Sashe 33
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai dama haka kake da kyau Ya Jafar ban sani ba, wallahi ba ka taɓa yin gayu irin na yau ba." Jafar na jin haka ɗan tsuke fuska, Uwani ta taɓe baki ta furta.
"Kai fa dama matsalata da kai baƙin hali, ina laifi don an yabe ka. Amma kai komai a ƙunci yake a wurinka, shi ya sa kullin fuskarka kamar fate..." Uwani ba ta gama magana ba Jafar ya fusgi hannunta ya zaunar da ita a gefen gado, ya ɗora ƙafarsa a gefenta fuska a haɗe ya ce. "Rashin kunya za ki yi mini?" Uwani ta murguɗa baki tana ɗauke kai gefe. Kunnenta ya riƙo da hannunsa ya murɗe da ƙarfi kamar zai tsinke mata su, ƙara ta ƙwalla tana runtse ido. Jafar ya sake haɗe fuska sannan ya fara magana.
"Ki nutsu ki saurari abin da zan gaya miki!" Ganin yadda Jafar ya birkice mata lokaci ɗaya ya sa Uwani ta shiga taitayinta, riƙon kunnen da ya yi mata ya sa ta shiga haɗa gumi saboda azaba.
"Yau su Safna za su zo gidan nan, wallahi-wallahi ko da wasa na kuskura na ga kin nuna wata alaƙa a tsakanina da ke sai na karairaya ki. Ke daga yau kin ji na rantse miki matuƙar kika sake nuna wa wani ma ni mijinki ne wallahi sai na bi dare na fita da ke daga gidan nan, na kai ki can dokar daji na harbe ki na wurgar da gawarki." Tuni cikin Uwani ya kaɗa jin an ambaci bindiga, a tsawace Jafar ya furta. "Ba za ki amsa mini ba?" Da sauri Uwani ta hau gyaɗa kai tana hawaye, ganin yadda ta tsora ta ya sa Jafar ya ci gaba da cewa. "Ko sunana na ji kin ambata sai na saka bakin bindiga na harbe ki, hanyar jirgi daban ta mota daban don haka ki kama kanki, zama da ke na ɗan lokaci ne don ina shawo kan Dada da Daddy zan sallame ki. Safna ita ce zaɓina ita nake so zan aura saboda ita ce daidai da class ɗina, kin ji me na gaya miki ko?" Uwani cikin kuka ta amsa masa. Sai da Jafar ya gama tsurar da Uwani sannan ya ta shi ya fice daga ɗakin. Zuciyar Uwanu ban da zafi babu abin da take yi, ita kanta ba za ta ce ga dalilin jin zafin zuciyar ba. Amma abin da ya fi tsaye mata a rai wai Safna ita yake so yake ƙauna, ƙwafa ta yi ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta ta koma kan gado ta yi lamo ranta duk babu daɗi.
Jafar na fita kiran Mami ya shigo wayarsa sai da ya shiga motarsa sannan ya É—auka, "Mami..."
"Wai Jafar me kake yi da ba za je É—auko su Hajiya ba?" Mami ta katse shi da sauri.
"Mami kin gan ni a mota yanzu haka fita zan yi." Mami ta saki murmushi ta ce. "Ka yi sauri don kada su yi ta jira jirginsu yanzu haka ya kusa sauka." Jafar ya ba ta amsa har zai katse kiran ta ce, "Maza kuma ka turo mini Uwani É—akina ka ce ina son ganinta yanzun nan." Bayan Jafar ya amsa ya fice daga motar ya koma wurin Uwani, Uwani na ganinsa ta kawar da kai. Shi ma bai kalli inda take ba ya ce.
"Mami na son ganinki a sashen ta yanzun nan." Yana gama maganar ya fice.
Jiki babu ƙwari Uwani ta wuce sashen Mami a falo ta same ta, tana zuwa Shukra ta ja hannunta suka shiga ɗakin Mami. Mami ta bi su a baya tana wurga wa Uwani harara, Uwani na tafe gabanta na faɗuwa har suka shiga ɗakin.
"Don uwarki kiranki na yi in yi miki kashedi, yanzu haka matar da Jafar zai aura ita da mahaifiyarta suna hanya. Wallahi ko da wasa na ga kin yi wani alamu ko kin faɗa wa wani alaƙarki da Jafar idan na riƙe ki sai na kusa kashe ki, kin san dai abin da ya faru a kan kuɗin Daddy da na sa Shukra ta kai ɗakinki ta ɓoye aka gansu a wurinki ko? Wallahi a wannan karon kika ɓata mini bajat sai na laƙa miki sharrin da za a ɗaure ki har ƙarshen rayuwarki, kin san zan iya aikata fiye da haka ko?" Da sauri Uwani ta gyaɗa kai tana hawaye, Shukra ta zuba mara ranƙwashi a kai ta ce. "Shegiya baƙa mai baƙar aniya, tun da kika zo gidan nan muke ta haɗuwa da masifa jaka mai ƙashin tsiya..." Shukra ba ta gama magana ba suka ji an turo ƙafar ɗakin da ƙarfi, Dada ta fasa kuka tana faɗin.
