Sashe 42
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kowannenku akwai hukuncin da zan yi masa, kuma na fara da kai Lado ka ga na ka sakamakon saura ke." Lado zai yi magana ya ji bakinsa ya yi ɓam tamkar an danne shi da dutse, bunsurun ya ƙarasa ya fisge ɗankwalin kan Mami. Tana son ta motsa abu ya gagara, bakinsa ya sa ya hura kan Mami nan take ta ji wata iska na shiga kanta. Ya sauka daga kanta ya ce. "Kuma idan kika kuskura kika bari Uwani ta dawo gidan nan sai na ba ki mamaki, don haka duk wani makirci da za ki yi don ta zauna a can gidan ki yi shi har sai na ba ki wa'adin dawowarta. Idan kuwa ta dawo gidan nan za ki yi kuka da idonki, ba dai so kike ta tafi can gidan Shukra ba? Yanzu ta fara zaman gidan, ku kuma yanzu za ku fara girbe abin da kuka shuka." Bunsurun na gama magana suka ga ya ɓace, ɓacewarsa ta yi daidai ta sulluɓowar gashin kan Mami gabaɗaya. Mami ba ta ankara ba sai ji ta yi kanta ya yi ƙwaryar molo babu ko ɗigon gashi, ta baya ta ji an shafo ƙeyarta a guje ta fice daga cikin garken. Lado kafin ya kai ɗakinsa sai da ya yi faɗuwa kusan uku.
Littafin kuÉ—i ne a kan 500 ta wannan Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala 800 neðŸ«
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
Mami saboda firgici da tashin hankali tana gudu tana dungurawa har ta shige cikin ɗakinta, tana shiga ta ji cikinta ya hautsina mata da rarrafe ta shiga banɗakin tun ba ta ƙarasa ba gudawa ta fara bin ƙafarta. Mami tana sakin gudawa tana kukan tashin hankali, a haka har ta gama ta cire kayanta ta gyara wurin. Kamar kazar da aka tsamo daga ruwa haka Mami ta faɗa kan gado yaraf, ta shafo kanta sai jin sa ta yi ya koma kamar bayan sulba. A haka gari ya wayewa Mami kafin asuba ta shiga banɗaki ya fi sau biyar, ko da gari ya waye jin ta shiru babu motsi ya sa Daddy ya leƙa ɗakinta. A kwance Daddy ya hango ta ta yi ringingine da alama ta lula duniyar tunani ba ta ji motsin shigowarsa ba. Sai da gari ya yi haske ta fahimci duk wata kafar gashi ta jikinta ta siɗe tamkar ba a taɓa tsirar gashi a jikinta ba, babban abin da ya fi ɗaga mata hankali bai wuce yadda ta ga gashin gira da na idonta sun siɗe fuskarta ta yi fayau ga goshin da kanta sun yi sanƙwalƙwal ba.
Da mamaki Daddy yake bin ta da kallo ya furta, "Saratu!" Jin kiran da Daddy ya yi mata ya sa Mami ta tashi a zabure tana kokawar rufe kanta.
"Me nake gani haka a kanki Saratu?" Daddy ya jefa mata tambaya cike da mamaki.
Idanun Mami suka ciko da ƙwalla amma da yake tsoro ya mamaye ta sai ta tattaro murmushin yaƙe ta ce. "Daddyn yara ai aski na yi jiya, wallahi kan ne ƙuraje ya takura mini. Gobe ma nake son ɗaukar azumi sai na yi ukuna a jere na huta." Daddy sake da baki yake bin Mami da kallo, don rabon da ya ga murmushinta har ya manta. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Saratu askin ne har da saman idonki kika kwashe? Me ya kai ki aske gira alhalin kin san bai dace ba?" Mami ta haÉ—iyi yawu mai É—aci ta ce, "Tsautsayi ne, da yake mai ne na fara gwada shi a gira ta na ga ko yana da kyau, ina wankewa na ga ya kwashe mini gashi." Shiru Daddy ya yi yana dubanta, alamunsa ya nuna rashin gamsuwa da zancenta.
"Allah Ya kyauta! Sai ki yi ta Istigifari kuma nan gaba kada ki sake wannan gangancin." Daddy ya furta yana fita daga É—akin.
Mami na ganin Daddy ya fita ta kife a kan gadon ta rushe da wani irin kuka, da yake Daddy bai yi nisa ba jin gunjin kuka ta ya sa ya sake turo ƙofar. A zabure Mami ta tashi zaune tana goge hawaye, Daddy ya yi mata kallon tsaf ya ce.
"Saratu an ya babu abin da yake damunki kuwa? Kukan me na ji kina yi." Mami ta rasa ƙaryar da za ta yi wa Daddy tun da ga hawaye nan shaɓe-shaɓe a fuskarta, don haka ta ce. "Kuka nake saboda saɓon da na yi wa Ubangiji, don Allah Daddyn yara ka ta ya ni addu'ar Allah Ya yafe mini kuskuren da na aikata." A wannan karon ma Daddy kallonta ya yi cike da tuhuma, ya jinjina kai sannan ya fice daga ɗakin.
