Sashe 61
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Zo Autar daddy mana." Auta ta yi É—akinta tana faÉ—in, "A'a Hajiya Aunty ni ma yanzu kaya zan cire na kwashe tuwo." Murmushi Aunty ta yi ta wuce É—akinta.
Da daddare bayan sun gama cin abinci Aunty ta dubi Auta ta ce, "Auta ba na son iskanci na lura tun da kika dawo bakinki akwai magana, wai wanne albishir ne?" Sai da Auta ta tashi ta saka sakata a ƙofa sannan ta koma ta zauna murya can ƙasa ta ce, "Aunty don girman Allah ki yi mini alƙawarin idan na faɗa miki babu wanda za ki faɗawa, ciki kuwa har da Daddy." Jim Aunty ta yi tana mamaki ta ce. "Shi kenan na yi miki."
"Yau dai ƙafa da ƙafa na je na gano 'yarki Uwani, kin ga yadda ta sauya kuwa?" A zabure Aunty ta ce. "Ke Auta da gaske?" Auta ta saki dariya sannan ta kwashe duk yadda suka yi da Uwani, sosai Aunty ta ji daɗin labarin kuma ta sake alƙawarin ba za ta sanar da kowa ba. Haka ta ce za ta saka lokaci ta je ta gano ta, har lambar Uwani ta ba wa Aunty suka ci gaba da tattaunawa dangane da Uwani.
Uwani tana zaune ta ga baƙuwar lamba ta shigo mata, a hankali ta ɗauka sannan ta yi shiru. Daga can ɓangaren ta ji muryar Aunty na faɗin, "Wai dama 'ya za ta guji uwarta ban sani ba." Jin muryar Aunty ya sa Uwani ta saki ihun farinciki tana faɗin. "Sai Hajiya Aunty da kanta."
"Ke kunna data na kira ki video call 'yata ta ce mini jikata ta mayar mini da ke uwar mata." Aunty ta furta tana katse kiran. Nan take Uwani ta kunna data, babu jimawa kiran Aunty ya shigo mata. Ba ƙaramin mamaki Aunty ta yi ba ganin yadda Uwani ta yi ƙiba kamar ba ita ba.
"Yata wai dama za ki yi ƙiba?"
A kunyace Uwani ta saki murmushi.
"Zan tambayi Dadynku fita In shaa Allah next week za ki ganmu." Uwani ta amsa sannan ta ce. "Aunty Ina Abid na san yanzu ya manta ni ko" Aunty ta haska wurin Abid da ke bacci ta ce. "Kin gan shi can kayan rigima bacci yake." Cikin wata irin kewarsu ta ce.
"Na yi kewarku sosai Aunty." Daga haka sai Uwani ta fara ƙwalla.
"Idan kuka za ki dinga yi mini ba zan sake kiranki ba, so kike ki sa kanki a damuwa kina fama da kanki ne?" Uwani ta goge hawayenta tana girgiza kai. Sun jima suna hira sannan ta miƙa wa Innarta bayan sun gaisa suka yi sallama.
"Maryama yanzu haka za a ci gaba da azabtar da mijin yarinyar nan kenan? Don Allah ki samu Dada ki ba ta haƙuri a kan zaman yarinyar nan ko yaron nan ya samu sukuni." Aramma ya furta cike da damuwa.
"Wani abu ya faru ne malam? Ko zaman Uwani ne ka fara gajiya da shi?" Ajiyar zucuya Aramma ya sauke sannan ya ce.
"Wallahi mijin yarinyar nan kusan zuwansa shida kenan ƙofar gidan, kuma duk zuwan da zai yi sai dai na ƙirƙiri wani uzurin na faɗa masa. Ko na ce kin yi tafiya, ko kuma na ce kin je unguwa. Zancensa ɗaya ina Uwani take. Kwanaki sai da ya kai har sha biyun dare a ƙofar gidan nan yana zaman jiranki, da yake ranar na ce kun je garin su Indo. Ni ina ganin da za a roƙi Dada ya ci a ce ta sauko yanzu." Har a cikin zuciyarta tana son zaman Jafar da Uwani domin yana da hankali da nutsuwa, Maryama ta dubi Aramma ta ce.
