← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 71

Sashe 6

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To kada ku kai shi dama É—an autan GoÉ—iya kwaÉ—ayin romon jariri yake ji sai na dafe masa shi." Uwani ta faÉ—a cikin wata irin murya, don ita kanta dagewa take da tuni dariya ta kwace mata.

"Wallahi za mu kai shi, Allah Ya kai mu gobe." GabaÉ—aya suka amsa.

"Kuma ya zama wajibi a gare ka, kai Isuhu ka saka ƙarfi ka danne Jafar domin a shayar da mai sunan malam idan ba haka ba komai zai iya biyo baya. Kuma sharaɗin da zan kafa muku na ƙarshe ko da wasa kuka faɗi abin da ya faru tsakanina da ku, sai na sa wuƙar aljanin mahauta ya yaɗe fatar jikinku sannan na ɗauke ku zuwa duniyarmu a azabtar da ku kamar yadda kuka azabtar da ni." Uwani na daga tsaye ta fara jiyo shasshekar kukan Baba Isuhu. Sai da ta lallaɓa ta ɗauke tukunyar naman da aka yi farfe su ta ajiye a soro sannan ta ce.
"Tukunyar namana da kuka dafa ku same ta a wurin garkena, kada wanda ya fito har sai an kira sallar isha'i domin tuni an zauna zaman fadar aljanu da ku. Kuma idan kuka bari namana da kuka dafa ya kwana a garkena cikin dare zan gayyato tawagar jinsinmu su É—auke mini ku." Uwani na gama maganar ta fara kukan tumaki tana wani irin dire-dire sannan ta É—auki tukuyar ta tafi a hankali, kai tsaye ta wuce garken awakinta.

Da yake duhu ya yi awakin Uwani duka sun kwanta, a hankali ta isa turken uwar garke ta ajiye tukunyar. Ta janyo igiyar uwar garke ta saƙale a jikin ƙafar tukunyar, zuciyarta fes ta wuce sashen Dada don ta yi sallar magriba tana tafe tana dariya kamar sabuwar kamu. Har alla-alla take gari ya waye ta ga irin diramar da za a tashi da ita.

A lokacin da ta shiga ɗakin Dada Jafar na zaune ta kofin shayi a gefensa , ga laptop a gabansa yana dannawa, dawowarsa daga masallaci kenan. Uwani na ƙare masa kallo ta tuntsire da wata mahaukaciyar dariya, domin yanayin zaman da ta ga ya yi ne har ta hango yadda Baba Isuhu zai danne shi a shayar da mai sunan malam.

Ɗagowa ya yi ya kalle ta sai kuma ya ci gaba da danna laptop ɗinsa, Uwani ta sake kallonsa ta ga yadda yake jin magani sai kawai ta tsugunna a wurin tana sheƙa uwar dariya.

"Uban me kike yi wa dariya?" Jafar ya furta a daƙile. Tamkar wacce ya sake ingizawa, sai Uwani ta sake fashewa da dariya har da hawaye da ta tuna duk irin haɗe fuskar da yake yi wai shi za a danne a shayar da mai sunan malam.

"Ba tambayarki nake yi ba?" Jafar ya buga mata tsawa.

"Dama wani wasa ne muka fara bugawa ni da ƙawata Lantana shi ne na shirya mata yadda zan cinye ta gobe." Uwani ta yi maganar tana ɗan murguɗa baki.
"Ba na son shashanci idan wannan iskanci za ki yi ki fice mini ba na son hayaniya." Uwani ba ta kula shi ba ta gimtse dariyarta ta shige uwar É—akin Dada.

Ku kawo wa Jafar ɗauki zai shayar da mai sunan malam🤭🏃🏼‍♀️😂

07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

SHAFI NA HUÆŠU

Tun da Uwani ta fito daga gidan baba Isuhu daga shi har Lami babu wanda ya kuma motsin kirki, baba Isuhu ya sharɓe hawaye ya dubi Lami cikin kallon tsana da jin haushi ya ce.

"Tsakanina da ke Allah Ya isa Lami, kin cuce ni kin cuci rayuwata. Ni ban san ƙaddarar da ta sa na auro ki ba, duk wannan ƙaton bakin na ki ko ina ya je da ban gan shi ba sai yanzu?" Lami ta wurga masa harara ta ce.
"Mun dai cuci juna malam ka gyara maganarka. Ni kaina ban azal da kuma rabo me zan yi da kai? Ka san dai duk a samarina kai ne faƙiri matsiyaci."

"Wallahi aurena da ke bai ƙare ni da komai ba sai masifa, ina zaman zamana kin jefa ni a jafa'i muguwa mai ƙashin tsiya..."
"Dakata malam, kada ka raina mini hankali. An gaya maka ban san dama can kana 'yan sace-sacenka ba? Ko ka manta kajin Yaya Haladu da muka taɓa soyewa?" Shiru baba Isuhu ya yi yana nazari, shi kam ya ci alwashin daga uwar garke har abada ba zai ƙara taɓa kayan wani ba. Dama tun da yake 'yan ɗauke-daukensa ba a taɓa kama shi ba, don haka zai ajiye sata salin-alin ba tare da ta tona masa asiri ba.

Suna nan zaune suka ji an rafka kiran sallar Isha'i, babu jimawa suka ji takun Goggo Sala tana tafe da baya-baya, taku É—aya-biyu idan ta yi sai ta ci karo da kwanuka sannan ta furta. "Nasara dai a kanku Isuhu da Lami."

