Sashe 45
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ƙananan 'yan iska ni za ku mayar shegiya da." Fita ta yi daga ɗakin kai tsaye ta wuce kitchen ta buɗe ƙofar, Uwani na ganin Saminu ta ƙwalla ƙara tana faɗin. "Yaya Salim wani ya shigo mana gida, fito-fito wallahi ga shi nan a kitchen. Ko dai ɓarawo ne ma ka ga duk ya sauke mana labulen falo." Saminu da mamaki yake bin Uwani ya ga duk ta wani sauya kamar ba ita ba, yana fitowa ko ya shiga aika wa da Salim harara. Yana son tambayar key don ya buɗe ƙofa ya fita yana jin tsoro. Uwani ta fara tattara kayan falon tana 'yar mita.
"Don Allah wa ya hargitsa É—akin nan bayan jiya da dare tass na gyara shi."
Shukra cikin tausasa murya ta ce. "Uwani bar wannan aikin ɗauko jakarki za mu wuce gida, ni ma da yake jikin na wa babu ƙwari gaban Mami zan koma." Uwani ba ta musa ba ta shiga ɗakinta, ta ɗan jima a ciki har su Shukra sun fara murna Uwani ta leƙo ta ce. "To ai Aunty Shukra na tuna Mami fa dama cewa ta yi na zauna sai kin warke. Haba don gyaran gidan ai ba wani wahala ba ne a wurina." Hawaye ya ciko idanun Shukra ta ce, "A'a gara dai mu je kin ga Salim tafiya zai yi ba daɗi ya bar mu, mu biyu a cikin gida." Uwani ta gyaɗa kai kamar mutuniyar kirki sannan ta shige cikin ɗakin. Tana shiga ta saka sakata, ta faɗa banɗaki ta yi wanka tana fitowa ta faɗa kan katifa ta kwanta. Babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita don har lokacin jikinta ciwo yake yi.
Jiki a sanyaye su Daddy suka koma cikin gida don maganar da Lado ya yi abar dubawa ce, Lado yana tafe ban da zubar da ƙwallah babu abin da yake yi. Suna shiga cikin falon suka samu Mami tana kiciniya ita da ɗankwalinta, saboda tun fitar su Daddy take fama da shi da ta ɗaure sai ta ji kamar an fisge shi ya faɗo ƙasa. Ganin yanayin da Lado ya shiga ya sa jikin Mami ya yi sanyi, a dole ta shige ɗaki gabanta na faɗuwa fargabarta kada Lado ya tona asirinsu mutumcinta ya sake zubewa a idon su Dada. Aunty na ganinsu ta saki murmushi ta ce.
"Hajiya Dada an fasa tafiya? Ai da ma daga zuwanki Dada ko ruwa ba ki sha ba ki ce za ki tafi." Dada ta jinjina kai cike da damuwa ta ce.
"Ina zan tafi Lado da Saratu sun jangwalo mana jagwalgwalon masifa, kai ni kam tun da nake rayuwa na taɓa ganin jafa'i irin wannan?" Aunty ta yi sororo tana mamakin kalaman Dada.
Daddy da kansa ya shiga ɗaki wurin Mami ya ce mata ta fito za su yi magana, tun da Mami ta ji haka jikinta yake karkarwa. A haka ta yi ta maza ta sako hijabinta tana sunne kai ƙasa, don jikinta ya gama ba ta akwai abin da yake faruwa. Zamanta a ɗakin babu jimawa, Daddy ya dubi Lado ya ce ya maimaita abin da ya faɗa dangane da Mami. Lado ya karkace kai ya fara wassafo jawabi tiryan-tiryan tun daga lokacin da aka fara ganin gawarwakin kajin Uwani, har zuwa lokacin da wannan mummunar ƙaddarar ta faɗa kansu. Mami tsumu ta yi cikin sanyin jiki kamar an jiƙa kaza a ruwa, Daddy ya dubi Mami cikin ɓacin rai ya ce.
"Saratu wai yaushe za ki fahimci ɗa da dukiya ba a yi masa mugunta ne? Me ya sa idan kina wani abin tamkar ƙanƙanuwar yarinya? Yanzu wa gari ya waya? A tunaninki idan yarinyar nan ta ji abin da kika aikata raini ba zai shiga tsakaninku ba? Ko kina tunanin idan kika raba ta da kiwon da take yi kin gutsiri wani sashe a cikin rayuwarka." Tun da Daddy ya fara magana uffan Mami ba ta ce ba sai ruwan hawaye da ke zuba daga idonta, tun da ta zo duniya wannan karon ne na farko da ta far jin nadama dangane da abin da take aikatawa Uwani, ana cikin haka Malam mai Baƙara ya kira Daddy ya ce masa yana ƙofar gida.
Daddy ya miƙe kenan zai fita Lado ya hango 'ya'yan bunsurun sun sake ɓullowa ta kusurwar bango, tsalle-tsalle suka fara yi suna dire-dire sannan suka tunkaro shi suna kuka. Daga gefensa ya ji bunsurun nan ya shafo masa ƙirji ya ce. "Lado fa sai dai ka yi haƙuri yanzu ma sun sake dawowa za su sha."
A zabure Lado ya miƙe yana dafe ƙirji yana faɗin, "Don Allah ku taimaka mini wallahi yanzu ma sun zo za su zuƙe ni, wayyo Allah jama'a 'ya'yan bunsuru za su danne ni." Ganin da gaske sun yo kansa ya sa Lado ya yi sufa ya fisgo ƙafar Daddy da ƙarfi, sai ga Daddy ya dawo ta baya daɓar ya faɗi a ƙasa. Lado ya ji 'ya'yan awakin sun sake turmushe shi suna ƙoƙarin kai bakinsu jikinsa, da sauri ya janyo hannun Dada yana karewa a ƙirjinsa. Dada cikin tashin hankali ta zuba kabbara tana kiciniyar tashi daga gefen Lado tana faɗin.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel! Jama'a ku taimake ni zai saka mini hannu a ƙirjin aljanu." Lado da yake ganin ƙarfi da yaji awakin na turmutsa kai cikin ƙirjinsa ya sake warto ɗayan hannun na Dada yana dannewa. Dada ta fashe da kuka hankali a tashe sake cewa.
