Sashe 10
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Waye wancan a tsaye?" Na Madina ya nuna Jafar a daidai lokacin Uwani ta leƙo don jin abin da yake faruwa daga ita sai gajeren wandon jikinta, ta tuɓe riga ta rufa hijabinta a saman ƙirjinta. Dada ta kai kallonta wurin ta ce, "Jafaru ne sai Uwani da ta fito."
"Amma a rigar kwasam na san ba za ki manta Iron Alto ba?" A firgice Dada ta kalle shi, ba ita ba hatta Jafar ya san labarin Iron Alto a bakin Dada. Dada na shirin magana Malam na Madina ya katse ta.
"To Ta'adar Iron Alto na ji waÉ—annan yaran suna aikatawa..." Tun bai rufe baki ba Dada ta saki butar hannunta wacce ta É—auro alwala da ita jiki na rawa.
Yau dai bari mu tsagaita dariyar na ga jiya har da masu shiɗewa 😂
07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
SHAFI NA SHIDA
Dada ta zuba musu ido ganin yanayin da Uwani take ciki ya sa ta aminta da kalaman ɗan'uwanta, ta san dai ba zai taɓa yi musu ƙarya ba. Runtse idonsa Jafar ya yi yana fesar da iska mai zafi, ya buɗe idanunsa da suka rine jawur kamar gauta ya sauke su a kan malam Na Madina. A fusace ya ƙarasa gabansa ya cukwikwiyo babbar rigarsa ya riƙe shi wuri ɗaya rai a ɓace ya furta.
"Wallahi ba don ina duba tsufanka ba, da yau sai na bambamce maka tsakanin zuma da maÉ—aci." Jafar ya sake shi sannan ya wuce É—akinsa, saboda tsoro tuni malam Na Madina ya yi mutuwar tsaye. Dada ta bi bayan Jafar da kallon tsoro baki a sake.
"Yaya an ya Jafaruna ne ba aljanu ne a kansa ba..." Kuka ya katse maganar da Dada take yi.
"Sharrin ƙwaya ce Kulu, na sha faɗa miki wannan aikin ɗamarar ba zai haifar da samun ɗa mai ido a cikin zuri'armu ba. Yanzu wa gari ya waya? A ce Jafaru bai san Kano garin Musulunci ba ne? Ya ɗauka rayuwar da yake yi a Legas ita zai yi a gidan nan. Kin ga dai abin da ya faru a gabanki. Da fa dukana zai yi, kaico rashin haihuwa ne ya ja mini haka." Na Madina ya fashe da kuka, Uwani da ke gefe ko a jikinta ta shige ɗaki ta ci gaba da sauya kaya. Don ita hakan da ya faru ma daɗi ta ji, ko ba komai ta san Jafar da zuciya ba lallai ya sake shiga sashen Dada ba sai bayan kwana biyu, ballantana ya hora ta a kan laifin da ta yi masa.
Tana gama sauya kaya ta fice a nan harabar gidan ta ga Lawan da matarsa Fanteka, 'ya'yan ta É—ibo ta yi hanyar keji da su uwar ta rufa musu baya. Sai da ta dawo ta ga Lawan yana tsince-tsince a wurin akuyoyinta.
"Kai dai Lawan ka cika ɗan kishiya riƙon mai haƙuri, wallahi da kiwon ka aka ba ni da ka ja mini zagi a ce na bar ka da yunwa." Uwani ta yi maganar tana ƙoƙarin kama shi, Lawan ya yi tsalle zai dira a kan katangar gidan Baba Isuhu da ƙyar ta kama shi tana sakin murmushi.
Kai tsaye sashen Dada ta wuce tana shiga ta ci karo da Jafar ya fito É—auke da jaka a kafaÉ—a.
 "Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Yaya ka ga yaron nan saboda ya san tsiyar da ya shuka fita zai yi ya bar mu, ni dai wallahi Sa'idu ya cuce ni duk wannan abin da yake faruwa Sa'idu ne sila." Jafar bai bi ta kan su Dada ba ya fice daga gidan har yana hankaɗe Uwani.
"Kulu Allah Ya ba mu alheri, wallahi Jafaru ba zai yi mana turun jeka ka mutu ba. Ya shuka bishiyar tsiya mu da ba mu ji ba, ba mu gani ba mu girbe masa." Malam na Madina ya sake jan jaka ganin haka ya sa Dada ta ce.
"Ka jira ni yanzu zan kira Inusa dole ya tara mini 'yan'uwansa a gidan." Dada ta yi maganar tana faÉ—awa É—aki domin É—auko wayarta.
"Inusa a yanzu ba sai gobe ba ka tara mini 'yan'uwanka, wallahi idan ba haka ba zan bar muku gidanku na shiga duniya. Kuma ku yi gaggawar kiran Jafaru ku ce ya dawo don zaman nasu ne, shi da Uwani ne suka ƙulla tsiyar da bakina ba zai iya furtawa ba." Daga haka Dada ba ta sake cewa uffan ba ta kashe wayarta, da kashe wayar babu jimawa Baba Yunusa ya sake kiranta, Dada na ɗauka ta ce.
"Yunusa wai wa muke yi wa Sallah da azumi?" Daga can ɓangaren Baba Yunusa ya ce.
"Allah."
Dada ta sake haɗe fuska kamar yana ganinta ta ce. "Da ma saboda na fita haƙƙinka a matsayinka na babba shi ya sa na kira na sanar da kai, wallahi idan ba ka haɗo mini kan 'yan uwanka ba sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba." Dada za ta katse da sauri Baba Yunusa ya ce. "Shi kenan Dada ga mu nan zuwa yanzu In shaa Allah." Ta amsa masa sannan ta katse wayar, sai da ta lallami Na Madina sannan ya mayar sa akwatinsa.
