← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 71

Sashe 20

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can saman window Uwani ta hango Mami na ziro kai tana leƙen abin da yake faruwa, Uwani ta ɗaga kai tana wani gwale fuska ta nuno Mami da sandar hannunta ta ce. "Keeee me leƙen nan! Wallahi za mu mayar da fuskarki ƙeya, mu ɗebo ƙafafunki mu dawo da su ƙirjinki. Shi kuma ƙirjinki mu mayar da shi gadon bayanki." Tun Mami ba ta gama jin abin da Uwani ke faɗa ba ta yi saurin banke gilas ɗin window. Lado na ganin ya ɗan samu sarari ya zuba uban ihu ya nufi sashen su Mami a guje. Uwani ta rufa masa baya tana tafe tana ranƙwala masa sanda a baya, Lado ban da ihu babu abin da yake saki.
Jafar da ke cikin ɗakin Lado ya yi sharkaɓa da gumi jikinsa ban da karkarwa babu abin da yake yi. Lokaci ɗaya ya ji zazzaɓi ya rufe masa jiki, a lokacin da ya ji Uwani ta bi Lado a guje da sauri Jafar ya ja zani ya tura kansa a ciki yana kalmar shahada.

Lado na tura ƙofar sashen Mami ya tura ƙofar da datse da sakata jiki na rawa, da ƙarfi Uwani ta fara kartar ƙofar tana faɗin.
"Za mu jijjige ƙauren gidan mu shigo, mu banka wa mutanen cikin gidan wuta. Ko kuma mu burtso ta ƙarƙashin ƙasa mu kwashe ku tass."

A guje Lado ya shiga cikin gidan, da ɗakin Mami ya fara cin karo don haka ya banka da ƙarfin gaske ya faɗa ciki. Mami na kwance a kan gado cikin bargo ban da karkarwa babu abin da jikinta take yi, jin an yi sufa a kan gadon da take ciki an shige bargo ya sa ta yi tsammanin ko Daddy ne shi ma aka tsora ta yake neman ɗauki.

Sai da Uwani ta tabbatar da Lado ya gama tsurewa sannan ta yarda sandar ta nufi sashenta, kayan jikinta cire ta saka wata doguwar riga har ƙasa sannan ta shiga banɗaki ya wanke fuskarta ta haye gado ta kwanta abin ta.

Duk budurin da ake yi Daddy da su Shukra sam ba su sani ba, da yake Daddy ya tsaya nafilfulu bai kwanta da wuri ba. Kwanciyarsa babu jimawa bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi, da ma Mami ba É—aki É—aya suke kwana ba tun ranar da ya je mata da maganar auren Jafar ta yi masa yaji take kwana a É—akinta. Don haka ko da suka tare a sabon gidan ma, ba ta sauya zani ba.

Daga Mami har Lado babu wanda ya gane wanda yake kusa da shi, don haka sai da asuba ta yi Lado ya zuro kai a hankali. A daidai lokacin Mami ta É—ago kai karaf suka haÉ—a ido da shi, a zabure Mami ta ja da baya fuska a murtuke ta ce.
"Lado! Uban me ya kawo ka É—akina?"

Sai a lokacin Lado yake bin É—akin da kallo, don shi dai bai san lokacin da ya shiga ba. Hankali a tashe ya furta.
"Hajiya wallahi sai dai idan kawo ni aka yi! Wallahi ba ni na kawo kaina ba. Aljanun da suka biyo Jafar ne suka kawo ni..." A zafafe Mami ta katse shi.

"Fita don Ubanka Lado." Kamar sabon munafiki haka Lado ya fita yana waige-waige, kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana cikin tashin hankali. Banɗaki Mami ta faɗa ta ɗauro alwala ta yi sallar asuba, da yake gari ya yi haske sosai fita ta yi ta nufi sashen Uwani. A lokacin da ta fara buga ƙofa Uwani tana kwance, ta fara magana.
"Waye?"

