← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 71

Sashe 34

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jin kalaman Daddy ya yi daidai da jin mummunar faɗuwar gaban da ta mamaye shi ba tare da ya yi tsammani ba, lokaci ɗaya jikinsa ya ɗauki karkarwa idanunsa suka yi jawur. Hannu ya sa ya dafa bango yana jin wata irin juya na ɗibansa, wani irin gumi ne ya shiga keto masa da ƙyar ya samu sukunun kallon mahaifinsa ya furta. "Daddy me yake faruwa!"

"Sai wani abu ya faru? Umarni ne kawai na ba ka..."
"Don Allah Daddy idan wani laifin na yi maka ka gaya mini don na gyara kuskurena." Daddy ya kafe Jafar da kallo yana nazartarsa sannan ya ce. "Babu wani abin da ka yi mini, ka je kawai zan yi nazari a kai." Daddy na gama magana ya shige ta ƙofar baya.

Tun bayan da Daddy ya kira Jafar su Momma suka fito daga mota Shukra ta fito ta tafi da su, can sashen Mami ta kai su aka shiga tarbarsu cikin mutumci da karramawa. Mami sai yaƙe take don kar a fahimci halin da take ci, nan suka baje aka shiga hira Hajiyan Safna na yi mata Allah sanya alheri da kuma jajen abin da ya faru ranar kamu.

Jafar na ganin Daddy ya tafi kai tsaye sashensa ya koma don a tsammaninsa wani abin Uwani ta samu Daddy ta gaya masa, ganin ba ta nan ya sa ya saki ƙwafa rai ɓace ya kwanta a kan kujera yana jin ƙirjinsa na zafi. Wata irin tsanar Uwani ta tsargar masa yana ayyana irin hukuncin da zai yi mata idan ta shiga hannunsa.
Yanan nan zaune ya ji kiran Safna ya shigo wayarsa, sai da ya É—an saita nutsuwarsa sannan ya É—aga.
"Baby ina ka tafi ne." Jafar ya saki murmushin yaƙe ya ce. "Daddy ne ya saka ni wani aikin amma na gama ki fito gate mana, kin san ciki mutane sun yi yawa." Amsa masa Safna ta yi sannan ya katse wayarsa ya fice.
A É—an zagayayyan wurin hutawa mai É—auke da kujeru suka zauna, Safna ta kalli Jafar cike da so ta ce.
"Hubby kamar ba ka yi missing ɗina ba, duk na ganka wani some how." Jafar ya saki murmushi ya ce, "Burin zuciya da ruhina mallakar farincikin da koda ina cikin baƙin ciki tunaninta na yaye mini shi. Kin kasance walƙiyar da ke haske birnin zuciyata, kallon fuskarki na mantar da ni wanzuwar hallitar kowacce 'ya mace a doron ƙasa. Lafazinki na ratsa mini lungu da saƙon majiyar sautina, tamkar busar sarewar da ke nishaɗantar da me sauraro. Tsayawa surutanta siffa da tsarin hallitarki tamkar giɓi ne ko wata iyaka da zan yi miki domin kyawunki ya zarce tunanin mai tunani. Mallakarki shi ne babban buri da muradin raina a duk bugun numfashin da ke fita daga ruhina, rashinki a kusa da ni kan jefa ni a tekun damuwar da jin muryarki ne kaɗai ke iya yi mini zabarin da zan iya fitowa daga ciki. Ina ƙaunarki Cutie, ƙaunar da ba zan iya fasaltata ba har ƙashen rayuwata." Jafar ya ƙarasa maganar yana sakar mata murmushi, hannu ta sa ta rufe fuskarta. Suka ci gaba da hirar soyayya, lokaci ɗaya Jafar ya nemi damuwar da yake ciki ya rasa.

Uwani ganin asirin Mami ya tonu ya sa ta shiga yi wa Dada shagwaɓa son ranta, jin Dada ta sake maimaita maganar tafiya gida da ita ya sa Uwani ta zumɓuru baki gaba ta ce.
"Dada ni fa gaskiya ba zan bi ki ba, sharri ne dai Mami ta yi mini ni dai na yafe mata. Nan fa Dada na haɗa shayi da kaina na saka madara son raina, wallahi ko kallon banza Ya Jafar ba ya mini. Ke kuwa idan na haɗa shayi kin dinga mitar zan shanye miki kayan shayi, gaskiya nan na fi cin daɗi. Ga alkakina da dublan nan kullin sai na ci, sugan ma da biredi nake ci. Wai Dada ba ki ga na yi ƙiba ba?" Dada ta yi ƙwafa cikin jin haushin Uwani ta ce, "Sakaryar ba a ƙaunarki a wuri kina manne sai ki yi ta zama ai." Uwani ko a jikinta ta kwanta a cinyar Dada. Abin da ta saka wa ranta za ta ci gaba da zama a gidan Mami tana karta mata rashin mutimci, ita ma tana karta mata nata.

