← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 71

Sashe 30

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani tunani ne ya sake faɗo mata don haka ta miƙe ta fice daga cikin hall ɗin, ta watsar da shirin rezar da ta ci buri yi don ta lura wannan da za ta aiwatar sai ya fi tarwatsa lissafin Mami da Shukra. Waige ta shiga yi hagu da dama sannan ta hango wata 'yar kwana a bayan hall ɗin. Tana cikin tafiya ta hangi wani matashi zaune a jikin bishiya, da alama 'yan zuƙe-zuƙensa yake yi. Uwani ta lura sarai da yadda yake kafe ta da kallo yana murmushi tun kafin ta ƙarasa, tana zuwa daidai wurinsa ta yi masa sallama cikin murmushi ta ce.

"Yayana don Allah wani taimako nake nema." Abin ka da me jira da sauri saurayin ya miƙe tsaye yana kaɗe jikinsa ya furta.
"Haba 'yan mata faÉ—i kowanne irin taimako ne an gama shi." Uwani ta É—an kawar da kai a fakaice, jin tsamin kayan mayen da yake sha ya bugo ta sannan ta ce.
"Dama ƙannena ne suke fama da matsanancin tari, to shi ne muke buƙatar jangwalagwada guda biyu za a dafa musu an ce shi ne ƙat wurin maganin tari." Uwani ta yi maganar tana zaro kuɗi daga aljihunta ta ce.
"Ga wannan ba yawa don Allah sai a rage..."

"Haba ƙanwata, ai aikin lada za mu yi biyar ba zan karɓa daga wurinki ba." Uwani ta yi masa godiya, sannan ya ce mata ta tsaya a nan zai samo mata.
Ba a ɗauki lokaci ba sai ga shi ya dawo hannunsa ɗauke da wasu sharɓa-sharɓan ƙadangaru, leda ya zaro a aljinu zai saka mata da sauri Uwani ta ce. "Don Allah idan babu damuwa ka saka mini kowanne daban-daban a leda, don mamanmu ta ce za ta ba wa aminiyarta ɗaya ita ma yaranta tari suke." Matashin ya yi murmushi ya ce, "Ai sai yadda kika ce ranki shi daɗe."

Sai da ya saka wa Uwani a cikin leda daban-daban ya miƙa mata, ta ɗauko wani kyallen ragowar atamfarta ta buɗe ta saka a ciki, sannan ta zura a cikin wata ledar suka fara tafiya, suna tafe matashin sai zuba mata hira yake har suka ɗan gota hall ɗin bikin. Uwani ta yi masa dabara ya koma sannan ta koma ta shige cikin hall ɗin.

A lokacin da ta je Mami na ta gaisawa da mutane, Auta ta hango zaune a wata kujera da sauri ta zura ƙadangarun cikin aljihun rigarta.

"Masu yin rawa an gaji ne?" Uwani ta furta wa Auta tana jan kujerar kusa da ita. Sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Ki bari Uwani Mc ne ya kwafsa mana muna cikin rawa ya kashe, wai ba ya buƙatar taron ƙwailaye ki ji iskanci." Uwani ta saka dariya tana shirin magana Mami ta ƙarasa wurin Auta ta miƙa mata jakarta tana faɗin.

"Auta riƙe mini jakar nan kafin su Shukra su shigo kin san fa ni dama ba gwanar riƙe jaka ba ce..." Kalamanta suka katse sakamakom ganin Uwani a gefen Auta.
"Uban me kike yi a nan? Ɓarauniya nan ma zuwa kika yi kwashi kuɗin jakunkunan mutane? Wallahi ko cokali na ji ana cigiya sai kin yaba wa aya zaƙinta." Mami ta ƙarasa maganar tana wurga mata harara ta bar wurin, wannan ce rana ta farko da Uwani ta ji ta tsangwami kanta ta kuma muzanta. Saboda tsirarun mutanen wurin har sun fara kallonta, idonta ya ciko da ƙwalla Auta ta dafa ta ta ce. "Don Allah kada ki ɓata kwalliyarki Uwani, wai ma Ya Jafar ya gan ki kuwa." Murmushi ne ya suɓuce wa Uwani ta girgiza kai, don ita kanta make up ɗinta ba ƙaramin kyau ya yi mata ba.

Auta ta yi ta zolayar Uwani har sai da ta ga ta saki jikinta sannan suka ji an yi shelar za a shigo da amarya da ango. Da sauri Auta ta damƙa wa Uwani Jakar Mami ta nufi bakin ƙofa da yake sune masu anko, sai da suka jajjeru sannan aka saki waƙar Nura M Inuwa ta 'Lokacinki ne ya yi amarya 'yar amana...'

Ganin hankulan mutanen wurin ya yi kan Shukra da Salim, wasu na ɗaukan hotuna yayin da wasu ke yin Video ya sa Uwani ta sauke jakar Mami ƙasan table ta ware ƙyallen da ta saka ƙadangaren ta buɗe guda ɗaya, sai da ta zuge jakar ta hango damin kuɗin liƙin da Mami ta tanada. Murmushi ta saki mai sauti sannan ta ɗora jangwalagwadan akan canjin kuɗin, ta wurgar da ledar a gefe ya rage saura ƙadangare ɗaya. Da sauri ta dawo da jakar ta ajiye, ta ci gaba da kalle-kallenta. Babu laifi Shukra ta yi kyau sosai, da yake ta saka atamfa ja da wani yadi mai kalar ruwan toka, shi kuma Salim ya saka dakakken yadi ruwan toka an yi masa aiki da jan zare a babbar rigar. Mami na daga gefe sai sakin murmushi take, a haka har amarya da ango suka wuce kan kujerar da aka tanadar musu. Da zamansu babu jimawa Auta ta je wurin Uwani ta karɓi jakar Mami ta kai mata, daga haka dangin su Salim suka shigo ɗauke da turarukan wuta dana ruwa ana fesawa. Dada ita ma sai a lokacin ta shigo da yake ita Jafar ne ya kawo, ita da wata Kakar Salima suka nufi wurin su Shukra aka ba su turare suka shiga fesa musu.

