Sashe 32
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dada na jin abin da Uwani ta faɗa da sauri ta saka hannuwa biyu ta dafe ƙirjinta tana faɗin, "Ku dubi girman Allah kada ku yi banda da ni." Uwani ta sake cukwikwiyo ƙirjin Dada ta ce, "Mu ai ba da ke za mu yi banda ba, yanke waɗannan za mu yi. Kai ku ba ni laujen nan na girbe tsohuwar nan." Dada na jin haka ta rushe da kuka, dama tuni futsari ta gama jiƙe ɗan tofinta. Duk da a cikin duhu ne ba ta ganin Uwani amma sai ta haɗa hannuwa biyu alamar roƙo ta ce, "Don Allah ku taimaka ku yi mini rai."
Uwani ta yi wani gurnani ta dafa Dada tana wata irin girgiza ta furta, "Za mu rabu da ke, amma zan kira yanzu É—an autan kwaratan cikinmu sai ya miki fyaÉ—e don na ga ke taurin kai gare ki." Tun Uwani ba ta gama magana ba Dada ta sake rushe wa da kuka tana faÉ—in.
"Yau kam ni nake ganin rayuwa, ni Kulu yau ni ce kwarton aljani zai wa fyaɗe wayyo jama'a ku kawo nini ɗauki." Jin Uwani ta yi shiru ya sa Dada ta fara rarrafawa, sai da Uwani ta bari Dada ta kusa kai wa ɗaki ta sa hannu ta sake zugo ƙafafuwanta. Uwani tana cikiniyar sake riƙo ƙirjin Dada sai kawai Dada ta yi kukan kura har da wani zillo ta doke Uwani gefe ta faɗa ƙofar a guje ta shige ciki, Uwani saboda tsabar dariyar da take yi ƙasa-ƙasa har sai da ta kwanta. Ba ƙaramin mamakin ƙarfin Dada da gudun ta Uwani ta yi ba, a iya sanin ta Dada ko tafiya take tana ɗan ɗingisawa amma yau wuya ta sa ta ware ƙafa ta zuba a guje.
Duk budurin da ake yi wasu daga cikin mutanen ɗakin bacci suke yi, Uwani ta suri wayar cazar ta shiga ɗakin su Dada waɗanda suke kwance ta shiga fyauɗa musu, lokaci ɗaya ɗakin ya kaure da ihu da koke-koke. Gudun kada asirinta ya tonu ya sa ta yi saurin ficewa daga ɗakin. Da sauri ta laɓe a kusurwar bango ganin Daddy ya taho da sauri hankali a tashe, sai da ta ga Daddy ya wuce ta yi sauri ta wuce ta nufi sashenta.
Daddy na shiga É—akin ya kunna fitilar É—akin, a tsaye ya hangi Dada daga ita sai É—an tofi ta É—auki akwatin kaya ta É—ora a kanta. Fuskarta sharkaf da hawaye, ga wani irin fitsari da take saki lokaci-lokaci saboda tashin hankali.
"Dada lafiya kuwa? Mene ne yake faruwa?" Dada na jin haka ta sake rushewa da kuka tana faɗin. "Ni dai Mamman ka zo ka kai ni kura." Da mamaki ya zaro ido waje ya ce. "Kura fa Dada? A tsohon daren nan?" Dada ta gyaɗa kai ta ce. "Wallahi ganin idona yau har autan kwaratan waɗancen jinsin na gani, ni dai ba zan ambaci sunansu ba ballantana su ce da su nake. Don Allah Mamman dube ni tsofai-tsofai za a yi wa fyaɗe, tun daga ƙuruciya ban ga wannan iftila'in ba sai yanzu da komai ta saki kamar robar wando." Dada na zuwa nan ta sunkuyar da kai ta kalli ƙirjinta ta cikin kuka ta ci gaba da magana. "Ba don Allah ya dubi tsufana ba Mamma da tuni har 'yan mazauna ƙirjina za su tsintsinke, ni dai wallahi duk furucin da na yi jiya a wurin 'yan Jarida aikin sheɗan ne." Daddy ya sauke wa Dada akwatin kanta sannan ya furta.
