Sashe 64
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da Aunty ta fita ba ta samu ta gama sallamar mutane ba sai gab da za a tashi daga hall ɗin, sai da ta damƙa wa Shukra duk abin da ya kamata sannan ta shiga wurin Uwani ta yi mata magana suka fita. A daidai kuma wannan lokacin Jafar na cikin motarsa ya ɗora kai asitiyarin motarsa cikin damuwa da ɓacin rai. Ta jima ta hangensa a cikin mota har suka wuce wani irin abu na yawo a cikin jikinta.
Can titi suka fita suka tari adaidaita sahu suka wuce gida har lokacin Uwani ba ta daina jin zuciyarta na yi mata zafi ba. Lokacin da suka koma gidan babu kowa don haka suna zuwa sashen Aunty ta karɓi doguwarta mara nauyi bayan ta yi wanka ta saka, ta kwanta tana tunanin rayuwar da suka yi da Jafar a baya.
Su Aunty sun jima da dawowa sannan sauran 'yan bikin suka dawo har da amarya.
"Maman baby me ya sa kika son azabtar da ɗan'uwana? Me ya sa kike son horar da shi alhalin ba laifinsa ba ne? Wallahi-wallahi yau duk wanda ya ga abin da Ya Jafar ya dinga yi sai ya tausaya masa, me ya sa ba za ki saurare shi ko da na ɗan mintuna ba ne." Auta ta furta a sanyaye don ma'auratan ba ƙaramin tausayi suke ba ta ba.
"Auta na san waye Ya Jafar, matuƙar zan tsaya saurararsa kema kin san ba zai taɓa bari na koma wurin Innata ba. Kuma ko Kur'ani zan haɗiya Dada ba za ta yarda da ni ba." Auta ta dafe kai cike da damuwa sannan ta furta.
"Yanzu shi kenan haka za ku ci gaba da rayuwa? Na san abin da Mami ta yi sam ba ta kyauta ba, amma nake ganin yanzu ta gane kuskurenta. Me ya sa Dada ba za ta haƙura ki koma ɗakinki ba." Uwani ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Kin san an ce duk abin da babba ya hango yaro bai isa ya hango shi ba, addu'a dai ita ce mafita. Kuma wallahi ban ce ki sanar masa ina nan ba, idan ba haka ba na yi miki rashin mutumci."
Auta ta taɓe baki ta ce, "Munafuka ji yadda take magana kamar gaske, da zan fallasa ki ai tuni a wurin zan faɗa masa. Tun da ni ce mutum ta farko da ya fara kira ya tambayi wurin da kike." Uwani ta yi murmushi ta ce. "Ki taɓo mini Aunty Shukra idan za ta tafi ni zan bita yau a gidanta zan kwana." Auta ta riƙe haɓa sannan ta ce.
"Oh! Yau nake ganin ikon Allah ƙiri-ƙiri mata na gudun mijinta, ai shi kenan sai mu rankaya mu kwana a can. Na san gudunki dai kada ya zo nemanki nan."
Uwani haka ta zauna a É—akin Aunty don kada wani ya fitar da rahoton ya ganta a cikin gidan, sai da Shukra za ta wuce gida kusan goman dare sannan Auta da Uwani suka sulale jiki suka bita. Suna hanyarsu ta zuwa gidan Shukra Jafar ya sake kiran Auta yana tambayarta Uwani, ta ce masa ita ma da ta dawo gida ba ta ganta ba. Babu yadda ya iya haka ya katse wayar a lokacin yana harabar gidan Daddy, bayan ya yi aike ya fi goma a kan a gano masa Uwani a É—akin Aunty.
Jafar da ya runtse ido Uwani yake gani tana sakin murmushi tana yi wa Aura liƙi, tunani da fargabarsa a wurin da Uwani za ta kwana ga shi ga dukkan alamun da ya gani cikinta ya tsufa. Ya gagara fasalta irin kyawun da ya ta sake yi, ta sake zama babbar mace tamkar ba Uwaninsa ba.
Ba shi ya koma gida ba sai kusan sha biyun dare, a lokacin da ya je Safna na zaune ta cika fam. Saboda tun a hall da Jafar ya fita ba ta sake ganinsa ba. Ko amsa sallamar da ya yi ba ta yi ba, yana shirin wuce ta da sauri ta sha gabansa.
"Wacce 'yar gidan uban waye ta sha gabanka da har ka dizga ni kana ambatar sunanta a wurin Kamu." Kai tsaye Jafar ya ce.
"Wata mai muhimmanci ce a rayuwata."
Wani ashar Safna ta ƙunduma za ta sha gabansa ya janye ta gefe a shige ɗaki, ɗakin da yake ajiya kayan tarkacen aikinsa ya shiga tana shirin tura ƙofar ta ji ya saka sakata a jiki. Safna ta yi bugun dunjya Jafar ya yi banza da ita, cike da takaici ta koma ɗaki ta faɗa kan gado ta fashe da matsanancin kuka. A ranta ta raya za ta je ko gidan Daddy ko wurin dinner Auta, don ta ci alwashin a wannan karon ko wace ce sai dai a yi wacce za a yi a tsakaninta da ita.
