Sashe 52
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wa'iyazubillah, subhanallah ina Nurses ku zo ga mai laruri ta yi dama da ni, kuma subhanallah ta kasance ba muharrma ta ba." A daidai wannan lokacin Nurses suka ƙaraso suka kamata, suka wuce da ita ɗakin da take tana tafe tana ɗingisa ƙafa. Da sauri Aunty ta ƙarasa ɗakin Shukra, don shigowarta babu jimawa ta hango an wuce da ita.
"Hajiya wace ce ke?" ÆŠayar Nurse É—in ta tambayi Aunty. Aunty na shirin magana Shukra ta ce.
"Mahaifiyata ce, wallahi uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya da ita." Jin haka ya sa suka ƙyale Aunty ta shiga a fili suka dinga murmushin soki-burutsun Shukra, suka sake duba Shukra a wannan lokacin har ta kai 8cm. Bayan sun gama duba ta suka fita Shukra ta fara ihu.
"Shukra ki dinga salati kina addu'a kin ji In shaa Allah, Allah zai raba ku lafiya."
"Don Allah Aunty kada ki haihu, wallahi ganin idona yau na ga haihuwa na kawo mini farmaki." Aunty ta yi murmushi ta ce, "To shi kenan Shukra ba zan haihu ba."
Shukra ta ja hannun Aunty tana ƙoƙarin kai mata shi ƙasanta ta ce, "Don Allah ki fisgo jaririn nan ko na huta Aunty. Wayyo bayana wayyo marata, ya Allah ka mayar da cikin nan jikin Salim. Allah ka sa shi ma cikin nan ya fito masa ya haife shi, wai Aunty ko ke zan ba wa cikin nan ki haife mini?" Aunty ce ta shiga kwaɓar ta tana nusar da ita addu'o'in da ya da ce ta yi, lokaci ɗaya ciwon ya taso mata gadan-gadan da sauri Aunty ta fita ta kira Nurses ɗin, shigowarsu babu wuya Shukra ta haifo jaririyarta mai tsananin kama da Salim.
Littafin kuÉ—i ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala cmplt 800 neðŸ«
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*DoctorMaryamahGraphics and Data Services.*
MTN
•1gb ₦300
•2gb ₦600
•3gb ₦900
•5gb ₦1500
AIRTEL
1gb ₦350
•2gb ₦700
•3gb ₦1.050
•5gb ₦1.750
Glo
•1gb ₦300
•2gb ₦600
•3gb ₦900
•5gb ₦1500
9mobile
1gb ₦350
•2gb ₦700
•3gb ₦1.050
•5gb ₦1.750
Our Services:-
•Data Bundles
•Airtime purchase
•Cable TV subscriptions
•Recharge card
•Electricity Bills payment
•Converting Airtime to cash
•WAEC, NECO and jamb pins
Make payment into:-
3195402912 Firstbank Maryam Ibrahim
8136402046 Opay Maryam Ibrahim
Send the receipt into:-
+234 701 714 8194
Available 16hours📌 from 6am to 10pm.
And All types of different Logo invitation card and vide, save the Date and more_____
For more info:- 08136402046
Ba a ɗauki lokaci ba Nurses suka gyara Shukra da jaririyarta, Aunty ban da murmushi babu abin da take yi. Ta ƙura wa jaririyar ido cikin ranta tana harsashen nan da ɗan wani lokaci ita ma tana nan ɗauke da ɗanta ko 'yarta. Da kanta da fita ta nuna wa su Uwani jaririyar sai a lokacin Salim ya ƙarasa, a daidai lokacin ne kuma Hajiyar Salim da yayarsa Aunty Khadija suka ƙaraso. Salim ban da sakin murmushi babu abin da yake yi, nan take suka shiga ɗaukan jaririyar hoto. Auta ta ɗauki waya ta kira Mami ta sanar da ita, tana shirin kiran Daddy ya sauri Aunty ta katse.