"Dada har yanzu fa ban fahimci me yake faruwa ba." Sai da Dada ta share hawayenta sannan ta kwashe duk abin da ya faru ta faÉ—a masa, shiru Daddy ya yi abin duniya goma da ashirin ya mamaye shi. Ya mayar da kallonsa wurin ragowar mutanen É—akin da ke tsaitsaye suna susar wurin da Uwani ta shauÉ—a musu wayar caja.
"Dada yanzu don Allah ku yi haƙuri zuwa safiya, In shaa Allah zan san abin yi." Dada ba ta amsa ba sai sauran mutanen ɗakin ne suka amsa, Daddy har ya juya zai fita da sauri Dada ta riƙo hannunsa. "Wallahi Mamman ƙafata ƙafarka, mu je can ɗakinka har zuwa wayewar gari." Daddy bai musa ba ya jira Dada ta janyo doguwar rigarta ta shiga banɗaki ta wanke jikinta, ta saka rigar sannan suka fice daga ɗakin.
Koda suka je can É—akinsa a kan katifarsa Dada ta kwanta, tun tana gyangyaÉ—i har dai bacci ya yi awon gaba da ita.
Hannuwa biyu Daddy zuba yana tagumi saboda abubuwan da suke faruwa, mamakinsa bai wuce duk malaman da yake kira su yi karatu ba nuna masa suke gidan lafiya ƙalau yake babu wasu sheɗanu da ke ciki masu tayar da hankali. Mayar da kallonsa ya yi wurin Dada da ke ta sauke munshari, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ɗauro alwala ya tayar da sallar nafila.
A ɓangaren Mami ma ta jima bacci bai ɗauke ba sakamakon tunani da ɓacin ran da ya mamaye ta, sai da su Hajiya Falmata suka dinga lallaɓarta suna kwantar mata da hankali.
"Ƙawata wannan lamarin yana ɗaure mini kai, ni kam ban san jarrabawar da ta same ni ba. Yanzu babban tashin hankalina lokacin Dinner kada shi ma a sake hargitsa mini mutane." Mami ta furta ƙwalla na zuba, Hajiya Falmata ta furta. "In shaa Allah hakan ba zai faru ba, sai mu sa a yi addu gari na wayewa." Sun jima sosai suna ba wa Mami baki sannan ta ɗan saki jikinta.
Koda asuba ta yi Dada a É—akin Daddy ta yi sallar, bayan Daddy ya dawo daga sallar asuba da suka gama gaisawa da Dadda ya É—auki wayarsa kamar da wasa ya shiga Facebook. Gidan wata jarida ya ga sun wallafa rubutun da ya ja hankalinsa mai taken:
'Tattaunawa da mahaifiyar Babban É—an sandan nan DC Muhammad Mai shanu kan abin da ya faru a wurin taron bikin 'yarsa Shukra.'
Da sauri Daddy ya yi linking ga mamakinsa sai ga Vedio Dada raɗau tana jawabin da 'yan Jarida suka ɗauka. Dada na jin sautin muryarta tana gefe ta rushe da kuka ta ce, "Mamman don Allah ka taimake ni ka sa 'yan jaridar nan su goge wannan jawabin nawa, wallahi ko su goge ko kuma duka ka yi ƙararsu." Daddy ya yi kasaƙe yana ci gaba da kallon Video Dada ba tare da ya tanka ba har sai da ya gama sannan ya ce. "Dada ai aikin gama ya gama, da kanki fa kika ce su ɗani sautunki ga shi wasu har da vedio sun ɗauka. Ashe dama ke ce kika gayyato mutanen da suka tarfa ki da kanki?"
