Sashe 66
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke tsaya Rakiya ni ma fa ba tsoronki nake yi ba, an ƙi a gaya miki yana da matar ke kin biyo ta sigar da za a faɗa miki hakan ne? Jafar ɗana ne ko yanzu na so ya sauwaƙe wa Safna sai ya sake ta, Allah na tuba ma ban da ƙaddara ina ni ina haɗa zuri'a da ke..."
"Iyeee ni kike faɗa wa haka Saratu? Wallahi kin yi da 'yar halak. Ni ban ce ƙaddara ce ta sa 'yata auran ƙaramin ma'aikaci kamar ɗan sanda ba sai ke? Kin san dai duk tsiya koda girgiza kurna ta fi magarya, nesa ba kusa ba Safna ba ajin Jafar ba ce. Don ma jaraba irin ta ɗan yau da ka haife shi ba ka haifi halinsa ba, wallahi Saratu da ni kike zancan kuma duk wata dukiya da kika san na damƙa miki ki dawo mini da abata, tun da ba ƙira babu abin da zai ci gawayi." Jin kalaman Hajiyan Safna na ƙarshe ya nemi ɗaga wa Mami hankali, don ta san ba ta da kafar da za ta biya ta maƙudan kuɗi da ta dinga karɓa a wurin Hajiyan Safna, koda kuwa tana gidan Daddy ne ballantana da a yanzu babu wasu kyawawan kuɗi da suke shigo mata.
"Haba Hajiya wannan fa ba wani abin É—aga hankali ba ne..."
"Saratu kada ki raina mini hankali, kin san dai ni ba sa'ar ƙawancenki ba ce ko? Zumuncin yara ne ya haɗa mu kuma ya raba don haka babu wata magana da za ki faɗa mini a yanzu." Daga haka Hajiyan Safna ta katse wayarta, Mami ta yi mata kiran duniya ta ƙi ta ɗauka. Lokaci ɗaya damuwa ta cunkushe kwanyar Mami, nadamar kwaɗayi da son zuciyar da ta bi ya mamaye ta. Jiki a sanyaye kamar akuyar da ta bi ta mahauta ta koma cikin su Aunty ta zauna, zamanta babu jimawa Dada da Baba Mustafa suka ƙarasa cikin asibitin, a wulaƙance Dada ke bin Mami da kallo don tun da ta ji abin da ya faru ta ɗora laifi a kan Mami.
"Saratu me kike zo yi wurin jikata kuma? Ina 'yar so ɗin ai na ɗauka za ki bi ta a rufe ku tare?" Dada ta furta cike da takaici. Shiru Mami ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa, Dada ta wuce tana sakin tsaki. Jafar ne ya fito ya miƙa mata jaririn Dada ta karɓa tana zuba wata kabbara da har sai da ta bawa Nurse ɗin da ke kai kawo a wurin dariya.
"Mamman maza kira mini Maryama na shaida mata ta yi ango." Daddy ya yi murmushi ya ce. "Wallahi na kira ta Dada amma kin san Maryama da kunya ce wa ta yi tun da muna wurin shi kenan." Dada ta riƙe haba sannan ya miƙa masa wayarta ta sa ya kira mata ita, Sai da suka gaisa Maryama ta yi wa Dada barka sannan Dada ta fara yi mata faɗa. Da ƙyar dai Innar Uwani ta amince za ta zo washegari ta duba jikin Uwani.
Zuri'ar gidan Mai shanu ba su suka bar cikin asibitin ba sai kusan karfe goma É—aya na dare, Aunty ce ta zauna a wurin Uwani ai kuwa kafin Jafar ya yarda sai da Daddy ya yi masa fata-fata. Saboda cewa ya yi shi zai zauna ya kula da ita, ko da ya koma gida hotuna da videos É—in jaririn ya dinga kallo cikin farinciki.
