Sashe 46
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy ya sauke ajiyar zuciya zai yi magana suka ji sallamar Jafar, kafaÉ—arsa É—auke da jaka. Da mamaki duka suka dube shi, Dada ta yi saurin faÉ—in. "Wa nake gani kamar Jafaru?" Jafar ya yi murmushin gefen baki. Daddy cikin mamaki ya ce. "Jafar lafiya zuwa babu waya?" Jafar sai da ya sauke jakarsa ya zauna sannan ya ce. "Wallahi wata muhimmiyar magana ce ta kawo ni Daddy."
Littafin kuÉ—i ne 500 za ki turo ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala 800 neðŸ«
Uwani sai da ta ci bacci ta ƙoshi sannan ta tashi ta sake faɗa wa banɗaki ta watsa ruwa, ƙugi cikinta ya shiga yi saboda yunwa don haka ta saka wata doguwar rogar atamfarta ta ɗauko ƙaramin hijabinta ta ɗora ta fito falo. Jungum-jungum ta ga su Shukra sun yi gaba ɗaya suna zauna a falon, kowanne ka dube shi fuska ɗauke da damuwa. Washe baki Uwani ta yi ta ce, "Aunty Shukra wallahi ina shiga ɗaki daga kwanciya bacci ya ɗauke ni." Shukra a ranta ta furta. "Lallai yarinyar nan kin raina mana hankali." Amma a fili sai ta saki murmushin yaƙe ta ce, "Ai da Baby har zai taso ki na ce ya ƙyale ki jiya kin sha aiki dole ki huta..." A zabure Salim ya katse Shukra, "A gidan Uban wa zan tashe ta?" Dariya ta so ƙwacewa Uwani sai ta basar, ta mayar da kallonta wurin Saminu da goshinsa ya yi wani malolo ta ce. "Ya Salim dama wannan mutumin bai tafi ba?"
"Ba aljanunki sun haɗiye mukullin ba." Saminu ya faɗa a ransa. Uwani ta ɗago mukullin kamar ta san abin da yake ransa ta ce. "Ni wannan ko key ɗin ƙofa ne? Ina cikin bacci kawai ma ji an damƙa mini shi a hannuna." Da sauri Saminu ya karɓi mukullin baki na rawa ya ce. "Yawwa bari na je dama fa yanzu nake shirin tafiya." Saminu na buɗe ƙofa Salim ya yi caraf zai bi shi da sauri Shukra ta riƙo rigarsa ta ce.
"Ina za ka tafi ka bar ni." Salim ya ce. "Office zan tafi baby."
Shukra ta janyo shi ba ya ta ce, "Salim dama kana zuwa office ba ka yi wanka ba." Uwani a zuciyarta ta ce. "Yanzu wuya ta sa ba za a kira shi da Babyn ba ne?"
Salim ya fara kiciniyar ƙwacewa don tun da ya samu hanyar fita, babu yadda za a yi ya zauna a cikin bala'i. Shukra ta sake fusgo shi ganin Saminu zai tsere masa ya sa Salim ya riƙo rigarsa yana faɗin.
"Abokina don Allah kada ka tafi ka bar ni." Saminu ya juya ya doke hannun Salim, ya shiga kiciniyar ƙwace kansa ya ce.
"A'a Salim wannan lamarin na ku family issuee ne daga yau kada ka sake kira a kan matsalarka." Lokaci ɗaya Saminu ya shiga fisgewa Salim na riƙe da shi, shi kuma Shukra ta ƙwaƙume rigarsa. Uwani ta saka hannuwa biyu ta toshe kunnenta ta ƙwalla ƙara tana ce wa, "Kaaaaaaaaiiii" A zabure gaba ɗaya suka fita a guje cikin tashin hankali. Gali mai gadi na zaune yana jin redio ya ga Saminu ya fito a guje yana faɗin. "Wayyo Allah jama'a ku taimaka aljanu za su ƙarasa illata ni." Jin takun Shukra a bayan Salim ya ƙara faɗar masa da gaba a zabure shi ma Salim ya zuba ihu yana faɗin,
"Gali! Wayyo Gali ka kawo mini ɗauki, wallahi aljanu ne suka sauke danginsu a ciki." Gali miƙewa ya yi tsaye ganin mutanen gidan gabaɗaya sun fito suna ihu ya sa ya banka ƙofar ɗakinsa a guje ya danna saka.