"Malam ba a nan gizo yake saƙar ba, idan ba ka manta ba matsalar ba daga wurin Jafar ba ce. A wannan karon Dada na yin yaƙi ne da Saratu, wallahi na tabbata Dada ba za ta yi abin da zai cutar da Uwani ba. Yadda ta kawo mana ita take ci gaba da ba ta kulawa, mu kawo ido mu zuba mata. Duk wannan abin da yake faruwa watarana sai labari." Jinjina kai Aramma ya yi, a ransa yana tausayin yanayin da yake ganin Jafar.
"Mommy akwai fa matsala, wallahi tun da muka yi aure na rasa gane kan Jafar. Na fahimci yana cikin damuwa kuma na lura akwai abin da yake ɓoye mini. Na farko tun da muka yi aure ko sau ɗaya bai taɓa kai ni familynsa daga na Daddy har na Mami ba, kullun magana ɗaya yake mini ba shi time sai weekend. And kowanne weekend ya zo akwai uzurin da yake ba ni, Mommy ni fa ina zargin akwai budurwar da ta ɗauke hankalinsa because wani lokacin ko a cikin bacci haka za ki yana cewa Jidda" Safna ta ƙarasa maganar hawaye na zuba. Daga can ɓangaren Mommy ta ce.
"Ki daina zubar da hawayenki a banza kin san dai mu ba irin zama da kishiya ba ne. Mahaifiyata har ta koma ga Allah ba a yi mata kishiya, ni ma kuma ga ni da Daddynki har tsufa ya zo. Sai ke ƙanƙanuwarki za a yi wa kishiya? Ƙyale shi zan kira mahaifiyarsa na ji abin da yake faruwa, yanzu za ki ga aiki da cikawa. Kin san Hajiya Saratu da kuɗi, yanzu zan jefe ta 'yar dubu ɗari biyu. Ina me tabbatar miki har haƙuri sai ya ba ki." Farinciki fal fuskar Safna suka yi sallama.
A ranar da Jafar ya koma daga wurin aiki kallon sama-sama ta yi masa saboda yadda Mommy take nuna mata za su saye mahaifiyarsa, shi ma bai bi ta kanta da don abinci ma gabaÉ—aya cokali bai fi biyar ya ci ba. Dama kuma idan da sabo ta saba da haka, damuwa ce ta mamaye shi da tunanin Uwani da halin da take ciki musamman da a 'yan kwanakin nan yake yawan mafarkinta.
Mami na zaune ta ga alert É—in dubu É—ari biyu daga akawunt É—in Hajiyan Safna, jiki na rawa ta tafi lalubo lambarta sai ga kiranta ya shigo mata.
"Hajiya da kanki haka ai da kin bari na kira." Mami ta furta murya na rawa.
"Kai haba Hajiya Saratu ai an zama É—aya, ya gida ya yara?"
Mami ta wayance ta amsa don babu wanda ta taɓa nuna wa ba ta gidan Daddy, hatta Hajiya Falmata duk yadda suke ba ta taɓa sanar da ita ba. Sai da suka gama gaisawa sannan Hajiyan Safna ta fara wassafo ƙorafin Safna, lokaci ɗaya Mami ta fututtuke tana nuna laifin Jafar. Sannan ta ɗora da cewar.
"Allah na tuba ma wane maganar budurwa ko zancen ƙarin aure? Jafar ɗin nawa yake kuma duka yaushe suka yi aure? Ban da ma auren zamani ya ci a ce har an fara samun saɓani ne? Amma ki bar ni zai zo ya same ni Hajiya." Mami ta furta sannnan suka yi sallama, har Hajiyan Safna ta kashe Mami ba ta daina bambaɗanci ba.