"Ke dai Saro kin yi asara wallahi, ashe sharri kika laƙa wa Uwani muka dinga aibanta yarinyar nan? Wallahi dama tun da na hango ku ke da Shukra kun janyo ta ɗaki haka kawai na ji ban yarda da ku ba, Saro tun wuri ki nemi yafiyar yarinyar nan domin kin ɗauki haƙƙinta."Mami da Shukra lokaci ɗaya suka rikice, Mami ta saki murmushin makirci da ta yi wani tunani ta ce. "Yanzu Dada ƙiyayyar da kike yi mini har ta kai ki yi mini sharri, idan na yi wa Uwani sharri wacce riba zan ci." Dada na shirin yin magana suka ji an sheƙa ruwa a banɗaki, wani abu ya sake tsarga wa Mami tana fargabar wanda ke cikin banɗakinta ba tare da ta sani ba. Daddy ne ta turo ƙofar banɗakin ya furta.
"Ribar abin duniyar da kike son cim ma! Wallahi tun ranar da abin ya faru na ji a jikina Uwani ba za ta taɓa ɗaukan maƙudan kuɗi har sama da miliyan biyu ta kai ɗakinta ba, kin kyauta Saratu wallahi ko iya taron ki da ya wargaje miki a gaban mutane jiya ya ishe ki ishara. Haƙƙin ɗan adam abin tsoro ne amma saboda kin tsani yarinya har za ki laƙa mata sata." Mami da Shukra suka yi zuru-zuru, Dada ta share hawayen idonta ta ce. "Wallahi ni kam Saratu tsoro take ba ni kuma tsaf za ta iya kashe mini Uwani, don haka idan na tashi tafiya ƙafata ƙafarta. Jafaru ko shi ne ɗan autan maza Uwani ta gama aurensa." Dada na gama magana ta ja hannun Uwani suka fice daga ɗakin.
A sanyaye Mami ta dubi Daddy ta furta, "Daddyn yara..." A zafafe ya ɗaga mata hannu ya katse ta. "Ba na son jin komai daga gare ki Saratu, duk irin ƙiyayyar da na san kina yi wa yarinyar nan ban taɓa tsammanin ta kai haka. Duk fa a kan Safna kike aikata haka ko? Jafar dai ɗana ne kuma duk duniya babu mai iko shi sama da ni, wallahi-wallahi kin ji na rantse idan ban ga dama ba Jafar ba zai auri Safna ba. Tun da na mallaki hankalin kaina Dada ba ta taɓa ba ni umarni na tsallake ba, amma a wannan karon ko mahaifiyata ba za ta saka ni abin da ban yi niyya ba. Mu zuba ni da ke mu gani idan har tusa na hura wuta." Daddy na gama maganar ya fice a fusace.
Daga Mami har Shukra rasa mai bakin magana aka yi, wannan shi ne tashin hankalin da ba a saka masa rana. Lokaci ɗaya Mami ta fara hawaye, wata irin nadama ta ɗarsar mata don ta tabbata a wannan karon ta kai Daddy maƙurar bango.
"Mami ki daina kuka don Allah, ba na son wani ya fahimci abin da ake ciki. Kin san fa mutane ba sa raina abin magana." Goge hawaye Mami ta yi abin duniya goma da ashirin ya haÉ—e mata.
Dada na shiga É—akinta ta rushe da kuka, nan mutane suka shiga tambayar ba'asi. Tiryan-tiryan Dada ta ba su labarin abin da ya faru, lokaci É—aya suka É—auki salati kowa da irin abin da faÉ—a akan Mami.
Lokacin da Jafar ya isa airport jirgin su Safna tuni ya sauka, kiranta ne ya shigo wayarsa bayan ya ɗaga ya kwatanta mata a wurin da yake. Babu jimawa sai ga Safna ita da Momma sun ƙaraso, kowacce hannunta ɗauke da jaka. Safna sanye take da doguwar rigar abaya, ba ta yi wata kwalliya ba don dama ita tarkacen kwalliya bai dame ta. Har ƙasa ya tsugunna ya gaida Momma sannan ya karɓi jakarta, Safna sai wurga masa kallo take cikin shauƙin so da ƙauna. Ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, bayan Momma ta shiga mota ta gagara haƙuri ta ce.
"Baby ka yi kyau, na ga har wata ƙiba ka yi me ye sirrin?" Ta ƙarasa maganar rana kashe masa ido ɗaya, murmushi ya yi mata yana mata alamun da Momma na mota don haka ya yi saurin shige wa mota ita ma ta buɗe ta shiga tana sakin murmushi.
Lokacin da suka ƙarasa gida Daddy yana gate yana zirga-zirga, Jafar na yin parking ɗin mota bayan da su Momma suka fito ya ƙwala masa kira. Jafar na zuwa wurin Daddy rai a ɓace ya furta.
"A yanzu ba sai anjima ba, ka sanar da mahaifiyar budurwarka ina son ganin ta. Kuma ina son ka shafe duk wani babin soyayyar da kake yi wa Safna daga zuciyarka."
07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