Nan take suka shiga 'yar tsere, Uwani ta dinga bin su tana kiran sunansu. Duk wanda ya ji an ambaci sunansa sai ya sake manna a guje, ita kuma Uwani ba ta yi ihu don ta tsora ta su ba, ta yi ihu ne domin ta ce musu dambarwar da suke yi ta yi yawa ba girmansu ba ne. Su kuma a nasu ganin sun yi tsammanin ko mutanen jikin Uwani ne suka sake dawowa suke kiran sunayensu.
Uwani kan motar Saminu ta hau ta zauna don yunwa ta fara cin ta, ganin haka ya sa Saminu ya fakaice ta ya zare sakatar gidan ya fita a guje. Salim da Shukra na ganin haka suma suka fice Shukra daga ita sai hijabin sallah har ƙasa, ta ciki kuwa wata 'yar figigiyar rigar bacci ce a jikinta. Uwani na zaune ta hango Gali na hangenta ta windo, ta zaro masa idanu tana wani ƙambare hannu. Da sauri ya sauke labule cikin tashin hankali.
Miƙewa Uwani ta yi ta koma cikin gida, ta buɗe firji ta ɗauko kaza duk ta yi ƙanƙara. Kayan miya ta ɗan jajjaga, ta tsoma kasar a cikin ruwa bayan ƙanƙarar ta narke ta yayyyanka ta ɗora farfesu. Ƙwai ta hango a kutchen ta ɗebo guda goma tana sakin murmushi, gabaɗaya ta fashe ta soya shi. Ta ɗora ruwan tea ɗan kaɗan daidai cikinta. Kafin wani lokaci Uwani ta haɗa kwanuka sun kusa biyar a gabanta, sai da ta je ta saka wa ƙofar sakata sannan ta bararraje tana faɗin.
"Shegiya aunty Shukra dama tana da wannan kayan daɗin jiya ta bar ni da shinkafa, wannan gadon mugun hali da kika yi a wurin Mami dai ba ki gaji abin arziƙi ba. " Uwani ta yi maganar tana zuge cinyar kaza a bakinta, lumshe ido ta yi jin daɗi ya ratsa ta ta ce. "Yoo ai dama abinka da cikin mutumin ƙauye, dole na tuna Kura na ɗebi banza son raina. Tun da dama an ce waman taraka bati siddan, wanda ya ga ba ti ya ƙyale wahuwa jahilun shi jahili ne." Uwani tana cin abinci tana surutu sai ga shi kaɗan ta rage, ta ja gefe tana gyasa. Ɗaga can ta hangi A/C, hannu ta sa ta latsa ta ce. "A dole mu murji banza tun da babu a house. Allah Ya dai ya hore wa Daddy muma ya saka mana A/C ko ma ƙara jin daɗin duniya." Uwani na cikin surutu bacci ya yi awon gaba da ita.
Fuska É—auke da damuwa Daddy ya dubi Jafar ya ce. "Wacce irin muhimmiyar magana gare ka?" Jafar ya ce.
"Jiya da daddare aka saki list na P-SKEEPING to sunana yana ciki za a yi refferel ɗinmu zuwa ƙasar Sudan, abin da ya kawo ni zan je Bompai akwai form ɗin da zan cike na yi submitting a can. Jirgi muka biyo ni DC Musa Jobe, shi ya sa ma ban kira ba." Shiru Daddy ya yi sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Shi kenan Allah Ya bada sa'a ya tsare ku a duk inda kuke." Jafar ya lura da sanyin jikin mahaifinsa don haka ya saki murmushi ya ce. "Ai ba daɗewa za mu yi ba Daddy, ina jin bai fi shekara ɗaya zuwa ɗaya da rabi ba." Daddy zai yi magana Dada ta katse shi da cewar.
