Sashe 5
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni fa Mamman ban ce ka kira shi ka yi masa tijara ba, ina zaman zamana Jafaru ya zo ya cika ni da nunkufurcin tsiya. Ni ban san ma lokacin da Saratu ta koya maka masifa ba, yara irinsu Jafaru sai addu'a da lallashi. Kai kanka Mamman ba don tsayuwar da na yi a Harami ba ai da ban san abin da za ka zama ba, Allah dai Ya shirya mana zuri'a." Baba Mamman ya yi murmushi ya amsa mata sannan suka yi sallama. Uwani sam ba haka ta so wayar ta kasance ba, don haka ta miƙe har za ta fita sai kuma ta wuce uwar ɗakin Dada tana sakin murmushi. A can ƙarƙashin gado ta ciro bankinta ta ƙwaƙulo kuɗaɗen da suke ciki, sai da ta ƙirga su kusan dubu ɗaya da ɗari biyar ne. Ta ɗaure su a ɗankwali haka kawai ta fara sakin murmushi, Dada ta bi ta da kallon mamaki baki a sake.
Baba Mamman na kashe waya ya kira Jafar ya yi masa faɗa sosai, tare da nuna masa illar tsoratar da Dada da ya yi musamman da shekarunta suka tura. Jafar ya fahimci mahaifinsu sai dai shi tsokanar Dada yake da ya ce harbe ta zai yi. Can ƙasan akwatinsa ya je ya tura bindigar ya ajiye sannan ya shiga banɗaki ya watsa ruwa ya wuce ɗakin Dada. A nan ya shiga tsokanarta suka fara hira har Malam na Madina kamar ba shi ne ya gama kabbara yana naushinsa ba.
Uwani na fita can kantin Ɗan bala ta wuce ta sayo alawa irin da raɗin suna leda biyu, sai ta ƙarasa wurin Ali mai dabino shi ma ta sayo gwangwani uku. Sai da ta tsaya a gefen hanya ta kunce kowacce leda ta zuba kofato biyu da ragowar jelar tumaki ɗai-ɗai sannan ta ɗaure. Tana tafe tana sakin murmushi har ta ƙarasa gida, kai tsaye sashen Baba Isuhu ta nufa za ta shiga kenan ta gan shi ya fito da alama masallaci za shi don an kira sallar Magriba.
"Sakaryar banza ke ba kya ganin mutane ne?" Baba Isuhu ya furta yana wurga wa Uwani harara.
"Ga shi wata mata ta ce na kawo maka." Uwani ta faɗa tana miƙa masa ledar hannunta. Da mamaki ya karɓa ya furta, "Wata mata kuma? Ba kuma Lami aka ce ki kai wa ba?" Uwani ta girgiza kai cikin alamun tsoro ta ce.
"Kai ta ce a kawowa kuma ni fa idanun matar ya ban tsoro wallahi, Baba Isuhu dama mutane suna da kofato ne ban taɓa sani ba sai yau?"
A firgice Baba Isuhu ya saki ledar alawar ya ce.
"Kofato fa? A ina kika ga kofaton?" Uwani na ganin yadda ya firgice sai ta basar ta ce, "Bari dai na wuce wurin Dada..."
"Don ubanki za ki tsaya ki mini bayani ko kuwa?" Baba Isuhu ya yi magana jiki na rawa, don bai jima da barin gidan Talle Mai gari ba, da yaje duba shi sakamakon yana kwance sharɓan. Kuma a dubiyar da ya je ne yake shaida masa abin da ya faru da shi a banɗaki da kuma ɗakinsa.
"Eh matar ce na ga ƙafarta da kofato, sai ta miƙo mini ledar nan ta ce na ba ka. Kuma ta ce na faɗa maka idan ka wurgar da saƙon nan a kan mai sunan malam za ta fanshe."Da sauri Baba Isuhu ya tsugunna ya fara tattaro dabino da alawar, a nan idanunsa suka ci karo da kofato, tuno abin da Uwani ta faɗa ya sa jikinsa na rawa ya haɗa ledar ya sa a aljihu ya dubi Uwani ya ce.