Falon tsit ya yi da ka kalli fuskokinsu ka san kowanne yana cikin damuwa, Baba Yunusa ne ya yi ƙarfin halin cewa.
"Dada gaba ɗaya ga mu mun hallara." Jafar tun da ya sunkuyar da kai ƙasa zuciyarsa ke tururi, Uwani na raɓe a gefe sai raba ido take kamar ƙosan sadaka.
Ganin haka ya sa jikinsu ya sake yin sanyi, don sun tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa.
 Sai da Na Madina ya kalli Jafar da Uwani sai ya sake fashewa da kuka, ganin haka ya sake raunata zuciyar Dada ta ja gefen mayafi ta fara sharce hawaye sannan ta fara magana.
"GabaÉ—ayanku na tabbata idan za ku yi mini shaidar Allah da Annabi, za ku yarda da abin da zan faÉ—a." Suka amsa mata cikin haÉ—in baki. Dada ta ci gaba da ce wa.
"Wallahi ƙanin mahaifinku Sa'idu ya cuce ni cutar ta har abada, amma ya je ba ni ya yi wa ba zumuncin Allah ya yi wa kuma ranar gobe ƙiyama sai igiyar zumunci ta zarge shi. Ni dai ba zan shiga tsakaninsa da Ubangiji ba amma sai mun tsaya a gaban Ubangiji ni da shi." Sororo gaba ɗaya suka yi hankali a tashe suna kallonta. Baba Yunusa ya ce.
"Dada me yake faruwa haka ne Baba Sa'idu fa? Baba Sa'idu da ya zame mana bango madafa kuma majingina, mutumin da ya maye gurbin mahaifinmu..."
"Inusa wa ya samar maka aikin Sojan nan? Kuma wa ya samarwa É—an'uwanka Mamman aikin ÆŠansanda, shi kuma wancan Rosofti?" Dada ta Katse shi.
"Duka Baba Sa'idu ne ya samar mana Dada wani abu ne ya faru?" Ya tambaye ta a sanyaye.
"Aikin É—amarar ba shi ya kai Jafaru Lagas ba?" Duka suka amsa mata, jin furucin Dada ya sa Jafar ya É—ago a fusace. Dada ta cigaba da faÉ—in.
"Silar haka ai ga shi muna shirin samun Iron Alto na biyu a cikin gidan nan." Jin kalaman Dada ya sa gaba ɗaya suka ɗauki salati hankali a tashe. Baba Isuhu ya wurga wa Jafaru wani mugun kallo cike da ƙyama, yana riƙe da haɓa hannunsa ɗaya kuma na riƙe da mai sunan Malam.
Sai da ɗakin ya lafa da hayaniyar da ake yi sannan Na Madina ya ce, "Wallahi ba tun yau ba shi ya sa magana ta a kullin yaran nan a aurar da su, amma da yake nasara ya hure muku kunne sai ku ce yara sai sun yi karatu. Yanzu dubi garsamemen ƙato kamar Jafaru a ce bai yi auren fari ba, ni wallahi ina kamarsa da Allah Ya ba ni haihuwa da na yi 'ya'ya uku. To yanzu me ya fi wannan haushi? Wa ya sani ma a Lagas ɗin ko 'ya'yan ƙedarai ne suka suke buɗe masa idanu, yake wartar ɗaya bayan ɗaya yana sakayewa a gefe. Ga shi nan yanzu ai ya gagara haƙuri ya ja Uwani ɗakin Kulu suna watsa wa sunnar Ma'aiki ƙasa a ido." Kamar haɗin baki gabaɗaya mutanen ɗakin suka furta. "Innalillahi Wa'inna ilahirraji'un."
 Duk budurin da ake yi ko a jikin Uwani ita babbar damuwarta ba ta wuce ta samu ta tsira daga horon Jafar ba, don ta san yadda ransa ya ɓaci idan ta shiga hannunsa sai Allah. Ran Jafar ya kai matuƙar ƙololuwar ɓaci don haka a zuciye ya buga tsaki haɗe da miƙewa zai fice daga ɗakin.
"Wallahi matuƙar Jafaru ya fita daga ɗakin nan Mamman sai ka bi ɗanka, tun da ni da ɗan'uwana ba mu isa da shi ba." Dada ta yi furucin rai a ɓace.
"Koma ka zauna Jafar." Mahaifinsa ya furta murya a dashe saboda ɓacin rai.
 "Daddy wai ba ka ji me waɗannan mutanen suke faɗa ba ne? Wannan wanne irin abu ne. A ce a rasa ƙazafin da za a yi mini sai na zina, kuma na rasa da wa zan yi sai Uwani yarinyar da ƙazanta ta samu gurbin zama a ilahirin jikinta..." Na Madina ya katse Jafar sakamakon rarrafowar da ya yi, ya dafa ƙafarsa. Kwanciya na Madina ya yi a gabansa sannan ya fashe da kuka.
"Don Allah kada wanda ya hana Jafaru ya rufe ni da duka, dama ɗazu ka so dukana to ka saka bindiga ka tashi kaina a kan waɗannan magangun da kake faɗa mana ni da 'yar uwata." Na madina ya furta ƙwallah na zuba, idan ka ga yadda yake rusar kuka sai ka rantse da Allah wani abin aka yi masa.
"Ba na son sakarci ka koma ka zauna Jafar." Mahaifin Jafar ya buga masa tsawa. Sai da ya haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ya koma ya zauna yana wurga wa su Na Madina harara, ya sunkuyar da kai ƙasa cikin ɓacin rai. Baba Inusa da kansa ya ƙarasa ya tashi Na madina ya koma mazauninsa sannan shi ma ya koma ya zauna.