"Wai Jafaru za a kai Sudan aiki? Magana ta gaskiya babu inda za shi, kai Mamman ba ka jin labarin kashe-kashen da ake yi. Maza kira mini shugaban 'yan sandan na duk duniya wallahi sai na sa ya sallami Jafaru daga aiki." Gudun kada Dada ta ja maganar ya sa Baba Mustafa ya ce. "Yanzu dai bari mu gama da wannan matsalar sai a ji da ta Jafar ko Dada?" Dada ta kalli Mami da ke sunkuye ta ce, "Duniya da Lahira dai Jafaru ba zai ga matsala ba, Saratu da Lado dai sune a cikin matsala dumu-dumu."
Malam ne ya yi gyaran murya sai ya tambayi Malam Harisu a yaushe ne zai mayar da su Lado yadda suke, Malam Harisu ya ce.
"Shi kam Lado a daren yau ma zai koma yadda yake, wato cikakken namiji. Ita kuwa Saratu sai dai ta yi zaman jiran tsattsafowar gashi. Don ina kwashe mata gashin kanta Zuwaira jikata ta ƙone shi. Saboda haka sai ta jira zai tsattsafo a hankali." Ya nuna Mami yana ci gaba da faɗin, " Kuma daga yau ki daina saka hassada, baƙinciki ko ƙyashi a kan abin da wani yake da shi. Idan ba haka ba kuma watarana sai kin kai kanki wurin da za ki kashe kanki, domin kowa kika gani a duniya da arziƙin da Allah Ya ƙaddari zai samu. Wani ba ya taɓa yi wa wani arziƙi don haka ki cire wannan baƙin ƙadarin na zuciyarki, abu na gaba da zan faɗa miki kuma ki samu mai kiwon ki nemi yafiyarta idan ba haka ba ki tafi da haƙƙinta." Shiru wurin ya ɗauka, kan Jafar ya ɗaure yana mamakin kalaman Lado, sai dai ganin sauyin hallitar Lado ba ƙaramin mamaki ya ba shi ba. A ɓangare ɗaya ya sake mamakin dalilin da zai sa Lado ya faɗa wa mahaifiyarsa maganganu mafara daɗi haka. Mami shiru ta yi tana gyaɗa kai, sai dai har a ranta ba ta jin za ta iya samun Uwani ta nemi yafiyar ta, don tsanarta tana nan a zuciyarta ba ta sauya ba. Malam mai Baƙara ne ya yi wa Malam Harisu godiya sannan suka yi sallama, Malam Harisu ya dubi Dada ya ce. "Fillo to sai yaushe zan sake kawo miki ziyara?" Dada ta waro ido waje ta ce. "A'a Malam Harisu zumunci kam wanda ya haɗa mu ai ya raba ko? Ni dai sai dai in ce Allah ya bada ladan wanda aka yi a baya." Mutanen wurin suka saka murmushi don kowa ya ji yadda Dada ke magana ya san a tsorace take. Ba a ɗauki lokaci ba Malam Harisu ya yi musu sallama, lokaci ɗaya Lado ya faɗi yana wata irin atishawa.
"Daddy wai me yake faruwa ne?" Jafar ya tambaya.
"Ga mahaifiyarka nan ita ya kamata ka tambaya, tun da har yanzu ta gagara gane Annabi ya faku." Daddy ya faÉ—a cikin zafin rai.
Dada ta taɓo Jafar ta ce.
"Yoo Jafaru yau dai na ga ƙarshen Saratu, ashe Saratu ce take sa ake kashewa Uwani dabbobinta." Nan take Dada ta zayyane wa Jafar abin da ya faru, ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Ya furzar da iska mai zafi a hankali ya ce. "Allah Ya kyauta."