Tun bayan tafiyar su Uwani asibiti wasu yaran Jafar suka wuce da Safna can Bompai, kuma koda suka wuce da ita babu ɗigon nadama a tattare da ita. Cike da shagwaɓa ta kira Mami da Daddynta ta sanar da su abin da yake faruwa, Mami ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Daddy ne ma ya rife Safna da faɗan dukan da ta yi wa Uwani da ciki.
Waya Daddy ya É—auka ya kira wani babban ma'aikacin ÆŠan sanda domin a sakar masa 'ya, tashin farko aka tabbatar masa da ba shi da ikon da zai sa a sake ta tun da zarginta da ake da laifi kuma kai tsaye Safna ta amsa laifinta. Sai dai idan har zai bari zuwa washegari ya je ya yi belinta.
Kuma abin da ya sake ɓata ran 'yan sandan bai wuce yadda Safna ta dinga iƙirarin mahaifinta zai iya tuɓe ma'aikatan da suka kai ta can babbar Hedikwar hukumar 'yan sandan ba.
Mami da kanta ta sa Jafar ya yi mata jagora har zuwa wurin Safna washegari, saboda furucin maifiyarta ya ɗaga hankalin Mami. Sam bai so hakan ba don dai Mami ta matsa masa amma ko sunanta ya tuna ransa ɓaci yake yi.
Ta jikin ƙarfen cell ɗin Mami ta leƙa fuska ɗauke da damuwa ta ce, "Sannu Safna!" A wulaƙance Safna ta dube ta sannan ta ce.
"Me ya kawo ki wurina? Ki adana kalamanki Malama domin komai ya faru ke ce sila, tun da ke kika munafurce mu ni da mahaifiyata."
"Ba ki da hankali mahaifiyata kike faÉ—a wa haka?" Jafar ya faÉ—a a tsawace.
"Na faÉ—a mata, munafiki azzalumi maha'inci, mayaudari."
Safna ta furta cike da tsiwa. Jafar zai sake magana Mami ta dakatar da shi ranta a ɓace, suna na shirin fita sai ga Hajiyar Safna ta ƙarasa ita da wani ƙanin Daddy kasancewar mahaifin Safna ba ya ƙasar.
Sai da Hajiyan Safna ta ƙare wa Mami zagin tsamar nama sannan suka ƙarasa ciki, suka yi duk cike-ciken da za su yi sannan aka ba su belin Safna. Ko da suka fito Jafar da Mami na shirin tafiya Safna da mahaifiyarta suka sake ɗorawa da wani zagin, a wannan karon ran Jafar ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Hajiyanta na shirin tasa ta a gaba su wuce gida Jafar ya miƙa mata takardar saki.
Duk wani rashin mutumcin da ke kan Safna a daidai wannan lokacin sai da ya sauka, sakamakon ido biyu d ta yi da abin da yake rubuce. Jiki na rawa zuciyarta na bugawa ta dube shi.
"Ni ka saka Jafar?"
Jafar bai tanka wa Safna ba ya buÉ—e wa Mami mota ta shiga, shi ma yana shiga ya tashi motar ya fice daga cikin Hedikwatar zuciyarsa na zafi.
Ganin haka ya sa wasu tagwayen hawaye suka fara bin fuskar Safna, Mummynta ce ta rungume ta tana share mata hawaye sannan ta ƙarfafa mata gwiwa suka wuce gida.
Kwanan Uwani uku a asibiti aka sallame ta saboda jikinta ya yi kyau, kai tsaye Dada ta ce za ta wuce da Uwani wurinta a nan kuma Jafar ya kafe kai da fata a kan ba zai bar matarsa ta bi Dada ba. Sai da Daddy ya yi masa da gaske sannan ya amince, ranar kuwa da aka mayar da Uwani Kura shi ma Jafar a cikin gidan ya kwana, don gani yake idan ya tafi kamar Uwani za ta sake guje masa.
