Sashe 14
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yaya Shukra lafiya? Me ya same ki a goshi? Mene ne wannan yake wari a jikinki kamar kwata? Ina shi Yaya Salim ɗin?" Auta ta jero mata tambayoyi, sai dai babu ɗaya da ta iya amsawa ban da hawaye da ke shatata a fuskarta. Mami da Auta suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan ta faɗa musu abin da ya faru, suka shiga zagin Ba ka da nauyi suna mamakin in da Salim ya je bayan motarsa na ƙofar gida.
Jin ihun Dada ya sa su Atika shiga sashenta da sauri, ganinta a daskare daga ita sai ɗan tofi ya ba su mamaki domin Dada ba ta taɓa sauya kaya a gaban mutane.
"Dada lafiya?"
Hannu na rawa ta nuna uwar É—akin.
"Wani tabbataccan kwarto ne ya fisge mini zani ya yi uwar ɗaki. Ni Kulu ban san uwar me zai laluma a jikin tsohuwa ba." Da sauri su Atika suka leƙa ɗakin, ba su iya hango komai ba sai 'yan idanun Salim da ke duƙe a ƙarƙashin gado. Fa'iza ce ta kira Baba Isuhu, da sauri ya ƙarasa hannunsa ɗauke da ƙatuwar gora ya fisgo Salim.
Sai dai sororo ya yi yana bin yadda halitar fuskar Salim ta sauya.
"Wa nake gani kamar Salim? Kai uban me ya kai zanin Dada hannunka?"
Salim da gefen baki zuwa fuskarsa ya kumbure sundundun ya ce, "Baba wani mahaukaci ne zai sauke mini fuska don Allah ku ɓoye ni. Ya ɗauke Shukra a ka ma ya tafi da ita." Sai a lokacin suka fahimci wurin da maganar Salim ta dosa, Baba Isuhu ya miƙa wa Dada zaninta. Ya kama hannun Salim suka fice Salim sai tirjewa yake, a zuciye baba Isuhu ya waigo ya furta.
"Me kake yi haka ne wai? Ka san Allah ka ci sa'a na gane kayan jikinka don mun gaisa ɗazu kana ƙofar gida, wallahi da don ta wannan sukunbiyar fuskar taka ne ba zan gane ka ba. Dubu fa yadda ka koma fuska kamar ta sumammiyar akuya. Mu je na raka ka ƙofar gida ka tafi don indai Ba ka da nauyi ne fiye da haka ma zai yi maka." Sai a lokacin Salim ya saki jiki suka ƙarasa, da sauri ya shige mota ya fusge ta da gudun gaske ko waige ba ya yi.
Su Dada suna tsaye suna mayar da yanda aka yi wayar Dada ta fara ringing, da sallama ta É—auka jin muryar Maryama mahaifiyar Uwani ya sa ta furta.
"Ke kuwa Maryama da ƙuruciyarki amma waya ta nemi ba ki wuya, tun daren jiya nake kiranki na sanar da ke abin alheri amma waya a kashe." Maryama cikin shasshekar kuka ta ce. "Dada hankalina ne ba a kwance ba."
"To Allah ya rufa asiri ai ni dama tun da na ga yanayinki na san Aramma na zalintarki, ki ci gaba da haƙuri Maryama komai ya yi don kansa." Maryama ta saki kukan da ke cinta, Dada na son Maryama shi ya sa duk lokacin da suka yi waya take tausarta.
"Kin ga ki yi shiru 'yar nan su maza fa haka suke, ni tsorona ma kada Aramma ya zo ya ji kina mini kuka ya ce ko Umaru kika tuno. Yanzu dai ba wannan ba jiya da dare dai an cika alƙawarin da aka ɗauka, Uwani dai an ɗaura aure ita da Jafar. Abin ne ya zo a gaggauce, amma dai tariya sai nan da watan maulidi." Maryama ta ji daɗi don ta san waye Baba Mamman, amma har a ranta ta so a ce Uwani ta yi hankali kafin ɗaurin auren. Sai da ta kwararo addu'a sannan ta sanar da Dada dalilin kiranta.
"Dada dama kiranki na yi na faɗa miki Me sunan Iya ce ta rasu (Babbar 'yarta ta gidan Aramma.)" Salati Dada ta rafka sannan ta yi mata gaisuwa ta kuma yi mata alƙawarin washegari za su shiryo su zo mata gaisuwa. Bayan sun gama waya Dada ta miƙa wa Uwani waya, suka gaisa sannan ta yi masa sallama.
Kimanin ƙarfe goma na safe su Dada suka isa ƙauyen da mahaifiyar Uwani take aure, sun yi kara sosai don har su Baba Yunusa gabaɗaya suka je mata da matansu. Tun da suka faka motoci yara ke zuwa kallonsu, mazan suka zauna a tabarmar da ke ƙofar gida suka tambayi mijin Maryama aka ce musu ya shiga cikin gida. Su Dada kuma suka shiga ciki.
"Gata nan da ran Allah ita ta san inda ta kai mini yarinya aka cinye ta, amma idan ta zauna ta ishi mutane da kukan munafurci. Daga zuwanta garinsu ta dawo da yarinya ba lafiya, wai muna zuwa aibitin gangare da suka tura mu babban asibiti a binni aka ce sikila ce, yo ban da ƙaryar likitoci lokacin iyaye da kakanni aka san wata sikili? Ta kai mini yarinyar dai mayu sun cinye kawai." Shigar su Dada gidan suka samu Aramma na zazzaga wa Maryama masifa yana kumfar baki, tana durƙushe a gefen yayan Aramma da ya zo yi mata gaisuwa. A lokacin Aramma ya zo wucewa ya shi ne yake yi mata sababi. Ganin su Dada da yanayin shigarsu ya sa ya hau yashe baki. "Barkanku da zuwa Hajiya."