"Wallahi Saratu kin saka kanki a wahala, kwaɗayi dai mabuɗin wahala ne. Ke yanzu a ƙaramar ƙwaƙwalwarki kina ganin wannan ɗan abin da matar nan take ba ki ya fi mutumcinki? A tunaninki har abada ba za ta fasu cewar Jafar na da wata matar har da ciki ba? Yanzu idan watarana suka tabbatar da matar yaron nan har da ɗanta ko 'yarta me za ki ce wa mahaifiyar yariyar nan da ita yarinyar?" Matar mahaifinta ta furta cike da takaici. Cikin halin ko inkula Mami ta ce, "Kafin lokacin zan daidaita komai, ni yanzu ma can gidan Daddyn yara zan je na ba shi haƙuri don na gaji da zaman kaɗaici 'ya'yana suna can wata ƙatuwa na mora."
Inna ta saki shewa haÉ—e da buga cinya ta ce.
"Ai Saratu kin daÉ—e da yin sake, wallahi kin yi sake É—an zaki ya girma amma za ki ce na faÉ—a miki, ke dai a juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe."
Suna gama magana Mami ta kira Jafar ta dinga yi masa faɗa a kan abin da Hajiyan Safna ta faɗa mata, Jafar shiru ya yi yana sauraronta sai da ta gama faɗan sannan ya ba ta haƙuri suka yi sallama.
Wata galleliyar atamfa Mami ta saka hannu da ƙafa sun sha ƙunshi gwanin birgewa, sai da ta rangaɗa ɗaurin ɗankwalinta sannan ta nufi gidan Daddy. Ta yi sa'a ta same shi yana zaune a baranda, da murmushi ta ƙarasa wurinsa tana faɗin.
"Ranka shi daÉ—e hutawa ake?" Kallonta ya yi lokaci É—aya ya ga duk ta lalace, ta É—an yi duhu ga ramar da ta yi.
"Me ke tafe da ke?"
Russunawa ƙasa Mami ta yi ta fara jera masa ban haƙuri, sai da ya gama sauraronta sanna ya ce.
"Saratu ai ba ni za ki ba wa haƙuri ba, ki je ki samu Dada idan har ta huce a kan Uwani za ta koma ɗakinta fani'ima, ko yanzu Uwani ta dawo za ki dawo ɗakinki. Ai maganar mai sauƙi ce, akasin haka kuma kin ga shi kenan dama kowa ya sayi rariya ai ya san za ta zubar da ruwa."
Aunty ce ta ƙarasa wurin hannunta ɗauke da jug ta dire a gaban Daddy, ganin Mami ya sa ta ɗan faɗaɗa fara'arta tana faɗin.
"Aunty Saratu ina kwana." Sai da Mami ta goge ƙwallar idonta sannan ta amsa.
"Lafiya ƙalau Zainabu ya kwanan yaran?" Aunty ta amsa sannan ta fara ƙoƙarin barin wurin. Da sauri Mami ta tare ta tana faɗin.
"Don Allah Abuwa ki taya ni ba wa Daddyn yara haƙuri."
Jikin Aunty ba ƙaramin sanyi ya yi ba ganin mace mai isa da izza kamar Mami, tana zubar da ƙwalla har tana roƙonta a kan ta ba wa Daddyn yara haƙuri. Aunty na shirin magana Auta ta nufo wurin hannunta ɗauke da Abid yana kuka, turus ta yi ganin Mami a tsugunne tana hawaye. Ganin haka ya sanyaya mata jiki, ta ƙarasa wurin tana faɗin.
"Mami yaushe kika zo?" Mami ba ta iya amsa mata ba sai ƙwalla da ke zubo mata. Har cikin zuciyarsa Daddy bai ji daɗin yanayin da ta riske su ba. Don haka ya dubi Mami ya ce.
"Ki wuce gida an jima zan je na samu Dada za mu yi magana." Hakan ne ya ɗan ƙarfafa gwiwar Mami ta miƙe ta yi wa su Aunty Sallama ta fice daga gidan.