"Auta ba za ki riga ni isar da sakon zuwan kishiya ba, ni zan kira Daddy da kaina na sanar da shi." Uwani ta saki murmushi sannan ta ce. "Ni ma bari na kira Nur na sanar da shi zuwa baby, kai bari ma na kira shi Video call." Da yake a yanzu sunan da Uwani ke kiran Jafar da shi, shi kuma yana kiranta da bakin tsiwa ko ya ce mata Jidda.
Daddy ba ƙaramin farinciki ya yi ba, a ɓangare ɗaya ya jinjina mutumcin da karamcin Aunty duk irin zaman doya da manjar da suke yi ita da Mami, hakan ba sai ta watsa wa jininta ƙasa a ido ba. Nan take ya ce musu zai ƙaraso asibiti, kafin ya kashe wayar ya yi wa Aunty tukwici mai tsoka.
Kafin wani lokaci tuni labarin haihuwar Shukra ya watsu daga danginta har zuwa dangin Salim. Da yake Shukra an sha ruwan zafi sai baccin wahala take sha, saboda dare ya yi a lokacin da ta haihu don haka likitocin suka ce sai da safe za su sallame ta, don su ƙara ganin kyawun jikinta da na jaririyarta. Aunty ce ta kwana a wurinta, Auta da Uwani suka koma gida. Uwani ta girka abinci Auta ta kawowa su Aunty da ruwan zafi, gabanin su Uwani za su fita daga asibitin ne kuma Madina ta ƙarasa da yake ranar tana da lectures sai bayan da aka yi haihuwar aka sanar da ita.
Tun da Shukra ta ga irin É—awainiyar da Aunty take yi da ita da jaririyarta jikinta ya fara sanyi, game da irin rashin mutumcin da ta dinga yi mata a baya. A daren ranar jaririyar kwana ta yi tana rigima, amma Aunty ta ce Shukra ta kwanta ta yi bacci bayan ta ba ta mama ta sha, ita ta ci gaba da kula da ita. Washegari da sassafe sai ga Mami ta dira a asibitin, ko da ta shiga É—akin da Shukra take sallama kaÉ—ai ta yi wa Aunty amma ko ya me jego ba ta ce mata.
"Shukra yanzu me yake damunki? Babu dai wani abu da kike buƙata, don kin san wani abin dole sai uwa ce za ta yi maka shi." Mami ta furta a gadarance, Aunty ta ji zafin maganar amma sai ta yi kamar ba ta fahimci zancen Mami ba. Ta danna wayarta ta kira Daddy tana faɗin.
"Ranka ya daɗe na fa turo maka hoton amaryarmu na Good morning, ni sai da na turo maka ma na ce an ya wankanta ba zai ƙwace mana kai ba." Aunty ta ƙarasa maganar tana ajiye jaririyar a kan cinyar Mami ta fita ta ba su wuri, ta yi haka ne domin kada Mami ta lura maganarta ce ta ba ta haushi har ta fita.
"Mami gaskiya abin da kika yi bai kamata ba, matar nan mene ne ba ta yi mini ba? Tun fa jiya take wurin nan ko motsi na yi sai ta ce ko akwai abin da nake buƙata, kuma idan ina so nan take za ta yi mini yanzu kuma ki faɗi haka? Ni wallahi yanzu ma kunyarta nake ji a kan abubuwan da na yi mata a baya, wallahi na fahimci mutumiyar kirki ce..."
"Ke dalla rufe mini baki." Mami ta katse Shukra a zafafe.
"Ai kin haihu yanzu gani kike matsayinmu ɗaya dole ki faɗa mini abin da ranki ya so, sakarai shashasha. Maƙiyinka dama yana sauyawa ne ban da haukanki?" Shiru Shukra ta yi ta tura baki gaba tana jin babu daɗi akan abin da mahaifiyarta take faɗa.