"Ina matar take yanzu." Uwani ta zuba hannu biyu ta yi tagumi ta ce. "Ni fa tana ba ni ledar nan da na waiga sai ban ganta ba, wallahi ina jin ɓacewa ta yi don kamar ƙiftawar ido haka na neme ta na rasa." Wani irin sanyi ƙafafun Baba Isuhu suka yi, Uwani ta yi kamar ba ta gane yanayin da yake ciki ba ta shige cikin gidansa.
Baba Isuhu yana nan tsaye har zai fita ko me ya tuna da sauri ya faɗa cikin gida, yana tafe hawaye na zuba don jikinsa ya gama ba shi ta shi ta zo ƙarshe. Uwani na daga ɗakin Lami ta hango shi nan da nan ta ƙunshe dariyarta, yana shiga ɗakin ita kuma Goggo Sala na sirka ruwan wanka don aiki ne ya hana ba ta yi wanka da wuri ba.
"Lami ni kam na shiga uku!" Da sauri Lami ta kalle shi, Uwani na jin haka ta muƙe ta fice. Da yake ta lura hankalinsu ba ya kanta kai tsaye ta bi hanyar banɗakin da Goggo Sala ta bi domin yin wanka.
Lokacin da Uwani ta je wurin banɗakin Goggo Sala ta riga da ta tuɓe har ta fara wanka, a hankali ta saɗaɗa ta janye kayan da ta cire. Sannan ta fara wani irin gurnani tana kukan tinkiya. Goggo sala ta riga da ta saɓa sabulu a fuska da sauri ta dakata, jin ta daina wankan ya sa Uwani ta yi wani gurnani mai ɗan tsoratarwa sannan ta maƙe murya ta ce.
"Gani gare ki Goggo Sala, ki nutsu ki saurari abin da zan faÉ—a miki domin zai yi miki amfani a matsayinki na jinsin bil'adam." Nan take jikin Goggo Sala ya É—auki karkarwa kamar mazari, hannu biyu ta sa ta fara kiciniyar goge kumfan fuskarta amma yajin sabulu ya hanata buÉ—e ido.
"Nan wurin da kike wanka masarautarmu ce, kuma kina tsaye ne akan karagar shugabarmu ga hadimanta nan sai zagaye ki suke yi. Wani abin haushi kin saka su kallon tsiraici, don ma Allah Ya taimake ki aljani Manu É—an kwarto ba ya kusa da tuni ya haike miki." Jin haka ya sa Goggo Sala ta fashe da kuka, Uwani ta gimtse dariyarta ta cigaba da cewa.
"Ni ce uwar garke wacce kika dafa namanta, to yanzu haka na dawo domin ni dama ba tinkiya ba ce. Kuma namana da kika dafa a tukunya na ɗauke shi na kai garkena, sannan zan kafa miki wani sharaɗi matuƙar kika saɓa masa zan ɗauke ki zuwa duniyarmu."
Goggo Sala baki na rawa ta ce. "To Babata uwar garke faÉ—i kowanna sharaÉ—i ne ni mai biyayya ce a gare ki." Uwani ta sa hannu ta toshe dariyarta ta ci gaba da cewa.
"SharaÉ—in shi ne kullin za ki dinga goya Isuhu sau uku a rana, safe, rana da kuma dare. Idan kika zo goya shi ki dinga yi kina lasar baki, kuma idan kika kuskure koda na lokaci É—aya ne ba ki yi ba take zan É—auke ki ko kuma na tsotse romon kanki."
"Wallahi zan yi ba dai goyo ba, ko har da Lami aka ce zan haÉ—a na goya su." Goggo Sala ta faÉ—a cikin kuka.