Mami da kanta ta kira Daddy ta sanar da shi maganar sakin Safna, don ta samu a yanzu Daddy na sauraronta idan ta kira shi a waya. Ran Daddy ya ɓaci matuƙa, kuma a nan take ya kira Jafar don ya ji daga bakinsa.
Ba ƙaramar kulawa Uwani take samu a wurin Dada ba, haka daga ɓangaren Jafar wani abin da yake yi musu ita da babyn har kunya take ci. Sunan mahaifin Uwani aka saka masa don haka suke kiransa da Hibban, hankalin Jafar ba ƙaramin kwanciya ya yi ba ganin Uwani na zaune daram a wurin Dada. Abu ɗaya ne yake damunsa da Dada korarsa da take yi da zarar ya shiga wurin matarsa, sai ta dinga ce masa miji ba ya zuwa wurin mace idan tana jego sai dai kallo daga nesa.
Ranar da Uwani ta cika kwana goma da haihuwa Jafar ne ya shiga É—akin a lokacin Dada ba ta nan, a zaune ya samu Uwani ta gama shayar da Hibban. A kusa da ita ya zauna bayan ta amsa sallamarsa ta furta.
"Ina wuni Nur?" Jafar ya shagwaɓe yana faɗin.
"Ba zan amsa ba! Jidda yanzu biyewa Dada za ki yi ta dinga hana ni ganinki ina jin ɗuminku?" Shiru Uwani ta yi tana murza hannunta don ita kanta idan ta ce ba ta yi kewar mijinta ba ta yi ƙarya.
Janyo Uwani ya yi jikinsa cike da shauƙin so da ƙauna, ajiyar zuciya Jafar ya sauke yana jin ƙaunarta na fusgarsa, sake janyo ta ya yi ya fara yi mata raɗa a kunne haɗe da sakar mata kisses.
Lumshe ido Uwani ta yi tana jin ƙaunar Jafar a ranta, suna nan a haka suka ji motsin Dada. Da sauri Uwani ta fara kiciniyar ƙwace kanta cikin jin kunya ta furta.
"Ya Jafar Dada za ta shigo!" Idon Jafar a lumshe ya furta.
"Zunubi na aikata ko me?" Dada na ƙarasawa wurin ƙofa ta fara hasko su da touchlight tana faɗin.
"Wai ni motsin me nake ji a cikin É—akin nan ne? Abu kamar munafurci har da sauke labule su waye a ciki?"
A wannan karon ma Uwani ta so ƙwace kanta Jafar ya matse ta, Dada na shiga ɗakin ta ƙanƙance ido ganin Uwani rungume a jikin Jafar ya sa ta wurgar da touchlight ɗin hannunta tana rafka salati.
Jafar ya gimtse daryarsa ya yi kamar bai ga Dada ba ya É—ago Uwani ya haÉ—e bakinsu wuri É—aya, idonsa a lumshe ya É—ago yana faÉ—in.
"Jiddana kin ga tun da Dada hana ni zuwa take yi wurinki a ɓoye ba sai na dinga ɗaukanki muna fita daga gidan ba. Ni fa na yi kewarki Jiddana, kuma na lura Dada so take ta wargaza sunnar Ma'aiki." Jafar ya furta cikin kwaikwayon kalaman Dada, ya ɗan waigo ya ga yadda Dada ta dafe ƙirji hannuwa bibbiyu ya sake gimtse dariyarsa ya cigaba da cewa.
"A gaskiya ba zan iya jira har sai kin yi kwana arba'in za ki koma wurina ba. Idan kuwa Dada ta tsaurara tsaro sai ki haife mata ƙanin Hibban a gabanta." Dada na jin haka sai kawai ta fashe da kuka ta ce.
"Jafaru dama abin da yake kawo ka É—akina kenan? Munafiki algungumi ashe huÉ—ubar tsiya kake yi 'yar mutane shi ya sa idan na kore ka sai Uwani ta É—auki fushi da gaba da ni."