Sashe 22
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hakan ma ya yi idan kana ganin ya fi a wurinka, amma ka sani a waɗannan kwanakin naka duk inda za ka saka ƙafa sai dai ka tafi da Uwani. Ba zai yiwu kwana biyu da yin aure ka tsallake yarinya ka bar ta a nan ba, sannan kuma wannan matsalar da ke faruwa zan nemar muku magani idan daga kai ne ko kuma daga ita ne." Wani malolon ɓacin rai ya tokare Jafar, ya haɗiyi yawu mai ɗaci ya furta.
"Shi kenan Daddy." Daga haka Daddy ya sake yi musu nasiha sannan ya sallame su.
Jafar na fita ya kira Amir a waya bayan sun gaisa yake ce masa ga shi nan zuwa, a lokacin da ya je Amir na zaune da Laptop a gabansa yana aikin tracking. Kamar mai ciwon haƙori haka Jafar ya yi sallama ciki-ciki ya zauna a bakin katifa.
"Ango ka sha mai, kai ka ga yadda saman hancinka yake ƙyalli. Shegen kaya kana so kana kai wa kasuwa." Amir ya yi maganar yana dariyar shaƙiyanci.
"Ba na son iskanci ni ba wannan ne ya kawo ni ba." Jafar ya furta rai a ɓace. Da ido Amir ya bi shi da kallo Jafar ya ci gaba da cewa.
"Zuwa na yi ka ba ni aron É—aki na kamar sati biyu."
"Ni kuma na je ina? Ka san dai ai hutu muka dawo ko?" Jafar ya dage kai da hannuwa biyu cikin damuwa, Amir ya sanarwa yadda suka yi da Daddy sannan ya É—ora da cewa.
"Allah Ya sani ba zan iya tafiya Lagos da Uwani ba, haba kawai sai na fara nuna ta na ce ga matata. Kuma ka san duk yadda zan ɓoye wa Safna na yi aure matuƙar na je da Uwani sai asirina ya tonu." Jafar ya sauke ajiyar zuciya ransa na ɗaci ya ci gaba da magana.
"Ga Safna na shirin ɓallo mini ruwa ita ma." Nan ya kwashe hirar da suka yi da Safna, ya ɗora da cewa.
"Abokina don Allah ka ba ni mafita komai ya cushe mini, al'amura duka sun kwaɓe mini."
Shiru Amir ya yi yana nazari, da sauri ya É—ago ya ce. "Na samu mafita. Yanzu dai da farko ka É—auki Uwani ka kama muku hotel, ba ka ce makaranta za a saka ta ba. Idan kuka cinye wannan hutun ka ga ai sai dai ka dinga zuwa ka na dawowa, ita kuma Safna idan har ba jagwal kake son haÉ—a wa kanka ba to ka yi mata dabara har zuwa nan da bayan kwana biyu, idan ya so kafin nan matsalar Uwani ta ragu sai ka ji da waccan matsalar." Jim Jafar ya yi jiki a sanyaye ya ce. "Sai kuma kawai na koma rayuwar hotel kamar wani É—an iska."
"Wa ya ce maka 'yan iska ne kaɗai ke rayuwar hotel? Masaukin baƙi ne fa. Kuma idan ma iskancin za ka yi ai matarka ka ɗauka ko?" Amir ya yi maganar cikin zolaya. Sun ɗan taɓa hira sannan Jafar ya yi masa sallama ya wuce gida.
Daren wannan ranar a ɓangaren Mami suka kwana, Daddy ya sa aka buɗe musu ɗakin Dada suka shiga ciki. Fes yake babu ƙura a ciki, wannan karon Jafar bai kori Uwani daga kan gadon ba saboda a matuƙar tsorace yake. Kowannensu ya juya bayansa ya kwanta, bini-bini Uwani idan za ta gyara kwanciya sai ta ƙara tamke kai da ɗan kwali.
Kimanin ƙarfe tara na safe Uwani da Jafar suka shirya kowannensa ɗauke da jaka, Uwani kayanta ta ɗiba ta saka a akwati kamar yadda ya gaya mata. Mami da ta je yi wa Jafar sallama sai jaddada masa take ya kula da kansa tamkar wani mace, shi maganar tata har kunya ma take ba shi. Daddy ne ya ɗauke su a mota ya nufi tashar sabon gari da su, Jafar yana gani bai faɗa masa cewar ya fasa zuwa Lagos ba don nauyi yake ji ya ce masa hotel zai kama musu. Sai da ya tabbatar da motar Daddy ta yi nisa da tasha ya dubi Uwani ya ce.
"Sai ki É—auko jakarki."
Ba musu Uwani ta fara jan jaka har suka samu mai adaidaita sahu, Jafar ya ce masa ya kai su Light Hotel da ke Zoo road.
"Ina kuma za mu?" Uwani ta watsa masa tambaya.
"Sayar da ke zan yi. Wallahi idan muka je kika yi mini ƙauyanci sai jikinki ya faɗa miki." Uwani ta ja bakinta ta yi gum tana kalle-kallen titi. Har cikin harabar hotel ɗin ya shigar da su, nan Uwani ta saki baki tana kalle-kalle don wani lokacin sai Jafar ya yi gaba zai waiga ya ƙwalla mata kira, reception ya tsaya ya cike duk abin da ya dace. Aka ba shi key ya tasa Uwani a gaba da ta saki ba ki tana kallon wurin.
"Don Allah ina ne nan ka kawo ni kamar Dubai da nake gani a TV?" Jin tambayar da Uwani ta yi masa ga kuma mutane na kallonsu ya sa ya ce. "Eh Dubai ce." Cikin lifter suka shiga Uwani ta ji wani irin zuuuuummmm A firgice ta ƙanƙame Jafar ta saki ihu, ƙirjinta sai bugawa yake. Sai da suka tsaya sannan Uwani ta ɗan ɗago da kanta amma har lokacin jikinta bai daina karkarwa ba.