"Kin taimaki kanki, yanzu kayan da kika cire zan kai shi garkena amma zan bar miki ɗankwali, kuma kada ki kuskura ki fito sai an kira sallar Isha'i domin anfara tattaunawar fadar aljanu da ke. Sannan ɗan autan shugabanmu ya ce da baya da baya za ki tafi ɗaki kina cewa nasara a kanku Isuhu da Lami." Goggo Sala ta amsa, a zuciyar tana da-na-sanin zuwanta zaman daɓaro gidan Lami.
Uwani na gama maganar cikin sanɗa ta koma har lokacin baba Isuhu yana ɗakin don ta hango shi ta cikin labule, ta raɓe a gefen ƙofar ɗakin ta karkace murya ta fara kukan tinkiya. Shiru ta ji sun yi sannan ta yi wani gurnani tana yi tana buga ƙafa irin tsalle-tsallen da awaki suke yi.
"Shi kenan Lami ta zo ina jin tafiya za ta yi da ni." Baba isuhu ya faÉ—a cikin kuka.
"Ba zan tafi da kai yanzu ba. Ni uwar garke ni ce na aiko maka da saƙo ɗazu. Ku buɗe kunnenku da kyau, uwar garke ba mutum ba ce. Na zo na kafa muku sharuɗɗana idan kuka bi su zan yafe muku zunubin da kuka aikata mini, idan ba haka ba kuma a gabanku zan yi farfesun mai sunan malam na saka ku cinye shi kuma ku shanye romonsa."
"Wallahi ko mene ne kika ce mu yi za mu yi miki biyayya." Lami ta faÉ—a a tsorace.
"Kai Isuhu da farko taimakonka za mu fara yi kafin ka ji sharaɗinmu. Ƙanwar mahifiyar matarka babbar matsafiya ce a ɓoye, kuma dama da biyu ta zo zaman daɓaro gidanka. Idan kuma ka yi yunƙurin korarta za ta halakaka da iyalinka gaba ɗaya. Daga gobe ne wa'adin aikin da take yi a kanka zai fara, don haka yanzu ma za ku ga ta fito tana tafiya da baya-baya tana ambatar sunanku don haka kada wanda ya tanka mata. Kuma gobe za ta zo da sassafe ta ce maka za ta goya ka. Duk rintsi kada ka bari ta taɓa maka jikinka."
A zabure Baba Isuhu ya ce. "Goyo fa? Ni Isuhu za a goya da giramana ban da iskanci?" Uwani ta katse shi.
"Idan muna magana ba a tankawa. Sannan SharaÉ—in da za mu kafa maka ya zama wajibi ka É—auki rigunan mama na Lami guda uku ka kai wa mahaifiyarka Dada ka ce ta saka su..."
"Dadar ce za ta saka bireziya..." Baba Isuhu ya furta cikin suɓutar baki. Uwani ta buga masa tsawa cikin gurnani ta ce.
"Idan ka saɓa mana wallahi sai mun hallaka ka da kisa mafi muni." Nan take Baba Isuhu ya ce. "Duk abin da kika ce na bi Inna uwar garke."
"Na dawo gare ki Lami. Ke kuma akwai dafin da Goggo Sala ta saka miki a ruwan wanka wanda wa'adinsa gobe zai cika, ko ba kya ganin irin maganin da take zuba miki a ruwan wanka kullin?" Da sauri Lami ta gyaÉ—a kai.
"Idan kika sake shayar da ai sunan Malam daga gobe ke da shi mutuwa za ku yi, domin dodonta zai zuƙe jininku tas." Da yake Lami ta san Goggo Sala da shegen bin malamai nan take ta aminta da kalaman Uwani.
"SharaÉ—in da zan kafa miki ya zama dole daga gobe ki dinga É—aukan mai suna Malam kina kai wa Jafar shi yana shayar da shi a sashen Dada." Cikin haÉ—in baki Lami da Baba Isuhu suka ce.
"Jafaru kuma? Shi zai shayar da mai sunan Malam?"