"Uwarki ce." Mami ta amsa a taƙaice.
Babu musu Uwani ta buɗe ƙofar ta furta. "Ina kwana..."

"Riƙe gaisuwarki, ina Jafar yake?" Uwani ta wara hannuwa ta ce. "Ni ma ban wayi gari na gan shi ba, yanzu nake shirin zuwa na tambaye ki." Rass gaban Mami ya faɗi, da sauri ta fice daga sashen Uwani ta nufi wurin Lado da ke zaune a kujera yana jin rediyo.

"Lado ba ka ga fitar Jafar ba?" Mami ta tambaya.

"Hajiya ai Jafar na cikin ɗakina tun daren jiya, yanzu haka na yi-na yi ya buɗe wallahi ya ƙi, ni tsorona ma kada mutanen ɓoyen nan su dawo su tarfa ni a wurin nan." Lado ya ƙarasa maganar wasu tagwayen ƙwalla na zuba. Mami ba ta ƙarasa jin maganar Lado ba ta nufi ɗakin tana bugawa.

"Son buɗe mini ƙofa Maminka ce." Daga cikin ɗakin muryar Jafar can ƙasa ya furta. "Mami ku miƙo mini ruwan alwala, ba zan iya fitowa ba wallahi gwagwiye mini ƙafa za su yi." Duk yadda Mami ta so Jafar ya buɗe ƙofar fir ya ƙi buɗewa, Lado ya miƙa masa ruwa ta window da sauri Mami ta nufi sashensu kai tsaye ta wuce ɗakin Daddy.

Da sallama Mami ta shiga, turus ta yi ganin Daddy na zaune a kan dadduma yana karatun Alƙur'ani. Ganin Daddy ba shi da niyyar sallame karatun ya sa Mami ta furta. "Daddy gidan nan fa babu lafiya. Domin ganin idona na ga aljanu a daren jiya, yanzu haka Jafar yana ɗakin Lado tun daren jiya ya ƙi fitowa. Ka ga dai yau kwananmu ashirin da biyu a gidan nan ko kunama ba ta taɓa tsoratar da mu ba, amma zuwan yarinyar nan ga shi aljanunta suna neman sabauta mini yaro." Daddy ya kafe Mami da kallo, a daƙile ya furta. "Allah Ya sawaƙe." Ran Mami a ɓace ta ce.

"Iya abin da za ka iya faɗa kenan Daddyn yara? An ya kana ƙaunata ni da 'ya'yana yanzu kuwa?" Sai Mami ta fara zubar da ƙwalla. Daddy bai tanka mata ba ya rufe Kur'anin sannan ya naɗe dadduma ya fice daga ɗakin.

Duk abin da yake faruwa Lado ya zayyana wa Daddy, Daddy ya isa bakin window ɗakin Lado ya leƙa. Ban da gumi babu abin da Jafar yake yi, da ƙyar Daddy ya shawo kan Jafar ya buɗe ƙofar. Lokaci ɗaya Jafar duk ya yi zuru-zuru, Mami ta ƙarasa ta ruƙo hannunsa tana faɗin. "Son amma babu abin da yake damunka ko?" Uwani da ta ƙarasa ta nuna kamar ba ta san abin da yake faruwa ba ta ce.

"Ya Jafar ina ka shiga da asuba na ga ba ka nan." Jafar ya bi Uwani da shanyayyun idanunsa da kallo, Mami ta wurga mata harara sannan ta ja hannunsa suka wuce sashenta. Uwani ta gimtse dariyarta ganin yadda Jafar yake tafe yana ɗimgisa ƙafa, sai ƙara wani shagwaɓe wa Mami yake.