Wuni guda Jafar da Safna tare suka yi da juna, bayan la'asar ya ɗauke ta a mota suka dinga zaga gari. Shi ne saya mata wannan saya mata wannan, har sai gabanin magriba suka dawo gida. A wannan lokacin ne kuma 'yan matan gidan suka fara shirin tafiya Dinner, Shukra ce ta kira Safna ta ce mata ta shirya za su tafi wurin make up. Jafar ya ce su tafi shi da kansa zai ɗauke ta ya kai ta, idan an gama yi mata kwalliya ya ɗauke ta su wuce hall ɗin tare. A wannan karon ma Uwani ita da Auta tare suka tafi wurin kwalliya, Auta da kanta ta shiga ɗakin Uwani ta zaɓo mata kayan da za ta saka. Wani dakakken leshi ta ɗauko mata sky blue da ratsin adon ja, an yi mata ɗinki doguwar rigar bubu. Make up ɗin da aka yi wa Uwani ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, saboda hodar da aka yi mata amfani da ita duk kalar fatarta ce. A wannn karon da ta kalli kanta a mudubu bayan an yi mata ɗaurin ɗankwali ba ƙaramin kyau ta ga ta yi ba, bayan an gama yi wa Auta kwalliya suka wuce a lokacin ƙarfe takwas na dare ta yi.

A can gidan Mami kuwa tun da Dada ta ga an fara shiryawa za a tafi wurin Dinner Dada ta ce Allah Ya kashe ta ba za ta ba, don ta ce babu yadda za a yi ta sake zuwa sheÉ—anu su dinga kawo farmaki. Daddy ma yana barandarsa yana ganin duk wainar da ake toyawa, a rasa yana mamakin hali irin na Mami.

Hall ɗin ba ƙaramin kyau ya yi ba, Shukra ita da Salim aka sauke a bakin hall ɗin. Ƙawayen shukra da suka yi anko ne suka fita a jere cikin birgewa, wani narkakken material Shukra ta saka an yi mata ɗinkin amare irin gown ɗin nan wanda yake ja daga baya. Uwani na zaune sai raba idanu take don a wannan karon hall ɗin ba ƙaramin tashin kanta ya yi ba, har a ranta tana wasu-wasin ko za ta iya aiwatar da ƙudurin da ta zo da shi. Tana nan zaune su Shukra suka shigo gwanin birgewa, take kallo ya koma kansu don kowa ya yaba da tsarin shigar da suka yi daga amare, ƙawayen amare har abokan ango.

Mami zaune take a kujera ita da su Hajiyan Safna, kallo É—aya za ka yi wa tufafin jikinsu ka san an narka dukiya a wurin. Musamman Mami da ta saka wani É—anyen leshe mai walwali da É—aukan ido, ta sha kwalliya É—aurin nan ya yi dass tamkar ba ta ajiya su Jafar ba.
Shigar su Shukra babu wuya Uwani ta miƙe za ta fita waje, don ta samu ta ga tsarin wurin ta yadda take so ta samu damar baza manufarta, saboda ta ci alwashin sai ta ƙunsa wa Mami baƙincikin da zai kafa mata tarihi a kundin rayuwarta. Tashin da za ta yi idonta ya sauka a kan Jafar da ke zauna a wata kujera shi da Safna, lokaci ɗaya ƙirjin Uwani ya buga don ko ba a faɗa mata ba tabbata ta kusa da Jafar ce Safna, duba da yadda suke sakarwa juna murmushi suna hira cikin so da ƙauna. Ƙwalla ce ta ciko mata ido ba tare da ta san dalilinta ba, ta haɗiyi yawu mai ɗaci. Tana shirin fita suka haɗa ido da Jafar, kallonta yake tamkar ya ga sabuwar hallita. A hankali ta janye idonta ta fice daga cikin hall ɗin, da sauri Jafar ya miƙe ya kalli Safna ya furta.

"One minute love."
Bai jira amsarta ba ya bi bayan Uwani, a can wani ɗan dandamali ya hango ta. Zamanta babu jimawa ya hango wani matashin saurayi ya ƙarasa wurinta, sallama ya fara yi wa Uwani a hankali ta goge hawayenta ta amsa masa.

"Mai kyau lafiya kike kuka kuwa?" Matashin ya furta a daidai lokacin da Jafar ya ƙarasa wurin.
"Kaina ke ciwo!" Uwani ta furta a sanyaye.
"Kai! Me kake yi a nan?" Jafar ya furta a tsawace.
"Dama beb É—in nan ce ta yi mini shi ne..."

"Ku me ya sa wani lokacin ba ku da hankali ba kwa tantance matar aure da budurwa ne?" Da sauri matashin ya riƙe baki ya ce, "Mai gida don Allah ka yi haƙuri ban san tana da aure ba." Jafar bai amsa masa ba sai aika masa da harara yake yi.

"Me ya fito da ke nan za ki zo kina kuka, har wani ƙato ya dinga ce miki mai kyau?"
"Me ya sa ko korar mini saurayi?" Uwani ta wurga masa tambaya ita ma. Ran jafar ya sake ɓaci a ɗan tsawace ya ce, "Za ki amsa mini ko sai na ɓata miki rai."
Chapter 34 · 0% Book details