Take wurin ya kacame kowa burinsa ya ga fuskar amarya da ke ƙumshe cikin lulluɓi, Uwani ta zagaya ta bayan kujerar da suke zaune duk yawan mutane ta kutsa daidai kunnen Shukra ta sauya murya ta raɗa mata a kunne.

"Muna taya ki murnar amarcewa a matsayinki na 'yar matata. Ki sanar da masoyiyata Saratu zan bata gudunmawar aurenki, kuma kema zan damƙa wa angonki ta ki gudunmawar."

Da yake rurumar mutane ta yi yawa babu wanda ya lura da wata Uwani, Uwani na gama magana ta matsa daga wurin tana dariyar ƙeta. Shukra da ke lulluɓe ana buɗe mata fuska har ta haɗa uban gumi sharkaf, gabanta ya shiga faɗuwa tana ɗan waige. A haka aka yi ta hotuna ana fesa musu turare ita da Salim, daga nan kuma MC ya ce su fito cikin fili domin su taka rawa. Ganin sauyin da Salim ya gani tattare da Shukra ya sa ya ɗan yi mata raɗa a kunne.

"Dear lafiya kuwa? Na ga kin sauya lokaci ɗaya, saɓanin yadda muka shigo mota." Shukra ta tattaro murmushin yaƙe ta ce. "Wallahi turaren nan ne ya yi mini yawa shi ya sa kaina ya ɗan fara ciwo." Wannan maganar da suke yi ba ƙaramin birge mutane suka yi ba, nan Mc ya ci gaba da wasa su Uwani na daga gefe tana sakin murmushin mugunta.

Shigar su Shukra cikin fili ya sa dangin Salim da na Mami suka shiga suka fara yi musu ruwan liƙi, ganin yanayin da Shukra ke ciki ya sa Mami ta zagaya ta yi mata raɗa a kunne.
"Haba Shukra ki saki fuskarki mana, kina ga fa duk wanda ya zo wurin nan domin ku ya zo fa." Da sauri Shukra ta zayyana wa Mami duk abin da ta ji a kunneta, tun ba ta gama magana ba Mami ta yi sharkaf da gumi, amma sai ta nuna wa Shukra su basar don su rabu da baƙinsu lafiya, saboda kada a lura da yanayinsu.

Ta cikin rurumar rawar da ake yi ne Uwani ta saɗaɗa ta zurawa Salim ƙadangaren a cikin aljihu, ta koma ta gefen Shukra ta raɗa mata cewar.
"Mun saka wa angonki gudumuwarki, ki yi gaggawar karɓa yanzu idan ba haka ba mahaifiyarki za mu ɗauke, kuma har abada ba za ku sake ganinta ba." Uwani na gama maganar ta yi sauri ta sulale, hankali tashe Shukra ta fara waige, Mami ganin ƙawayenta da 'yan uwa na ta liƙi ya sa ta zage jaka tana ɗan tattakawa cikin shauƙin rawar da kiɗan da ya ɗebe ta. Ta zura hannu da sauri don ta ɗebo kuɗi ta watsa, a wannan lokacin ne kuma Shukra ta ce wa Salim ya zura hannu a aljihunsa. Bai tambaye ta dalili ba, sai ma ya yi tsammanin ko Shukra na nufin ya yi mata liƙi ne, yana saka hannu a aljihu ya ji abu da laushi har da alamun ƙafafuwa. Yana fito da shi idanun mutane suka sauka a kan nararkeken jagwalagwada, ita ma Mami a wannan lokacin ta fisgo ƙadangaren cikin jakarta da hannunta, da yake da ƙarfi ta ɗauko da niyyar yin liƙi sai kawai gani aka yi ƙadangare ya yi sama.

Dada da Kakar Salim wato Inno a guje suka fita daga cikin filin, mutane suka fara guje-guje wasu na faɗa wa ƙasan table. Yayin da irin su Mami suna bazama a guje suna neman maɓoya.
Ƙawayen Shukra da ƙannen ango tuni suka bazama, sai ɗankwalaye da mayafai ne suka dinga tashi sama.
Uwani da zamanta a ƙarƙashin table ɗin da Dada ta ɓuya kenan, ta dubi Dada da hawaye ya gama wanke mata fuska. Ta tsince ta tana faɗin. "Ni kam Saro ta jangwalo mana masifa, yanzu Allah wannan ƙadangaren ashe bai bar ta ba?" Uwani ta haɗe fuska ta ce.
"Kin ci sa a da ba ke ya aura ba?"

"Uwarki Maryama kika faÉ—a wa ba ni ba, almura mai mugun hali wallahi Uwani kin yi asarar halin 'yan É—auke-É—auke." Shiru Uwani ta yi wa Dada tana murmushi.

Ganin 'yan mata na fita daga hall ɗin a guje ya sa securities ɗin cikin halla ɗin suka shiga suna tambayar abin da ya faru, wasu daga cikin masu ganin ƙwaƙwaf ɗin har sun fara yi wa ƙadangarun vedio suna watsawa a social media. Securites ɗin ne suka kwashe su suka fita da su sannan hall ɗin ya fara dawowa daidai.
Chapter 30 · 0% Book details