Daddy ne ya koma wurin Lado ya sake tambayarsa tsakaninsa da Allah a kan abin da ya faɗa masa, don shi bai yarda da abin da Mami ta faɗa ba. Gani yake kamar wani sabon shirin suka ɓullo da shi, sai da ya ji ta bakin Lado ya kuma nuna masa shatin bayansa wurin da Uwani ta caccaka masa sandar wurinsa sannan Daddy ya yarda.
Shiru Daddy ya yi yana nazari, a iya zamansu dai a gidan ba su ga wani baƙon abu ba. Sai tunaninsa ya tsaya a kan ko Uwani tana da iska, ya fi aminta da wannan tunanin na shi a kan mutanen jikin Uwani ne suke yunƙurin tashi tun da dama wasu sai an yi aure suke nuna kansu.

Jafar wanka ya yi Mami ta dafa masa tea ya sha sannan ya samu ya kwanta bacci ya yi awon gaba da shi, ita kuwa Uwani tana can zaune Daddy ya leƙa ya kira ta ya ce ta nufi sashen su Mami ta zaune akwai baƙin da zai kira za su yi saukar Alƙur'ani a cikin gidan. A rakaɓe Uwani ta zauna a falon, sai uwar harara da Mami take auna mata don ma Daddy yana gidan amma ta ci burin tun a ranar ta fara hora ta da aikin wahala.

Sai kusan sha biyun rana ragowar 'yan uwan mahaifiyar Uwani da wasu tsirarun 'yan uwan Dada suka sake dawowa ganin gidan Uwani, sai a lokacin ne Uwani ta É—an saki jiki suka dinga hira. Mami ba don ta so ba ta sa Inna mai aiki ta girka musu abinci, bayan sallar la'asar kuma kowa ya kama gabansa.

Daren ranar da ƙyar Daddy ya shawo kan Jafar suka koma sashensu, don ita Uwani fir nunaawa ta yi ba ta gane abin da Jafar da su Mami suke faɗa ba. Dalilin haka ya sa Daddy ya sake tabbatar da ƙila mutanen jikin Uwani ne suka tsora ta su. Sai da suka ci abinci a ɓangaren su Mami sannan suka nufi na su, suna zaune a falo zaman kurame wayar Jafar ta fara ringing. Number Safna ya gani bai san dalili ba haka kawai ya ji gabansa ya faɗi, a hankali ya ɗauki wayar daga can ɓangaren aka furta.

"Haba Baby wai ina ka shiga ɗazu na kira no respond." Jafar ya saki murmushi. "Cutie na gaya miki kwana biyu ba na zama but am very sorry, In shaa Allah haka ba za ta ƙara faruwa ba."

"Beb dama fa Daddy ne na ji yana yunƙurin haɗa ni da wani cousin ɗina, ni kuma na ce masa ina da wanda nake so. So yanzu dai ya ce kawai ka fito..." Tun Safna ba ta gama magana ba Jafar ya miƙe a zabure, "Da gaske kike Cutie?" Jin yadda ya karɓi maganar ne ya sa Safna ta ce. "Da wani abu ne Baby?" Jafar ya ɗan wayance yana sosa ƙeya ya furta. "Am ba komai Dear kawai na yi mamaki ne, na ɗauka Dad ba zai bari a yi maganar aurenmu yanzu ba." Cikin jin daɗi Safna ta ce.

"No ka san Daddy bai da matsala."
Jafar ya ma manta Uwani na wurin shi da Safna suka ci gaba da hirar soyayya, ya tabbatar mata da zai sanar da mahaifinsa duk abin da ake ciki.

Baki sake Uwani ke bin sa da kallo tana mamakin yadda yake sakin murmushi. "Ya Jafar dama kana dariya haka?" Uwani ta tambaya.

"Sai ki hana ni, da waya ce ki zauna ki saka mini ido?" Uwani ta tura baki gaba. Suna nan zaune sai ga kiran Dada ya shigo wayarsa. Sai da ta kusa katsewa sannan ya É—auka yana faÉ—in.
Chapter 20 · 0% Book details