"Barka dai." Dada ta amsa a daƙile. Jin muryar Dada ya sa Maryama ta miƙe tana goge hawaye ta shiga yi musu sannu da zuwa.
"Ai kuwa wannan mutumin sai na gyara maka zama." Uwani ta faÉ—a a ranta.
Maryama jiki a sanyaye ta miƙe za ta wuce da su ɗaki.
"Ke Maryama wanne irin rashin hankali ne haka kina ganin baƙi ba za ki kai su ɗaki ba." Aramma ya faɗa cikin faɗa shi a dole sai ya birge su Dada. Ɗaki ta kai su bayan sun gaisa suka yi mata gaisuwa cikin jimami, Dada har cikin ranta ba ta ji daɗin irin zaman da Maryama take yi da Aramma ba, domin mace ce mai sanyin hali da haƙuri. Duk wanda ya santa idan ya san Uwani dole zai ce albasa ba ta yi halin ruwa ba. Aramma jikinsa har rawa yake ya sa aka sayo musu ruwa, ba su jima sosai ba Dada ta kawo kuɗin sadaka dubu biyar ta bata. Sauran sirikan Dada kuma mai ɗari biyar mai dubu ɗaya duk suka haɗa mata, lokacin da za su tafi ne Dada ke ce wa Maryama Uwani za ta zauna har sai an yi sadakar uku za ta tafi. Har ƙofar gida Maryama ta raka su, su Baba Idris suka yi mata gaisuwa, suma suka kawo abin sadaka suka ba ta da shi ma Aramma. Har sun ɗauki hanya za su tafi Dada ta dawo ta ja Maryama gefe tana yi mata raɗa.
"Dama kuÉ—in da aka ba ki ko da wasa kada ki ba wa wannan mijin naki kin ji Maryam!" Maryama ta gyaÉ—a kai jiki a sanyaye sannan ta raka Dada bakin mota tana É—aga musu hannu.
"Dada gaskiya zan yi kewarki kwana biyu an ya ba biyo ku zan yi ba?" Uwani ta faÉ—a tana tura ba ki gaba.
Dada ta watsa mata harara sannan suka wuce.
Tun da suka koma cikin gida Uwani ta lura da mahaifiyarta sam ba ta da nutsuwa, suna nan zaune sai ga Aramma ya shigo.
"Ke Maryama kawo abin sadakar nan da aka ba ki zan haɗa a yi abincin rana." Tamkar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki haka Maryama ta miƙe jiki ba ƙwari ta kunto kuɗin wurin su Baba Idris ta miƙa masa. "Ke ba na son shashanci da rainin hankali, kina nufin su matan ba su ba ki komai ba? Wai Maryama me ya sa kin fiye baƙin halin tsiya ne." Ran Maryama ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ganin irin tozarcin da Aramma yake yi mata a gaban Uwani da kuma sauran mutanen da suka zo gaisuwa. Don haka rai a ɓace ta ce.
"Wai Aramma ya kake so na yi ne? Me ya sa..." Tun ba ta gama magana ba Aramma ya É—auke ta da mari, yana shirin kai mata duka Uwani ta shiga tsakaninsu ta furta.
"Baba bari na miƙo maka kuɗin a cikin jakar can ta ajiye dama na ji ta ce za a auno garin masara a yi tuwo, amma bari na miƙo maka." Jin haka ya sa Aramma ya washe baki ya ce. "Ka ji yarinya mai hankali maza miƙo mini, ke dai kin yi asarar hali Maryama."
Babu musu Uwani ta zuge jakar da ta ga mahaifiyarta ta zuba kuɗin a ciki, ta ɗebo su duka ta miƙa masa.
"Kai Allah wadaran naka ya lalace wallahi Maryama kin ji kunya ace wai har 'yar cikinki ta fi ki hankali." Wasu daga cikin ƙannen Aramma suka bi mahaifiyar Uwani da baƙaƙen maganganu. Ba ta tanka musu ba sai ma ruwan hawaye da ke tsiyaya daga fuskarta. Uwani na daga gefe ta ci gaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kowanne tana zana gashin azabar da za ta yi musu daga baya.
Sai da mutane suka ragu a ɗakin sosai daga Maryama sai 'yan uwanta ta dubi Uwani ta ce. "Me ya sa za ki ɗebi kudina ki ba shi." Ta ƙarasa maganar fuska a haɗe.
"Gobe da safe zai dawo miki da su Inna rance na ba shi!" Uwani ta furta cikin rashin damuwa.
"Rance fa? Ta ya ya zama rance bayan a kan idona kika ba shi?"
"Allah Inna kada ki damu zai dawo miki da kuɗinki har ma ya ƙara miki wasu." Jin sokiburutsun Uwani ya sa Maryama ba ta sake bi ta kanta ba saboda takaici.
"Maryama yaya aka yi kika bari har ya ga lokacin da aka ba ki kuɗin nan? Kin fa san halin mutumin nan sarai, ba shi da tausayi ko kaɗan." Indo kishiyar Maryama ta furta ƙasa-ƙasa.
"Ai kin san tun da ya gan su ya san za su ba ni wani abu, kuma ragowar ma ba ni na ba shi ba yarinyar nan ce ta ba shi." Maryama ta furta. Suka gama jajantawa juna, don zaman da suke yi sam babu kishi a ciki saboda dukkansu ba wani daÉ—in zama da shi suke ji ba.