Koda aka sallame su zuwa gida Aunty ba ta fasa duk wani abin kyautatawa da take yi wa Shukra ba, don hatta wanka ita take yi mata duk da ba wankan ganye ba ne saboda likitoci sun ce kada ta yi da shi don yana iya kawo hawan jini.
Da yake a wannan lokacin Safna ta dawo daga India haka ta haÉ—o wa Shukra kayan barka akwati guda, kayan jaririya kala-kala kallo É—aya za ka yi musu ka tabbatar da an watsa narkakkiyar dukiya a ciki. A haka lokaci ya ci gaba da gangarawa har aka yi suna, yayin da yarinya ta ci sunan Hajiyan Salim wato Nauwara. Kwanan Shukra goma ciff Daddy ya ce ta koma É—akinta, a cikin danginta ne Mami ta samo wacce za ta ci gaba da zama da Shukra a gidanta.
Bayan da aka yi suna ne ita kuma Aunty laulayi ya saka ta a gaba, har ya zamana duk ranar gidanta sai dai Auta da Uwani su yi abinci. Saboda wani lokcin da ta ji ƙamshin girkin za ta fara kwara amai, tuni Auta da Uwani suka ranfo Aunty. Sai dai Auta na son sanar da Mami tana tsoron faɗanta, saboda haka ta ja bakinta ta kulle.
Sannu a hankali Mami ta fahimci halin da take ciki, a lokacin hankalin Mami ba ƙaramin tashi ya yi ba. Ita dai ci wa kanta alwashin ba za ta taɓa zuwa wurin wani malami ta kai kukanta ba. Amma duk hanyar da za ta bi cikin makirci da tuggu ta ƙudurta a ranta sai ta bi ta salwantar da cikin jikin Aunty.
Ginin gidan da Daddy ya sa ake yi wa Jafar ba ƙaramim nisa ya yi ba, duk wata sai ya turo da kuɗi domin a ci gaba da aiki. Sai dai shi a tsammaninsa wurin zaman mace ɗaya ne, amma tun asalin fitar da famdisho Daddy ya sa aka fitar da tsarin zaman mace biyu. Hatta Mami ba ta san da wannan tsarin ba, abu ɗaya Mami ta dage a kansa shi ne haɗa kayan lefen Safna. Don ta yi lefe na bajinta har wani filinta ta sayar ta haɗa ta sayo wasu danƙara-danƙaran lesuna.
Su Uwani hada-hada suka shiga ta saukar Alƙur'ani da za su yi, tare da Candy sai dai tarazar kwana biyu ne a tsakani. Ranar Laraba suka yi candy yayin da suka yi bikin sauka ranar juma'a. Ɗalibai da yawa ne suka yi sauka aka raba musu kyaututtuka gwanin birgewa. Duk wanda ya halarci taron sai da su Uwani suka birge shi, bayan wani lokaci kowa ya watse suka wuce gida aka shiga gudanar da walima. Auta da Uwani tamkar tagwaye haka suka yi anko aka yi musu kwalliya gwanin birgewa, saboda wanda bai sansu ba idan ya gan su zai yi tsammanin ciki ɗaya suka fito. Domin ta ɓangaren kamanin suna yanayi sakamakon Uwani na fisgar kama da Daddy, kuma dama mahaifinta, baba Inusa da Daddy duk sun fi kama a cikin 'ya'yan Dada.
Maryama mahaifiyar Uwani takanas ta sa aka kawo wa Uwani da Auta tinkiya da rago a cikin awakin da take kiwo, lokacin da Daddy ya gani ya ji daɗi amma sai ya ce da ta ba su koda tinkiya ce a yanka musu, a yi sadaka ba sai ta haɗa da rago ba amma ta ce dama can ta ƙudurta haka a ranta. Ta shiga yi wa Daddy godiya bisa jajircewar da ya yi a kan tarbiyya da ilimin Uwani, sai da Daddy ya gama sauraronta ya ce.