Washegari ne ya kama ranar dinner Auta, kuma Uwani ta ƙudure a zuciyarta ba za ta je ba. Lokacin da Shukra ta shirya za ta je gida ta ce su shirya su tafi Uwani ta ce ita za ta yi zamanta, Shukra ba ta takura mata ba ta shirya ta fita. Wurin sallar azahar ne Auta ta dawo gidan bayan ta je ta gano yanayin decoration ɗin da aka yi ita da Madina.
Yamma liƙis ne kuma Auta ta ce wa Uwani ta shirya za su tafi wurin mai kwalliya amma fir ta ƙi yarda, ganin da gaske Uwani ba za ta ba ya sa ta kira Aunty kamar za ta yi kuka ta sanar mata.
Aunty ce ta ce a miƙa wa Uwani wayar ai kuwa ta rife ta da faɗa, Uwani ta tura baki gaba ta ce. "Ni fa Aunty ba don komai ya sa na ce ba zani ba ɗan ciwo-ciwo nake ji kamar fa haihuwa zan yi!"
Salati Aunty ta saki don ta gano ƙarya Uwani take ta ce, "To ki shirya idan haihuwar ta zo a hall ɗin sai na saka ki a ɗaki na karɓi haihuwar taki." Uwani ta saki murmushi don ta gane Aunty ta gano ta. Sai da Aunty ta yi wa Uwani da gaske sannan Uwani ta zumɓuri baki gaba ta suka shirya, abokin Dr ya zo ya ɗauke su suka wuce wurin make up.
A wannan ranar wani narkakken leshi Uwani ta saka wanda aka yi mata ɗinkin doguwar rigar. Abinka da mai jiki ga kuma cikin jikinta ba ƙaramin kyau ta yi ba, ita kanta ta yaba da wankan da ta ɗauka don haka Auta ta shiga zolayarta.
Jafar yana daga cikin mutanen farko da suka fara zuwa hall ɗin, don a wannan ranar ya ci alwashin ko sama da ƙasa za ta haɗe babu mai hana shi tafiya da matarsa.
Bayan an gama yi musu make up Dr ya zo shi da abokinsa, suka ɗauki Auta da ta sha doguwar rigar tsadaddan lace-material. Ba ƙaramin kyau ta yi ba, Uwani kuma ta yi wa Shukra waya a kan ta biyo wurin make up ɗin, za su wuce su karɓo jakunkunan gift da suka bayar. Sai kusan bayan isha'i suka ƙarasa da yake sun tsaya ƙara wasu tarkacen kayan gift ɗin a ciki. A lokacin da suka shiga hall ɗin ya cika da mutane sosai, Uwani na zuwa ta ji an saki waƙar Mamana. Da sauri ta buɗe jaka ta fara yi wa Auta da Dr liƙi, Safna ko da ta je wurin tana lura da yanayin Jafar, uffan ba ta ce masa saboda koda gari ya waye ba ta tanka masa ba. Idanunta na kansa tana kallon yanayinsa da shige da ficensa.
Yana daga zaune kamar an ce ya kalli wurin ya hango Uwani kamar dai jiyan, tana yi wa Auta liƙi tana ɗan jujjuyawa, wayarta ta ji tana ƙara da sauri ta ɗaga tana fita daga cikin filin. Muryar ƙawarsu Na'ima ta ji tana tambayarta kwatancan layin, don mai adaidaita sahu ya shiga layin hall ɗin da ita ba ta gane ba.
Fita daga cikin hall ɗin Uwani ta yi tana yi mata kwatance saboda ƙarar ƙidan da ke tashi, hakan ya sa Jafar ya rufa mata baya jikinsa har rawa yake. Safna na ganin Jafar ya fita ta suri jakarta ita ma ta bi bayansa, don ta ci alwashin sai dai a yi wacce za a yi.
Can wajen gate Uwani ta tsaya sai da ta gama yi wa Na'ima kwatancan layin da za ta shigo, waigowar da za ta yi idanunta suka sauka a kan Jafar da ke bayanta. Kallon-kallo suka fara wurga wa junansu kowannensu ƙirjinsa na bugawa, lokaci ɗaya jikin Uwani ya fara karkarwa. Abubuwa da dama game da mijinta suka bijiro mata, ta yunƙura da niyyar wucewa Jafar ya sa hannu biyu ya riƙo ta da iya ƙarfinsa ta faɗa jikinsa, ya riƙe ta ƙam tamkar wani zai ƙwace ta. Ɗago kan da za ta yi suka sake haɗa ido a karo na biyu, kusan lokaci ɗaya gabaɗaya suka sauke ajiyar zuciya sai kawai ta cusa kanta a cikin ƙirjinsa. Safna da ke baya kusan mutuwar tsaye ta yi ganin mijinta na rungume da mace.
Jama'a magana ta gaskiya wanga wuri ya kusa sumar da ni, shi ya sa na gagara Æ™arasa typing. Mu haÉ—e idan Allah ya kaimu🤠HaÉ—uwar masoya kusan wata 9 is not easyðŸ«
Littafin kuÉ—i ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 idan littafi ya kammala 800 neðŸ«