Dada ta sake yi tsilli-tsill da idanu tana hawaye, Daddy ya sauke ajiyar zuciya rai a ɓace ya furta. "Allah Ya kyauta." Yana kashe data ya fara cin karo da sakwanni a wayarsa na gidajen manyan Jaridu suna gayyatar a yi hira da shi a game da video Dada. Babu wanda ya yi wa replay, kuma kafin wani lokacin tuni vedio Dada ya zaga social media gabaɗaya, da yawan mutane sai suka mayar da shi abin barkwanci musamman da labarin abin da ya faru da Dada da dare ya ɗan fara ɓulla waje.
Bayan da gari ya waye Mami ta zo gaishe da Daddy bayan sun gaisa ya sa ta kira masa Shukra, fuskarta ta kumbura suntum saboda kukan da ta sha. Sai bayan da ta gaishe shi sannan ya ce. "Shukra duk abin da ya faru na ji labari har kawo abin da ya faru a cikin gidan nan da daddare. Mun yi kuma waya da Malam Idi mai Baƙara zai zo shi da ɗalibansa a yi karatu a gidan nan." Mami da Shukra suka gyaɗa kai sannan Daddy ya ci gaba.
"Sannan abu na gaba da nake son sanar da ke idan har akwai wani kiɗe-kiɗe da kuke shirin yi ku haƙura da shi, domin duk waɗannan abubuwan na sake janyo sheɗanu..."
"Daddy yau fa za mu yi Dinne kuma duk mun sanar da ƙawayenmu shi ma Salim ya gayyato abokansa..." Shukra ta katse Daddy cikin kuka. Ƙuri ya yi yana kallonta sannan ya ce.
"Shukra hanyar lafiya a bita da shekara, ki duba ki ga irin abin kunyar da aka ba ni labari ya faru a wurin taron na jiya, yanzu kun fi son ku yi abin da duniya za ta yi yawo da ku?"
"A gaskiya Daddyn yara ba ƙaramin kuɗi fa yaron nan ya kashe ba, yanzu don ƙaranta sai kawai a ce an fasa. Wallahi tsaf mutane za su ce dama can ƙarya muke ba a kama hall ɗin ba." Murmushin takaici Daddy ya yi sannan ya furta. "Lallai Saratu da alama har yanzu ba ki gama shiga taitayinki ba, amma tun da haka kika zaɓa ga fili ga mai doki." Shiru Mami da Shukra suka yi sannan ya ce, "Na gama za ku iya tafiya." Babu musu kuwa Shukra da Mami suka fita, suna fita Shukra ta ja hannun Mami ta furta. "Mami shi ma fa Salim ya gama tsorata don ya ce bazai je Dinner ba." Mami ta hangame baki jiki a sanyaye ta ce, "To yanzu me za mu ce wa mutane Shukra? Ke fa mace ce ke ba ki san kissar da za ki yi ki shawo kansa ba. Haba Shukra kina ga fa yanzu haka jirginsu Safna ya kusa sauka, yanzu ƙawayena me zan gaya musu?" Shukra ta share ƙwalla ta ce. "Shi kenan zan sake tuntuɓarsa na ji." Mami ta ci gaba da ɗora Shukra a kan abin da ya dace ta yi don ta shawo kan Salim.
Kusan ƙarfe goma na safe Jafar ya fito daga wanka yana tsaya a gaban mudubi yana taje kansa, wasu sababbin riga da wando ya fito da su kusan kala uku. Sai da ya zaɓi wacce ta fi kyau a ciki sannan ya saka, ya sake tsaya wa a gaban mudubi yana ƙare wa kansa kallo. Shigar Uwani ɗakin kenan ta bi shi da kallo ganin irin gayun da ya sha, rana ta farko kenan da ta ga Jafar ya yi masifar yi mata kyau. Lumshe idanu ta yi jin yadda take shaƙar ƙamshin turarensa, ta sake ware idanunta a kansa tana faɗin.