← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 71

Sashe 50

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A washegarin ranar ne kuma Shukra ta tashi da ɗan ciwon naƙuda sama-sama, don haka ta janyo jaka tana tafe da takalmi mai tsini ji kake ƙwas-ƙwas. Da Aunty suka haɗu Shukra na tafe tana cin cingam, da mamaki Aunty ta dube ta ta ce.
"Shukra lafiya? Ina zuwa haka?" Shukra sai da ta yi wani ƙas ƙas da cingam sannan ta ce. "Labour na fara na kira Baby yanzu za mu wuce asibiti." Uwani da zuwanta wurin kenan ta dubi Shukra tun daga ƙasa har sama, a ranta ta ce. "Ko da ban san ciwon haihuwa ba amma Aunty Shukra da alama ba ki fara cin ƙwal ubanki ba." Cikin salon gulma Uwani ta yi hanzarin riƙo akwatin Shukra ta ce. "Sannu Aunty Shukra! Ina za ki iya sauka da wannan akwatin, bari mu je ni da Auta mu raka ki asibitin. Ita kuma Aunty ko ruwan zafi ta dafa mana." Shiru Shukra ta yi da kamar ba za ta amince ba sai kuma ta sakarwa Uwani jakar tana tafe tana hura cingam. Jin horn a ƙofar gidan ya sa Shukra ta yi gaba tana faɗin, "Uwani ke da Auta ku yi sauri ga baby ya ƙaraso, kada ku sa na haihu a mota."

Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 Idan littafi ya kammala cmplt 800 ne🫠

#Ummou Aslam Bint Adam🌚

Har Shukra ta yi gaba Aunty ta bi ta tana faɗin, "Amma haihuwa Shukra kya tafi da su Uwani? Ba gara su zauna a gida ba ni mu tafi tare." Shukra sai da ta tauna cingam ta yi ƙwai da shi ta fasa sannan ta ɗan yamutsa fuska ta ce.
"No gaskiya ba sai kin je ba, just haihuwa ce kawai fa sai mun yi wata gayya. Ki zauna a gida kawai kamar yadda Uwani ta faɗa." Shiru Aunty ta yi don ba haka ta so ba, amma jin abin da Shukran ta faɗa ya sa ta amsa mata. A daidai wannan lokacin ne Su Auta suka ƙarasa sanye da hijabansu, tirtsi-tirtsi haka Shukra ta ci gaba da tafiya da tsohon ciki tana cangala ƙafafuwa da takalmi mai tsini. Har su Uwani sun yi gaba Aunty ta gagara haƙuri ta bi su tana faɗin.

"Uwani ki cire wayarki a silent zan kira na ji yanayin jikin nata an jima."
Amsawa Uwani ta yi tana kallon irin yauƙin da Shukra take yi, suna zuwa bakin gate suka samu Salim ya yi parking ɗin motarsa. Sai da suka zauna sannan Salim ya lura da Uwani, a ɗan zabure ya kalle ta. Yana son ya yi magana yana jin tsoro, tafiya suka fara yi kai tsaye suka nufi Zoo road asibitin Siyam Clinic da yake a can Shukra take yin awo.

Ta gaban Amnash Saloon za su gifta Shukra ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Baby ina son wanke kai kafin mu ƙarasa." Salim ya kalli ƙofar Saloon ɗin ya ce, "Amma baby ina tsoron kada ki haihu a ciki."Murmushi ta sakar masa a daidai lokacin ya yi parking ta ce.

"In Shaa Allah har za a gama." Shukra ta waiga wurin su Uwani ta ce.
"Ku fito za ku ɗan matsa mini ƙafa don na gaji." Uwani da Auta suka kalli juna ga gulma fal bakinsu ga babu damar yi.
Shukra na fita suka bi bayanta, Hajiya Maryam mai saloon É—in na ganinsu ta sakar wa Shukra murmushi saboda costomer ta ce.

"Maman biyu na ɗauka kin sauka ma?" Hajiya Maryam ta furta. " Shukra ta sake ɗan gantsarewa ta ce. "Ga mu dai muna fama, yanzu haka ai labour nake." Jinjina kai Hajiya Maryam ta yi suka ƙarasa ciki, ba a ɗauki lokaci ba aka gara mata kai tass. Uwani da Auta suna tsugunne kamar 'yan aiki suna matsa mata ƙafafuwa, ana gama gyara wa Shukra gashi suka wuce asibiti.

Ɗakin da aka kai Shukra su biyu da ita da wata matashiyar mata ita ma haihuwar fari za ta yi, amma ita har ta fara galabaita. A lokacin da Shukra ta shiga ne ta samu matar ta hau saman windon ɗakin, ta wala ƙafafuwanta tana faɗin.

"Ya subahanallahi, Summassabila yassara. Dr Hussain don Allah ka zo wallahi jaririn zai koma mini wuya."

A ɗan yatsine Shukra ta bi ta kallo ta ce, "Haba baiwar Allah mene ne haka kike yi? Yanzu idan Dr ya shigo ki ce masa me? Ko kunyar kanki ba kya ji sai wani yaye zani kike yi." Wani ƙululun baƙin ciki ya mamaye matar, ta sake maƙale window jin wani azabban ciwo ya murɗo mata ta ce, "Ya Allah ka ga wannan baiwar ta ka, Allah ka ɗauki cikina ka haɗa mata ta ji abin da nake ji." Shukra ta haye gado tana ɗaga waya tana selfie, tana sake gyara kwanciyar gashinta.