"Allahu la'ilaha'ilahuwal hayyul ƙayyum! Mammam ku taimaki tsufa da tsohuwa baiwar Allah, don Allah ku agaza mini kada Lado ya sa ni ma su mayar da hi mata-maza." Dada na kuka ta ci gaba da biya Ayatulkursiyyu, lokaci ɗaya Lado ya nemi awaki da bunsurun ya rasa. Yaraf Lado ya faɗi gefe yana sauke ajiyar zuciya, Daddy ya miƙe yana kaɗe riga cike da takaici ya fita shigo da Malam mai Baƙara.
Malam mai baƙara na shiga ya shiga gaisawa su baba Mustafa, har ƙasa ya tsugunna ya gaida Dada sannan ya mayar da kallonsa wurin Lado da ke sunne kai ƙasa. Ƙurawa Lado ido ya yi yana mamakin surarsa duk da kallo ɗaya ya yo masa ya fahimci akwai shafar jinnu a jikinsa. Daddy ne ya kora wa Malam jawabi sannan ya fita ya ɗauro alwala ya sa aka hura garwashi, ƙullin magunguna ya fara fito da su dangin su habbatus sauda. Sai da ya turara a ɗakin sannan ya fara biya karatun Alƙur'ani, a hankali Lado ya fara wata irin karkarwa idanuwansa na niyyar kakkafewa.
"Assalamu alaikum Malam mai Baƙara! Ni sunana Malam Harisu." Wata murya ta furta ta bakin Lado. Malam ya amsa sannan aka sake cewa. "Malam ka fita a wannan yaƙin don girman Allah, saboda alƙawari na ɗaukar wa Mai shanu zan kare zuri'arsa akan kiwace-kiwacen da za su gudanar. Idan har ka ga ban tsoma kaina a ciki ba to faɗan na su sai ya kasance na cikin gida ne, kamar irin abin da ya faru tsakanin Uwar garke da Isuhu." Malam mai Baƙara ya jinjina kai sannan ya ce, "A wane dalili ne kai kuwa ka ɗauki wannan alƙawarin?"
"Saboda na kasance Amini a wurin kakan Uwani wato Mai shanu, mun taɓa haɗuwa a cikin wani baƙin daji da rana tsaka a lokacin yana kiwon shanunsa. Ya yi mini wani taimako da na ji daɗinsa wanda silar haka ne, na ɗaukar masa alƙawarin duk rintsi zan kare zuri'arsa ta fannin kiwace-kiwacansu. Ko a lokacin da aka taɓa kai musu farmaki ba na ƙasar ne ina can yankin ƙasar India, bayan na dawo kuma ɗaya bayan ɗaya sai da na ɗauki mataki a kansu ko shi ban taɓa sanarwa ba sai yau da dalilin faɗar ta kama."
Malam mai Baƙara ya jinjina kai ya ce. "Amma kai musulmi ne?" Ta bakin Lado aka amsa.
"Ni cikakken musulmi ne gaba da baya."
"To amma tun da kai musulmi ne me ya sa za ka cutar da waɗannan bayin Allahn, musulmin ƙwarai ai ba a san shi sa haka ba. Kamata ya yi su da suka aikata ba daidai ba in ma su nemi yafiyar mai awakin ko kuma Ubangiji ya yi musu sakayya." Malam mai baƙara ya jima yana yi masa nasiha sannan Aljani Harisu ya furta. "Tabbas kalamanka sun yi tasiri a kaina, kuma na ji duk wa'azin da ka yi mini. In shaa Allah ba zan sake aikata haka ba, amma wallahi da ka bar ni da su wallahi da sai dai su ƙare rayuwarsu a haka." Malam mai Baƙara ya yi murmushi ya ce. "A'a Dattijio Harisu ba za fa a yi haka ba, idan ka bar Lado a haka wacce macen ce za ta aure shi. Ka ga ai an cuci samartaka." Duk da a lokacin mutanen ɗakin na cikin alhini sai da suka murmusa. Dada ta yi kasaƙe sannan ta ce.
"Wai Malam Harisu dai da na sani a shekarun baya mai zuwa wurin Malam?" Malam Harisu ya ce.
"Ni ne dai Fillo ashe ba ki manta ni ba." Dada ta zaro ido waje ta ce, "Yanzu saboda Allah dama Harisu duk nono da man shanun da ka dinga kawo mini abincin aljanu nake sha ban sani ba?" Malam Harisu ya yi dariya ya ce. "Fillo ai ba za ki iya cin abincinmu ba, nono da man shanu kuma sayensu nake idan zan kawo wa maigidanki ziyara na kawo masa." Dada ta yi jim tana nazari sannan ta ce. "Kuma Malam ya san kai ba mutum ba ne kafin ya rasu?" Malam Harisu ya ce.
"Tabbas na sanar da shi, kuma har ziyara na taɓa kai shi cikin dangina. Kuma ni na ce masa kada ya sanar da ke asalin wane ne ni, domin a halitta da ɗan adam mata akwai ku da tsoro." Dada ta yi shiru tana nazartar irin zaman mutumcin da suka yi da Malam Harisu, wani sabon tsoro ya shige ta don haka ta ja baki ta yi shiru.