Lado na zaune a cikin ɗakinsa daga shi sai singlet yana shan iska saboda zafi sai ya ji bugun ƙofa, tun da wannan al'amarin ya same shi ya daina kwanciya shan iska a gate. Bugun da ake yi da ƙarfi tamkar za a ɓalle ƙofar ce ya razana shi, a guje ya fita ya zare sakatar yana faɗin. "Wai waye haka ne ana zuwa!"
Cikin gajiya da bugun ƙofar Dada ta ce.
"Uwar Mamman ce, Lado ko iyaka za ka yi mini da ganin ɗana?" Lado ya shafa kai yana murmushin yaƙe ya ce. "Ni na isa Dada!" Lado ya yi maganar yana russsunawa ƙasa ya furta.
"Ina kwana Dada."
Karaf idanun Dada suka sauka a kan ƙijin Lado, da sauri Dada ta ja baya tana dafe ƙirji, ita dai a iya saninta da Lado ba ta taɓa ganin wannan sabuwar hallitar a jikinsa ba. Ta sha zuwa ta same shi babu riga yana wankin motar Daddy, amma ba ta taɓa ganin haka ba.
"Ko dai gamo na yi?" Dada ta raya a ranta, a tunanin Lado ko Dada ba ta ji shi ba sai ya sake cewa.
"Ina kwana Dada?" Da sauri Dada ta yi ciki tana faɗin, "Lafiya ƙalau Lado ai tuni na amsa maka." Ta ci gaba da sauri kamar za ta tashi sama, Dada tana tafe tana waige. Lado sai a lokacin ya fahimci saurin da Dada take yi, cike da faɗuwar gaba ya shige ɗaki jin Baba Mustafa ya turo ƙofar yana sallama. Rigar sanyin da Lado ya saba sakawa ita ya mayar sannan ya leƙo yana dariyar yaƙe ya gaida baba Mustafa.
Kamar wacce aka biyo da gudu haka Dada ta faÉ—a falon cikin sauri, Daddy da Aunty suna zaune suna hira suka ji sallamar Dada. Da murna suka tarbe ta Daddy ya ce. "A'a Dada yau ke ce a gidan sannu da zuwa."
Dada jiki a sanyaye ta ce, "Ɗan uwanka Muɗɗafa ne ya kawo ni, yana can ƙofar gida." Daddy ya ce, "Au me makon ya shigo kuma." Daddy har ya nufi hanyar fita Dada ta ce.
"Mamman dawo ka zauna!" Ganin yanayin sanyin jikin Dada ya sa Daddy ya dawo a sanyaye, musamman da ya tuna ko waya ba ta yi masa ta ce za ta zo ba. Don É—abi'ar Dada ce ba ta zuwa sai ta kira shi.
"Mamman ni dama mutum yana zama mata-maza da girmansa kuwa?" Daddy ya yi jim sannan ya ce. "An ya kuwa Dada? Duk da dai ba ɓangarena ba ne amma ba na jin haka za ta faru, matuƙar dai mutum da girmansa ne." Dada ta zuba hannuwa biyu ta yi tagumi a fili ta ce. "To ko gamo na yi ne Mamman?"
"Gamo kuma Dada?"
"Alƙur'an yadda na ga Lado da ƙirjin mata Allah Ya nuna mini Annabi. Idan kuwa haka ne ni dai gamona yi, Allah Ya sani Mamman gidanka nema yake ya fi ƙarfinka yanzu." Dada ta ƙarasa maganar tana hawaye.
"Ni dai a iya sanina da Lado ba shi da wata hallitar mata Dada, kin manta Lado fa tun bai fi shekara goma sha biyar yake yi mana gadi." Dada ta miƙe tana share ƙwalla ta furta. "To ni dai Saratu ta janyo wa zuri'ata masifa." A daidai lokacin Mami ta fito an sha ɗaurin ɗankwali an yi shar, Mami ta ɗan saki fuska ta gaida Dada. Saboda tun abin da ya faru tsakaninta da bunsurun nan wani irin tsoro ya shiga ranta, take tsoron kada ta yi wani abin a wani daren ta sake gamuwa da gamonta.
Dada na shirin amsa gaisuwar Mami sai gani suka yi an fisgi É—ankwalin kan Mami an yi wurgi da shi, gaba É—aya mutanen wurin babu wanda bai lura da abin da ya faru ba. Dada da Aunty suka saki baki cikin mamaki.
"Saratu mene ne haka?" Dada ta tambayi Mami tana ja da baya, Mami ta yi murmushin yaƙe sannan ta yi wa Dada bayanin da ta yi wa Daddy.
Dada gaba ta yi tana jinjina kai ta ce, "Mamman ni kam Allah ya ba mu alheri, gaskiya ina da abin yi a gida." Duk yadda Daddy ya so Dada ta haƙura ko zuwa yamma ne ta kai fir ta ƙi amincewa.
Tun bayan da Lado ya gaisa da baba Mamman ya fara jin kukan 'ya'yan akuya a cikin kunnensa, waige ya fara saboda a kunnensa yake jin yadda suke tsalle da dire-dire a harabar gidan. Ganin baba Mustafa na tsaye yana danna wayarsa ya fahimci shi kaɗai yake jin wannan kukan awakin. Yana nan tsaye ya hangi su Dada sun fito, daga gefensa ya ji an taɓo shi yana waigowa ya ga bunsurun nan a gefensa ya ce.