Su Uwani suna reception suna zaman jiran haihuwar Shukra, ta kira Jafar ta whatsapp a nan take sanar da shi suna asibiti Shukra za ta haihu. Sun ɗan taɓa hira da shi sannan suka yi sallama, suka tambayi wuri za su yi sallah don lokacin har sallar azahar ta yi. Wani ɗan ɗaki aka nuna musu bayan sun yi alwala suka shiga, a nan ne suka samu wasu mata guda biyu, ɗayar ta idar ta fita sai wata yarinya suka gani da ba ta fi shekara goma sha shida zuwa sha bakwai ba. Uwani har za ta tayar da sallah ta ga jikin yarinyar ya ɓaci ta baya, da alama baƙon watanta ne ya zo ba ta sani ba. Da yake Uwani ta ga su uku ne kawai a ciki sai ta taɓo ta ta ce, "Kin ga sallarki ta karye fa na ga jikinki ta baya ya ɓaci."
Yarinyar ta waiga a kunyace don ita ma ta san da halin da take ciki ta ce.

"Tun da muka zo ne dama na ga ya zo mini, to sai dai har yanzu Auntyn da na rako ba ta haihu ba. Amma Hajiyanta ta kusa zuwa idan ta ƙaraso zan koma gida, bari dai na yi sallah kada Aunty ta buƙaci wani abin." Da mamaki Uwani ke bin yarinyar don ta fahimci tamkar ba ta san hukuncin abin da yake jikinta ba. Kafin Uwani ta yi mata magana har ta ƙara tayar da sallah, Uwani ta sake taɓo ta tana faɗin. "Kin san idan fa ana Period ba a yin sallah ko ba ki sani ba?" Yarinyar ta gyaɗa kai sannan ta ce.

"Eh gaskiya ni ban sani ba don idan ya zo mini sallah kawai nake yi!"

"Idan kuma ya tafi fa ya kike yi?" Uwani ta wurga mata tambaya. Yarinyar ta wara hannuwa ta ce, "Shi kenan ba wani abu da nake yi. Ni dama takura ni yake yi shi ya sa wallahi duk wata ba na son ya zo." Ajiyar zuciya Uwani da Auta suka sauke, Auta ta ce.
"Ba kya zuwa islamiya ne ko ita Auntyn ta ki ba ta koya miki ba?" Take idanun yarinyar suka ciko da ƙwalla, a sanyaye ta ce.

"Lokacin da nake garinmu Innata ta saka ni a makarantar dare, to sai mahaifina ya cire ni ya sa aka kawo ni aikatau. Yanzu shekara ta huɗu kenan a garin nan, dama tun ina yarinya na fahimci mahaifina ba ya ƙaunata. Ita ma Innata da tana sona amma tun da, Ladidi dillaliya ta ba ta labarin kuɗin da ake samu a gidan aikatau shi kenan ta daina sona, saboda da sa hannunta aka kawo ni birni wai na tara kuɗin kayan ɗakin aurena." Yarinyar ta ƙarasa maganar tana hawaye, sai da share ƙwalla sannan ta ci gaba da cewa.

"Yanzu haka saura wata guda aurena da wani Gambo a garinmu yake shi zai aure ni, kuma ba yaro ba ne 'ya'yansa ma duk sun girme ni. Ga shi an ce matarsa masifaffiya ce, sai dai duk faÉ—in garinmu shi ne mai rufin asiri. Na fi tsammanin hakan ne ya sa mahaifina ya ba shi aurena."
Lokaci É—aya tausayin yarinyar ya mamaye su, Uwani ta ja hannun yarinyar gefe sannan ta ce.

"Ki yi haƙuri iyayenki suna sonki, a tunaninsu turo ki birnin ne zai rage musu wani raɗaɗin rashin da suke ciki. Amma haka za a yi miki aure ko ibada ba ki gama sani ba, shin kin san ma idan aka gama ana yin wanka kuwa?" Yarinyar ta girgiza kai tana faɗin.

"Na san dai sallah guda biyar ce a rana, amma ban san me ake faɗa a cikin sallar ba. Ina son na tambayi Aunty me take faɗa nake ganin tana motsa baki idan tana sallah, amma da yake Ladidi dillaliya ta gargaɗe mu da kiyaye abin da babu ruwanmu shi ya sa ban taɓa tambayarta ba."

"Innalillahi wa inna'ilahirraji'un." Abin da Uwani da Auta suka iya faÉ—a kenan, Auta jiki a sanyaye ta ce. "Kuma kin dade da fara fashin sallah?" Ganin yarinyar ba ta gane ba ya sa ta ce. "Ina nufin kin daÉ—e da fara ganin jinin jikinki." Yarinyar ta gyaÉ—a kai ta ce. "Eh zan yi shekara uku zuwa huÉ—u." Uwani da Auta ne suka shiga yi mata bayanin yadda za ta dinga gyara jikinta, don gudun kada ta dinga bari mutane na fahimtar halin da take ciki sannan Uwani ta É—ora da cewa.
Chapter 50 · 0% Book details