Sashe 58
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ya isa ba na son jin kukan nan!" Jafar ya furta a hankali.
"Amma Baby yanzu me kake son ƙawayena su ɗauke ni, wai me yake faruwa na gagara gane kanka ne?" Safna ta yi maganar cike da damuwa, gyara kwanciyarsa ya yi kansa na sara masa ya furta.
"Babu komai, yanzu me kike so?"
"Zuwanka wurin event!"
"Zan zo amma guda É—aya zan iya zuwa!"
"But please..."
"Na gama magana please akwai abin da zan yi yanzu." Jafar bai tsaya jin ta bakin Safna ba ya katse wayar. Kashe wayar ya yi gabaɗaya ya miƙe yana kaiwa da kawowa, haka kawai ya ji duniyar ta yi masa zafi. Wani tunani ne ya faɗo masa da sauri ya kunna wayarsa ya lalubo lambar Uwani ya kira, ya yi sa'a kuwa tana shiga amma har ta katse ba a ɗauka ba. Sai da ya kira kusan sau goma sannan Uwani ta ɗauka.
Ajiyar zuciya ya sauke a fili sannan ya furta. "Yanzu kin amince Dada ta raba tsakaninmu Hayatee, kin san dai ba zan jure ba. Kin sabar mini da abubuwa kala-kala da ba zan jure rashinsu ba, don Allah kada..." Ƙit ya ji Uwani ta kashe wayar gabaɗaya. Daga can ɓangaren Uwani ta cusa kanta cikin filo ta rushe da matsanancin kuka. Wata irin soyayyar Jafar take ji na ratsa ta har cikin gangar jiki da ruhinta, jin motsin Dada za ta shiga ɗakin ya sa ta yi lamo kamar mai bacci.
Mami tana fita kai tsaye gidan mahaifinta ta nufa, ta kira Ibrahim ta sanar da shi abin da Daddy ya yanke a kanta. Har za ta kira Jafar sai kuma ta ji wata irin kunyarsa ta lulluɓe ta, don ba ta san me za ta ce masa ba.
Kamar yadda Dada ta sanar da Baba Inusa ana yin sallar magriba ya yi sallama a sashenta, Dada ta dubi Uwani ta furta.
"Ga Inusa ya ƙaraso kamar yadda na faɗa miki zai ɗauke mu yanzu za mu kai ki wurin Maryama, wallahi-wallahi Uwani matuƙar na ji labarin kin sanarwa wani wurin da kike sai ranki ya yi mummunan ɓaci. Ɗazu mun gama magana da Maryama za ki koma wurinta da zama har zuwa nan da Allah Ya sauke ki lafiya, daga ni, mahaifiyarki, Inusa sai ke mu kaɗai muka san da tafiyarki. Kuma duk cikinsu babu wanda ban ja kunnensa na gargaɗe shi ba. Duk bayan sati ɗaya ko biyu zan dinga zuwa ganinki In shaa Allah." A sanyaye Uwani ta gyaɗa kai, ta ja akwatinta ta fito da ita a lokacin duhu har ya yi. Babu wanda ya lura da fitar su Dada don haka Baba Yunusa ya ɗauke su zuwa garin da mahaifiyar Uwani ke aure.
Tarba ta mutumci aka yi musu lokacin da za su tafi Dada ta ɗauko kuɗi masu kauri ta ba wa Maryama, Aramma da ita Uwanin kanta. Baba Yunusa ya sauke musu kayan abincin da Dada ta saka shi saya, a fili Aramma ya nuna rashin jin daɗin haka. Dada ta ce masa babu komai don ba daɗi a ɗora wa mutum nauyi, musamman da ake fama da yanayin rayuwa. Dada ta ja kunen Aramma sosai, don ta san matuƙar Jafar ya farga Uwani ba ta nan tabbas zai zo nemanta nan gidan. Aramma har ƙofar gida ya raka su yana sake jaddada wa Dada riƙe alƙwarin da ya yi mata.
Dada ta koma gida da kamar minti talatin sai ga Jafar ya je gidan afujajan, tana daga zaune ta hango shi a tsaye. Ta ɗan ƙanƙance ido ta ce. "Waye haka a tsaye zai shigo mini ɗaki a tsakar daren nan?" Jafar bai amsa ba ya shiga ɗakin ya zauna a kusa da ita ya ce.
"Dada ina matata?"
Sheƙeƙe Dada ta kalle shi ta ce, "Yanzu kam Uwani ai ta tashi daga matarka, miƙo mini takardarta." Dada ta yi maganar tana miƙa masa hannu.
"Wallahi ba ki isa ki raba ni da matata ba Dada, haka kawai ina son matata tana sona ki ce za ki raba mu. Wallahi ki guji fushin Ubangiji..." Tun Jafar bai gama magana ba Dada ta fashe da kuka, ta janyo wayarta ta yi latse-latsenta ta kira. Ana É—aga wa ta furta.
"Mamman wallahi tun wuri ka ce Jafaru ya fita daga idona." Daga can ɓangaren aka ce.
"Dada Abuwa ce ba lambar Daddyn yara kika kira ba sai dai a ba shi wayar." Cikin sauri Dada ta ce. "Maza ba shi kada Jafaru ya rufe ni da duka."
Daddy yana karɓar wayar ya ce. "Barka da dare Dada."