Da hannu Lami ta yafito baba Isuhu ta cikin labule take nuna masa ita, cikin gasgata maganar da Uwani ta gaya musu suka saki baki suna kallonta, a ɓangare ɗaya kuma tsoron Goggo Sala ya kama su. Tana shiga ɗakin da suke kwana da Lami ta banko ƙofa, can ƙuryar bango ta zauna sai kawai ta rushe da wani irin kuka mai cin zuciya.
"Kaico kwaÉ—ayina bai amfane ni da komai ba, Allah ka fitar da ni daga wannan gidan annobar. Wallahi nan gaba idan duniya Lami za ta haifa har abada ni da gidanta."

Ganin ta shige ɗaki ya sa baba Isuhu ya fita a hankali domin cika umarnin uwar garke, kai tsaye garken Uwani ya nufa yana haskawa kuwa ya yi ido biyu da tukunyar farfesun naman. Nan take ƙirjinsa ya buga, jikinsa ya fara karkarwa sai da ya yi ta maza ya ɗauko tukunyar ya nufi sashensa.

WASHEGARI

Baba Isuhu tun da ya yi sallar asuba ya gagara runtsawa saboda fargabar goyon da Goggo Sala za ta yi masa, yana zaune a gefen gado ya kallo Lami da ke kwance ita da mai sunan malam. Motsi ya ji a tsakar gida yana leƙawa ya hangi Goggo Sala tana kaiwa da kawowa, abin duniya ya dame ta saboda gari ya fara haske amma har kawo lokacin babu Isuhu babu motsinsa. Cikin sanɗa ta nufo ɗakin da suke ciki baba Isuhu ya leƙo ta windo ya ce.

"Munafukar Allah ta'ala ina ankare da ke, wato fakona kike za ki hallaka ni ko?" Goggo Sala ta washe baki tana basarwa ta ce.

"Isuhu barka da safiya." Baba Isuhu da ya tuna gargaɗin da aka masa, aka ce kar ya yi mata kora da hali shi ma sai ya yaƙe baki ya amsa. Amma a zuciyarsa ji yake tamkar ya fashe da kuka. Mai sunan malam ne ya motsa Lami ta yi fitgigit ta tashi zaune.

"Maza tashi mu je ki kai shi wurin Jafaru." Ba musu Lami ta tashi ta saka hijabinta, baba Isuhu ya manta Goggo Sala da ke waje tana fakonsa ya sa hannu ya buÉ—e sakata suka fito. Har zai yi gaba ya tuna bai É—ebo rigunan maman Lami da aka ce ya kai wa Dada ba, dama tun a daren ya sa Lami ta É—ebo masa guda uku daga cikin na ta. Komawa ya yi ya É—ebo ya zuba a aljihu sannan ya fito. Yana fitowa Goggo Sala ta yi wata uwar sufa za ta cafko baba Isuhu, a firgice ya zuba a guje yana faÉ—in.

"Wayyo Lami ki zo za ta cafke ni, wallahi tsaf za ta sa a tsotse romon kaina."
Goggo Sala na ganin rana ta fara fitowa ga shi ba ta cika umarnin uwar garke ba, ya sa ta rufa wa baba Isuhu baya yana gudu tana bin sa. Da yake ya gama tsorata da ita har gani yake kamanin Goggo Sala kamar har rikiɗe masa suke yi, Goggo Sala irin dogayen matan nan ne, shi kuma baba Isuhu ba shi da tsayi kuma ba shi da jiki. Don haka Goggo Sala ta kusa kama shi amma Allah ya taimake shi ya fice daga gidan, Lami ta rufa masa baya da sauri ya tura ƙofar ya datse ta. Wata gwaruwar ajiyar zuciya ya sauke yana ayyana shi kenan da tuni an bayar da jininsa.

Ɓangaren Dada a buɗe yake don haka ba su sha wata wahala ba suka nufi ɗakin da Jafar yake ciki, Lami ce ta fara ƙwanƙwasawa sun ɗan jima sannan Jafar ya buɗe da alama bacci yake yi. Daga shi sai singlet da gajeren wando ya buɗe ƙofar yana murza idanu. Da mamaki yake bin su Baba Isuhu da kallo ya furta.
"Ina kwana baba."
Baba Isuhu ya washe baki.

"Jafaru an tashi lafiya?"
Jafar ya amsa sai baba Isuhu ya ce. "Wurinka muka zo Jafaru amma ko za mu ƙarasa ɗakin Dada?"
Zuciyar Jafar fes ya ce.
"Ok to bari na saka kaya ga ni nan zuwa." Lami da baba Isuhu suka wuce É—akin Dada a lokacin tana zaune tana jan carbi.

Tana ganinsu ta shafa addu'ar, sai da ta cire hijabin ta ajiye carbin ta ce. "Isuhu lafiya na gan ku da farar safiyar nan?" Cikin haɗin baki suka gaishe ta. Baba Isuhu ya ciro rigunan maman hannunsa ya miƙa wa Dada ya ce. "Dada ga wannan a saka."

Dada ta karɓa tana yamutsa fuska.
"Kai kuwa Isuhu kamar wanda ya kwana da Uwani a rai, tun da farar safiya ka kawo mata wata rigar mama. Wannan dai rigunan ai na manyan mata ne, ina Uwani ina wannan lalacewar." Baba Isuhu ya É—an sosa kai ya ce, "Ai dama ba na Uwani ba ne, ke na kawowa Dada..."

Tun bai ƙarasa magana ba Dada ta katse shi, "Ni fa Isuhu? Ni kuwa me zan yi da rigar mama tsofai-tsafai? Amma dai ka ci mutumcina Isuhu, wai ko dai ka fara 'yan zuƙe-zuƙe ban sani ba?" Idanun baba Isuhu suka ciko da ƙwalla sai da ya share hawaye ya ce.
"Don girman Allah Dada ki É—iba ki shiga É—aki ki saka."
Chapter 6 · 0% Book details