← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 71

Sashe 49

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar yau ta kasance asabar ya sa Jafar ya ce Uwani ta shirya za su fita, kuma a wannn ranar saura kwana É—aya ya koma Lagos, tun da ta can za su wuce shi da abokan aikinsa. Uwani baki har kunne don a cikin ziyarar da su kai ya ce mata har da gidan mahaifiyarta, tare da Auta suka tafi duk da a farko Mami ta so hanawa amma Daddy ya ce su tafi tare.

Can dangin Mami suka fara zuwa sun ɗan zazzaga gidanjen 'yan uwanta, kuma babu yabo babu fallasa suka tarbi Uwani. Daga nan Jafar ya wuce da Uwani can garin da mahaifiyarta take aure, lokacin da suka je Aramma ba ya nan. Amma yanayin yadda Uwani ta samu mahaifiyarta da kishiyarta Indo ba ƙaramin burge ta ya yi ba. Gidansu tsaf su da yaransu fes ba kamar da ba, da kowa ya gan su yana san suna cikin wahala. Haka a ɓangaren cima duk da Innarta ba ta san da zuwan su ba samu suka yi sun yi tuwon shinkafa miyar taushe har da nama a ciki, saɓanin a baya da ta ji Indo na ƙorafin kullin tuwon dawa suke ci sai dai Aramma a tuƙa masa tuwon shinkafa, ko idan ya je cikin gari ya taho da semovita a tuƙa masa.

Marayama ta ji daɗin ziyarar da su Uwani suka kawo mata, saboda kara dama tun da aka yi auren Uwani sau uku ta taɓa zuwa wurinta. Sai dai zuwan farko da na biyu da ta yi sam ba ta ji daɗi ba ganin irin tarbar wulaƙancin da Mami ta yi mata, amma zuwan Aunty gidan ya sa wata rana da ta taɓa zuwa ta karɓe ta hannu bibbiyu. Sun sha hira sosai sai yamma liƙis sannan Jafar ya zo tafiya da su. Nasiha sosai Maryama ta yi wa Uwani don ta ji daɗin ganin yadda Uwani ta sake nutsuwa a kan da, Maryama godiya ta yi wa Jafar sosai lokacin da ta rako su. Ya ɗauko wata ƙatuwar leda a mota ya miƙa mata da kuɗi naira dubu goma, da farko Maryama cewa ta yi ba za ta karɓa ba sai da ƙyar ta karɓa Jafar na yi mata magiya. Za su shiga mota kenan Aramma ya ƙarasa ƙofar gidan yana washe baki ya ce, "Yau manyan baƙi ne a gidan namu?" Gabaɗaya suka russuna har ƙasa suka gaishe shi, Aramma ya zaro ɗari biyar-biyar ya miƙa wa Uwani da Auta. Jafar sai harara yake aika musu Uwani ta maze ta karɓa, ganin haka ya sa ita ma Auta ta karɓa.

Lokacin da suka shiga mota faɗa Jafar ya shiga yi musu, a cikin su babu wacce ta tanka masa har suka ƙarasa. Gabaɗaya sashen 'yan uwan mahaifinsa sai da ya shiga ya yi musu sallama sannan ya koma ɓangaren Dada suka dasa hira. Ba su suka baro cikin Kura ba sai bayan sallar Magriba, lokacin da za su tafi Dada sai zubar da ƙwalla take tana jimamin tafiyar Jafar ƙasar Sudan.

A daren ranar Jafar shi da Uwani suka haɗa kayan da zai tafi da su don gari na wayewa da sasssafe zai wuce, Jafar ya lura da sanyin jikin Uwani wani lokacin har ƙwalla take gogewa a fakaice. Washegari da sassafe Jafar ya shirya ya fito, su Mami duk suka fito rakiyarsa bakin gate. Mami ma zuciyarta duk babu daɗi, Daddy ne yake ƙarfafa mata gwiwa. Addu'a gabaɗaya suka yi masa, Uwani ta jingina da mota tana zubar da ƙwalla. Yana son ya yi sallama da Uwani don ya sake rarrashinta amma nauyin su Daddy ya hana shi, a fakaice yake kallonta fuskarta ta kumbura suntum sai goge ƙwalla take. Daddy ya dubi Jafar kamar ya san abin da yake ransa ya ce.

"Ya kamata kafin ka tafi ka lallashi matarka, kasan har yanzu da ragowar yarinta a kanta." Daɗi Jafar ya ji, don haka ya kama hannun Uwani suka shiga cikin sashensu, suna shiga na su gate ɗin Uwani ta faɗa jikinsa tana fashewa da matsanancin kuka. Riƙe ta ya yi tsam kamar wani zai ƙwace masa ita. Bubbuga bayanta ya fara yi yana jin kukanta har cikin jikinsa, sai da ya ji ta ɗan tsagaita sannan ya ɗago da fuskarta ya furta.

"Ɗigar hawayenki na zare mini ƙwarin gwiwar da je tattare da ni, kina son na tafi da rauni har na gagara gudanar da abin da zan je yi." Uwani ta girgiza kai tana hawaye. Jafar ya sa hannu ya lakace mata hawayen da ya gangaro sannan ya ce. "A yanzu addu'arki nake buƙata domin za ta yi tasiri a gare ni." Ya ɗauki hannun Uwani ya ɗora a saitin ƙirjinsa sannan ya ci gaba da cewa.