"Wallahi Mamman idan ba ka yi mini iyaka da Jafaru ba Hukuma za ta raba mu, saboda Allah ya zo ya har tsakar É—akina ya rufe ni da faÉ—a. Wai ina matarsa? Yo to ta ina Uwani take a matsayin matarsa? Ni ka gaya masa ma Uwani ba ta garin nan gabaÉ—aya, kuma gobe-gobe zan sa Isuhu ya kai ni kotu Jafaru ya ba ta takardarta."
Hankali a tashe Daddy ya ce. "Dada ina kuma Uwanin ta tafi?"
"Wa muke yi wa sallah Mamma?" Da sauri ya ce.
"Allah mana Dada.
"To wallahi tallahi Uwani ba ta gidan nan, kai ita da sake dawowa ma sai Allah ya sauke ta lafiya. Tsoron matarka nake haka kawai watarana ta biyo dare ta shaƙe ta har lahira." Jafar bai gama jin bayanin Dada ba ya faɗa ɗakinta, wayam ya gani babu Uwani babu alamarta ya shiga bi sashe-sashe na gidan yana tambaya, duk inda ya je sai dai ace masa ba ta nan yawanci ma a bakinsa suke jin Uwani ba ta gidan. Jafar ya dafe kansa a haukace yana jin tamkar zuciyarsa za ta faɗo daga ƙirjinsa.
Littafin kuÉ—i ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 idan littafi ya kammala 800 neðŸ«
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
Hankali a tashe Jafar ya koma É—akin Dada don sai a wannan lokacin ya tabbatar da abin da ta faÉ—a game da rashin Uwani a gidan, yana shirin yi mata magana ya ji ta ce.
"A toh wallahi matuƙar Jafaru zai dinga zuwa yana yi mini maganar Uwani na dai faɗa maka sharaɗina, a can uwarsa ta hana yarinya sukuni. Yanzu kuma ta bar gidan ma zai hana ta yin laulayi cikin kwanciyar hankali." Daddy ban da haƙuri babu abin da yake ba wa Dada, sai da ta yi faɗa mai isarta sannan ta miƙa wa Jafar waya. Saboda tsabar takaici ko kallon Dada bai yi ba, ganin ba shi da niyyar karɓar wayar ya sa Dada ta ce.
"Kasan dai Saratu ta fika ƙarfin jini Mamman, to ga shi dai ƙiri-ƙiri na yi wa Jafaru magana ya mayar da ni garu, ni dai ka dubi Allah da Annabi Mamman ka ce Jafaru ya fice mini daga ɗaki. Kwarankwatsa dubu ko bai shaƙe ni ba yanzu na san kaɗan ya rage masa." Daddy ne ya katse wayar Dada nan take ya kira ta Jafar, kamar ba zai ɗauka ba ya haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ya ɗauka.
"Daddy..."
"Ka zo gida yanzu ina son ganinka." Iya abin da Daddy ya faɗa kenan ya katse wayarsa. A ƙufule Jafar ya dubi Dada ya ce. "Wallahi Dada idan ba ki kai ni wurin hukuma ba ni zan kai ki, kuma duk abin da ya faru da matata ke ce."
"Sai ka fara kai ƙarar Saratu tukunna, kai wallahi bari Inusa ko Isuhu su zo Saratu ma ba ta daki Uwani a banza ba, sai na kai ƙararta idan ya so Jafaru ka ɗaure ni har igiya ta yi saura." Jafar bai tanka mata ba ya fita cikin ɓacin rai. A hanya ya ci karo da Na Madina har ya kusa bangaje shi, da mamaki ya bi Jafar da kallo sannan ya shige wurin Dada.
Wani irn mahaukacin gudu Jafar yake yi cikin ɓacin rai kamar zai tashi sama, a haka ya ƙarasa gida lokacin Daddy da iyalansa gabaɗaya suna babban falo a zaune. Kowa ka dubi fuskarsa ɗauke yake da damuwa duk da har lokacin Daddy bai sanar da su hukuncin da ya yanke a kan Mami ba. Jafar na shiga ya nemi wuri ya zauna, Daddy ya dube su ɗaya bayan ɗaya sannan ya ce.
"Kowannenku ya san abin da ya faru dangane da mahaifiyarku tsakaninta da Uwani, a don haka ne kuma Dada ta yanke hukuncin sai Jafar ya sawwaƙe mata kuma har a yanzu Dada tana kan bakarta don ba ta huce ba." Da sauri Auta ta ɗago tana kallonsa idanunta suka ciko da ƙwalla don ko kaɗan ba ta ƙaunar rabuwar Uwani da yayanta. A nan ne kuma yake sanar da su hukuncin da shi ma ya yanke a kan Mami. Shiru falon ya ɗauka duka zuciyoyinsu na suya, Aunty ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin.
"Amma Daddyn yara wannan hukuncin ya yi tsauri da yawa a wurin Aunty Saratu, saboda ka ga..."
"Na riga da na yanke hukunci, ba na buƙatar wata doguwar magana." Shiru gabaɗaya suka yi, cikin jin haushi Madina ta dubi Jafar ta ce.
"To Ya Jafar ba shi kenan ba, tun da dama ba ka taɓa sanar da Aunty Safna kana da aure ba ai ta zo maka gidan sau..." Kallon da Jafar ya wurga mata ne ya sa ta ja baki ta tsuke. Da mamaki Daddy yake kallon Jafar cikin kallon tuhuma.
"Kana nufin ba ka taɓa sanar mata cewar kana da aure ba? Hankalinka ɗaya kuwa Jafar? A haka za ka iya riƙe mata biyu?" Jafar da abin duniya ya gama haɗe masa, kamar zai yi kuka ya ce.