"Malama sake ni."
Jafar ya faɗa yana yakice Uwani. Kamar sabuwar munafuka haka Uwani ta dinga raba idanu kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci a tsorace take. Buɗe ɗakin ya yi suka shiga, a gajiye ya zube a kujera Uwani ta tashi ta fara leƙa ɗakin.
"Don Allah ina muka zo Ya Jafar?"
"Light Hotel." Jafar ya amsa mata a taƙaice.
A zabure Uwani ta miƙe tsaye jiki na rawa ta ce, "Wallahi ba zan kwana Otal ba salon haka kawai a dinga ce mini 'yar iska." Uwani ta dubi Jafar a yamutse ta ce.
"Ya Jafar ina maka kallon mutumci ashe kai ma kana cikin sahun sababbin 'yan iska ashe ban sani ba..." Jafar ya bige wa Uwani baki, cikin jin zafi ta sa hannu ta dafe bakin ta furta.
"Wallahi ban yafe ba..." Ba ta ƙarasa magana ya sake bige bakinta. Uwani ta zauna a gefen gado tana watsa masa harara. Wayarsa ya zaro ya fara dannawa, Uwani ta ci gaba da zama cikin gundura don ita tsarin wurin sam bai yi mata ba.
"Ni fa yunwa nake ji." Uwani ta yi maganar, Jafar ya yi kamar bai ji ba. Sai da ta maimaita sau uku amma ko ƙurar ta bai kalla ba, ta tashi ta leƙa ta window a nan ta hango mutane na zirga-zirga a farfajiyar wurin.
"Bawan Allah ka taimaka mini yunwa nake ji." Uwani ta ƙwalla wa wani mutum kira da ta gan shi ya wuce da take away a hannu.
"Mai farar rigar nan don Allah ka taimaka mini..."
Cikin zafin nama Jafar ya ƙarasa ya fisgo Uwani. Da ƙarfi ya wurga ta kan gado yana huci ya ce. "Ke wacce irin mahaukaciya ce ne? Wallahi kika nemi ki tara mini jama'a sai na zane miki jikinki."
"Ba na gaya maka yunwa nake ji ba? Wallahi ka kiyayi hukuncin Ubangiji atoh, a kan mage ma wata ta shiga wutar jahannama, ka san ni ma ka kashe ni da yunwa duk gatanka babu mai hanaka shiga Hawiya." Jafar ya yi yunƙurin kai mata duka da sauri Uwani ta zille tana dariya, tana gani ya ɗauki waya ya kira ita dai ta ji yana turanci amma ba ta san abin da yake faɗa ba. Bayan awa ɗaya sai ji ta yi an ƙwanƙwaso musu ƙofa, Jafar ya karɓi abincin ya dire. Plate ɗinsa ya ɗauka bai tanka wa matai ba, ganin haka ya sa ita ma ta sauka ta ɗauka ta fara cin abinci. Bayan ta gama babu jimawa aka kira sallar Azahar, tana idarwa ta ɓingire a akan dadduma bacci ya yi gaba da ita.
Tun da Jafar ya fita sallar Azahar bai dawo da wuri ba, kusan sallar La'asar Uwani ta farka shi ma sanyin AC ne ya dame ta. Banɗaki ta shiga yin alwala tana ta jinjina lamarin ƙayatuwar banɗakin da kuma nasu ɗakinsu, bayan ta idar da sallah atamfar jikinta ta sauya ta ɗauko wasu riga da wando baƙaƙe ta saka. Sai wata farar hula da ta ɗora a kanta, ta saka hijabinta ƙarami. Jin zaman ta yi ya gundure ta don haka ta buɗe ƙofar a hankali tana leƙe-leƙe. Sai a lokacin da lura da fasalin ɗakunan duk suna kallon juna sai dai kowacce ƙofa a datse take. Tafiya ta fara yi tana kalle-kalle ba ta yi aune ba sai ji ta yi garam ƙofar ɗakin ta datse, Uwani ba ta wani damu ba ta ci gaba da tafiya har ta fita wurin wata baranda ta hangi step ɗin bene. Takawa ta fara yi a hankali har ta sauka sai ganinta ta yi ta sauka can farfajiyar wurin da ta hango mutane na kai-kawo. A kan ɗaya daga cikin kujerun harabar wurin ta zauna, a gefe ɗaya kuma swimming fool ne tsirarun mutane sun zauna suna saka ƙafarsu a cikin. Abin ba ƙaramin birge Uwani ya yi ba, abu ɗaya ne ya takurata ganin yadda wani Alhaji da ke gefenta ya zuba mata idanu da sun haɗa ido sai ya sakar mata murmushi, ko ya kashe mata ido ɗaya. Kiransa ta ji an yi a waya ya ɗauka yana barin harabar wurin. Babu jimawa ita ma ta tashi ta nufi hanyar ƙafar benen da ta sauko, wata hanya ta bi wacce take ganin kamar hanyar ɗakinsu ce. Amma sai ta ga ta gagara gane ainihin ɗakinsu, wata ƙofa ta gani a buɗe. Ta ga yanayin wurin ya yi mata kama da ɗakinsu da sauri ta tura ƙofar, turus ta yi tana kallon mutumin.
Mutumin É—azu da ta ga an kira a waya ne, ya washe mata baki yana faÉ—in.
"Ranki shi daÉ—e ke kaÉ—ai ce?" Uwani ta yi saurin kawar da kai gefe don jibgegen mutumin daga shi sai gajeren wando, ya É—ora towel a kafaÉ—arsa da alama wanka zai shiga.