zo yi mini yarinya sai kin gama komai za ki zauna." Uwani ta dafe kanta da ke yi mata ciwo ta ce. "Wallahi na gaji yau ba zan iya wanki ba sai gobe." Shukra ba ta tanka mata ba ta tashi ta nufo ta, a tunanin Uwani ko Shukra marinta za ta yi don haka ta É—an ja baya. Shukra na zuwa ta É—auki shinkafar gaban Uwani ta juye mata ita a kanta, sannan ta kai mata mari tana faÉ—in.
"Don uwarki ni sa'arki ce da za ki faɗa mini haka? Ko Jidda kin isa ki faɗa mata haka ballantana ni? Kada ki gan ni ban da lafiya wallahi kika ƙure ni naɗa miki na jaki zan yi."
Shigowar Salim kenan ya ƙarasa ya rungumo Shukra jikinsa yana faɗin, "Baby lafiya kike hayaniya haka? Kin manta abin da likita ya faɗa ne?" Tsaki Shukra ta yi ta ce. "Wannan jakar yarinyar ce ta ɓata mini rai, na ce ta wanke mini kayan sawa da wanda na ɓata tun ɗazu ta tsaya iskanci." Salim ya dubi Uwani a yamutse ya furta.
"Ke dama Mami ba ta faɗa miki aikin da za ki yi ba ne? Baby ko ba mai aikinku da Mami ta ce za turo ba ce?" Kalaman Salim suka ɓata ran Uwani da wulaƙancin da Shukra ta yi mata, ta sa hannu a hankali tana karkaɗe shinkafar jikinta. Takaici ɗaya yunwar da take ji ga kuma iya shinkafar farantin kaɗai ta dafa, ta riski muryar Shukra na faɗin.
"Ita ce mana, kasan ɗan ƙauye bai iya wayewa ba ai. Ba ta ga ta goge tana sa suturu masu kyau ba." Salim ya sake tallafo Shukra ya furta. "Ke gargaɗi zan yi miki, wallahi likita ya kafa wa matata dokoki domin samun lafiyarta da ta abin da ke cikinta. Idan har ta samu matsala ta sanadinki wallahi sai na ɗauki mummunan mataki a kanki, farin cikin Shukra shi ne nawa. Don haka duk abin da take so shi za ki yi mata." Daga haka Salim ya ja Shukra suka shige ɗaki, a ransa yana yaba kyawun gidan da ƙamshin da ke tashi don rabon da ya ga gidan ya yi kyau haka har ya manta. Uwani bayansu ta bi da kallo a hankali ta furta.
"Ashe kuwa zan gyara muku zama É—aya bayan É—aya."
Sai da Uwani ta gyara wurin sannan ta ɗebo kayan wankin Shukra ta fita gate ta fara wankewa, ba ita ta kammala wankin ba sai kusan sha ɗaya da rabi na dare. A galabaice ta koma ciki ta samu Shukra da Salim suna cin chips da ruwan tea, kitchen ta wuce ta ɓararraka taliya ta zuba ta wuce ɗaki ba tare da ta tanka musu ba.
Daddy sai da ya dawo Mami take sanar da shi rashin lafiyar Shukra, amma sai ta nuna masa Uwani da kanta ce ta ce za ta je ta taya Shukra aiki. Don kada Daddy ya yi faÉ—a sai Mami ta ce masa Salim ma baya gari, da ya samu Aunty da maganar tafiyar Uwani jin abin da Mami ta faÉ—a ya sa ta ja bakinta ta yi shiru, don wani abin ba ta so ta fiye shigewa tun da ta lura Mami mace ce mai makirci.
Kamar yadda Lado ya tsara wa Mami hakan ce ta kasance, ƙarfe biyun dare na yi ta fito a hankali kai tsaye ta nufi wurin garken Uwani. Da yake Lado a matse yake da ya samu a raba shi da ƙirjin jikinsa tun ƙarfe ɗayan dare yake duba agogo bai ji motsin Mami ba.
Cikin garke ya sa ta suka shiga a hankali ta ce, "Lado ya ban ganta ba." Lado na shirin yin magana Mami ta ji an ɗane mata baya, ta waiga a firgice za ta yi ihu ta hangi bunsuru a saman kanta ya ce. "Duk ihun da za ki yi a yanzu babu mai jin ki." Ganin bunsuru na magana ya sa Mami ta saki fitsari ƙafafuwanta na karkarwa. Bunsurin ya dira kan katangar da ke zagaye da garken ya nuna Mami da kofatonsa ya ce.
"Wato ke ce kike aiko Lado domin ya tarwatse kiwon Uwani ko?" Mami jiki na rawa ta ce. "Ba ni ba ce..." Taass ta ji saukar mari a kuncinta, nan take ta yi shiru tana hawaye. Bunsurun ya zayyane mata duk abin da ya faru tsakaninsa da Lado. Wani irin tsoro ne ya mamaye ta, nadama da da-na-sani suka shige ta. Sannan bunsurun ya É—ora da cewa.