"Da kin san tarin abubuwan da ke ƙunshe cikin zuciyata da kin jinjinawa gwarzo kuma jarumin mijinki, ki sa a ranki a kodayaushe ina tare da ke. Zan yi kewar bakin tsiwarki, zan yi kewar rigima da rashin jinki." Uwani ta saki murmushi tana jin wani shauƙi a ranta, cikin shagwaɓa ta ce.

"Ni kuma zan yi kewar cin zali da muguntarka." Lokaci É—aya suka saka dariya, Jafar ya janyo Uwani ya yi mata raÉ—a a kunne da faÉ—in.

"Na jima ina dakon kalmar da muhallin da ya dace na furtata, zuciyata, ruhina da gangar jikina duka na sadaukar gare ki. Idan har ban bayyana miki mikin da ke cin zuciyata ba, ban san yadda zai ƙara girmama a cikin jikina ba. A duk hawa da saukar bugun numfashina, ina yin sa tare da so da ƙaunarki ne. Ina son ki! Ina ƙaunarki soyayyar da harshena ba zai iya fasalta irinta ba."

Kusan mutuwar tsaye Uwani ta yi tana jin wani abu yarrr na zagaye ilahirin jikinta, tun daga tafin ƙafarta har tsakiyar kanta. Lokaci ɗaya wata irin kunyarsa ta kama ta, ta sunkuyar da kanta ƙasa tana murza yatsun hannunta tana murmushi. Ɗago kanta ya yi ba ta yi tsammani ba ta ji ya haɗe bakinsu wuri ɗaya, duk yadda ta kai ga jin nauyinsa sai ta samu kanta da mayar masa da martani cikin sanyin jiki. Ya ɗago cikin wani irin yanayi ya sumbaci goshinta jin Daddy ya fara yi masa horn, ya dubi Uwani cikin wani irin shauƙin so ya ce.
"Ki kular mini da kanki, za mu yi waya idan na sauka." Jafar ya sake sakar mata kiss a goshi sannan ya riƙo hannunta suka fara takawa cikin sassarfa.

Ilahirin mutanen da ke wurin bin Uwani da kallo suka yi ganin yadda ta fito tana murmushi, sallama ya sake yi wa su Mami ta amsa masa a gwasale don ba ƙaramin haushin Jafar take ji a kan kulawar da ta ga yana ba wa Uwani ba. A sanyaye Uwani ta bi motar Daddy da kallo har ta fice daga gidan, Auta ta zagaya ta bayan Uwani cikin zolaya ta ce. "A toh ƙaryar a yi mini iskanci ta ƙare tun da yanzu dai kusan ɗaya muke da mutum." Uwani ta wurga mata harara ta ce.
"Gara da kika ce kusan É—aya amma dai ba É—ayan muke ba ai." Auta ta É—an haÉ—e fuska cikin sigar wasa ta ce.
"Faɗa mini wai wane karatun Ya Jafar ya biya miki da kika fito kina murmushi, yasin kowa ya fahimci a yanayin da kuka fito ke da shi." Uwani ta saki murmushi tana jin tamkar a lokacin Jafar yake sake faɗa mata daɗaɗan kalamansa, ta dubi Auta tana ɗaga mata gira ta ce. "Malama daina ambatar mini sunan miji kada ki sa gabansa ya yi ta faɗuwa, yarinya ba kin yi nauyin baki ba na ce zan faɗa wa Daddy Dr ya turo kin hana. Ai ke ma da anfara biya miki irin karatun da ake biya mini." Auta ta yi cikin gida tana dariya haɗe da faɗin, "Wallahi Uwani kin fi ƙarfina sai ki goge mini hadda."

Lokacin da su Jafar za su tashi sai da ya kira Uwani ya shaida mata sannan suka yi sallama, haka bayan da ya sauka ma bayan ya kira Mami da Daddy sai da ya kira ta. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya su Uwani suna ci gaba da karatunsu, yayin da Jafar ke ƙasar Sudan yana gudanar da aiki. Yawancin hirar Uwani da Jafar ta whatsapp suke yi, wani lokacin har video call suke yi musamman idan ba shi da duty a wurin aiki.

A wannan lokacin ne cikin Shukra ya tsufa, ganin haka ya sa Salim ya dawo da ita gida don gudun kada ba ya gida ciwo ya taso mata. Zaman Shukra a gida tsakaninta da Uwani babu yabo babu fallasa, saboda tun abin da ya faru take shakkar Uwani. Haka tsakaninta da Aunty sai gaisuwa amma ta daina yi mata kallon banza da habaici. A cikin wannan yanayin ne kuma ita ma Aunty ta fara wani irin zazzaɓi da ciwon ciki, ciwon Aunty ba ƙaramin tsorata Daddy ya yi ba. Hatta su Uwani sun tausaya mata ganin lokaci ɗaya ta yi wata irin rama, a ranar wata laraba ne ciwon ya matsanta mata ya sa Daddy ya ɗauke ta zuwa asibiti. Gwaje-gwaje aka yi mata, gaban Daddy sai faɗuwa yake musamman da ciwon cikin ne ya fi matsa mata. Yana fargabar kada a ce wani ciwon ne a cikin nata, da farinciki Dr Fadwa ta sanar da shi juna biyun da Aunty ke da shi, wani irin farin ciki ya mamaye Daddy ban da hamdala babu abin da yake yi.
Da yake Mami ta je garin Kaduna wurin gaisuwar ƙanwar mahaifinta, ya sa ba ta san duk wainar da ake toyawa. Ganin farincikin da su Daddy ke ciki ya sa Auta da Uwani suka keɓe suna gulmar ko dai abin da suke zargi ne ya tabbata.
Chapter 49 · 0% Book details