← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 71

Sashe 13

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da aka idar da sallar Isha'i a masallacin gidan marigayi Mai shanu har mutane za su fara watsewa, malam Liman ya yi shelar akwai ɗaurin aure da za a yi. Nan take aka gabatar da waliyai daga kowanne ɓangare, aka ajiye sadaki dubu ɗari da hamsin da alewar ɗaurin aure. Jafar da ke can kusurwar bango da mamaki yake bin malam Liman, a zuciyarsa yake ayyana wanne irin aure ne za a ce za a ɗaura shi da daddare? Ganin su Daddy a gaba-gaba ya sa gabansa ya yi mummunan faɗuwa, ya yi saurin kawar da tunanin da ya faɗo masa a rai har yana neman tsari da shi.
Wayarsa ya ɗauko ya fara latsawa, saƙon Safna ya ci karo da shi yana shirin buɗewa ya ji Liman ya furta.

"Ga waliyin Jafaru ga waliyin Hauwa kulu an kawo sadaki dubu ɗari da hamsin lakadan ba ajalan ba. A bisa duka shaidun da ake buƙata sun kammala kowa ya shaida an ɗaura auren Jafar Mamman mai shanu da amaryarsa Hauwa kulu Umaru mai shanu, a kan sadaki naira dubu ɗari da hamsin lakadan ba ajalan ba." Daga haka ya fara rattabo addu'o'i ana ta saka albarka. Baba Isuhu ya ƙarasa yana yi wa Jafar Allah sanya alheri, ganin shi ne angon waɗanda ba su san shi ba suka ƙarasa suna masa fatan alheri. Tamkar butum-butumi haka Jafar ya ƙame a wuri ɗaya, ta cikin hayaniyar mutane ya sulale kai tsaye ya wuce gida. Na Madina sai ƙwala masa kira yake amma ya yi banza da shi, Jafar kai tsaye ɗakinsa ya shige ya datse yana kai wa da kawowa.

"Ga alewa da dabinon É—aurin auren É—anki, ki saka albarka domin addu'arki na da muhimmanci a wurinsu. Bayan mun idar da sallah aka É—aura auren Jafar da Uwani."
Daddy ya furta wa Mami bayan ya shiga gida. A fusace Mami ta suri ledar dabinon ta yi wulli da ita, cikin ɓacin rai ta furta.

"Daddyn Jafar yanzu tozarcin da za ka yi mini kenan? Wannan tsinannan auren zan saka wa albarka? Wallahi a daren nan sai Jafar ya saki Uwani." Murmushin takaici Daddy ya yi ya ce.
"Na riga da na gama magana da Jafar, ki sani idan kika tilasta shi ya saki yarinyar nan wallahi sai na sauke miki igiyar aurenki uku daga kaina." Baki sake Mami ta bi Daddy da ya wuce ɗakinsa da kallo, saboda takaici sai kawai ta fashe da kuka. Su Shukra ne suka ƙarasa suka fara lallashinta.

Cikin ƙanƙanin lokaci garin ya ɗauka 'Yar ƙashin gwiwa ta yi aure, wasu masu ƙarfin halin har gidan suka shiga yin tsegumi. Uwani duk wainar da ake toyawa ba ta sani ba sai daga baya Dada take sanar da ita, babu wani abu da ya ɗaga mata hankali abin da ya fi damunta ciwon jikin dukan da su Mami suka yi mata, wanda ta ci alwashin gabaɗaya za ta ladaftar da su ɗaya bayan ɗaya.

Washegari ne ya kama sunan gidan Baba Isuhu sai dai tsamin jikin da Uwani take fama da shi ya hana ta walwala, don ta ci burin ko yaya ne ta tarwatsa 'yan taron suna.

Yamma liƙis Uwani da ƙawarta Kubra na tafe suna hira Kubra ta ce.
"Oh 'Yar ƙashin gwiwa yanzu dai aurenku da Ɗansandan nan ya tabbata, to kema 'yar sanda za ki zama?" Uwani ta yi jim sannan ta ce.

"Da dai tuƙin jirgin sama nake son koya na dinga lulawa a jirgi ta cikin gajimare, an ce fa idan ka na jirgi har taɓo gajimare ana yi da hannu idan aka zira hannu. Amma dai yanzu tun da na auri Ɗansanda gaskiya ina jin ni ma 'yar sanda zan zama, ko ba komai Yaya Jafar ba zai mini baraza da bindiga ba tun da kar ta san kar..." Maganar Uwani ta maƙale sakamakon hango Shukra da saurayinta a ƙofar gida, suna jingine a jikin mota Shukra sai karairaiya take masa tana fari, a can gefen wata bishiya ta hango wani mahaukaci da ake yi masa laƙabi da 'Ba ka da nauyi.' Ɗabi'arsa ce ya ɗauki mace ko namiji ya dinga yawo da kai a gari yana ce wa ba ki da nauyi, kuma ba zai dire ka a ko ina ba sai tsakiyar kwata.

A fili Uwani ta sheƙe da dariya Kubra ta ce.
"Lafiya kike dariya 'Yar ƙashin gwiwa?" Gyaɗa marau ɗin hannunta ta kalla sannan ta ce.
"Zo mu je wurin ba ka da nauyi."

Kubra ta zaro ido, da sauri Uwani ta haÉ—e fuska.
"Malama tsaya a nan wallahi kika ɓata mini shiri sai na sa shi ya ɗauki Baffanki gobe." Kubra ta ja baki ta tsuke don ta tabbata Uwani za ta aikata fiye da haka.

"Baka da nauyi za ka ci gyaÉ—a marau?" Uwani ta faÉ—a tana kaÉ—a ledar gyaÉ—ar a gaban mahaukacin. Washe baki ya yi cikin katuwar muryarsa ya ce. "Anci gyaÉ—a."

"To bari kaji ina da gyaɗa marau soyayyiya da yawa, idan kana son na baka to ka ga waccen saurayi da budurwar ka je ka ɗauki budurwar ka zaga gari da ita, duk wanda ya zo cetonta ka haɗa masa jini da majina ni na sa ka. Na maka alƙawari zan ƙara maka wata, ƙila ma ba baka kwano guda..."

Tun Uwani ba ta gama magana ba, Baka da nauyi ya fisgi ledar gyaÉ—ar hannunta ya saka a aljihu, kai tsaya ya nufi wurin su Shukra ya tsaya a gabansu yana sakin shashashar dariya.

A yatsine Shukra ta dube shi ganin yadda kayan jikinsa suke duƙun-duƙun ya sa Shukra ta tsartar da yawu sannan ta ce.
"Malam mene ne haka ka zo ka saka mutane a gaba? Haka kawai ka saka mu tashin zuciya, dalla matsa daga nan." Ta yi maganar a yatsine ita a dole ta yi birga a gaban Salim.
Salim ya kaÉ—a mukullin motarsa yana shirin yin magana sai gani ya yi Baka da nauyi ya suri Shukra yana dariya, da mamaki Salim ya dube shi fuska a haÉ—e ya ce.

"Kai Malam wannan wane irin iskanci ne..." Tun Salim bai rufe baki ba Ba ka da nauyi ya sa gwiwar hannunsa, ya yi masa mahangurɓa a fuska ya kusa haɗa masa jini da majina. Wani haske Salim ya gani ya gifta masa kansa ya yi wani irin nauyi dum. Cikin gigita ya faɗa cikin gidan da gudu, da yake sashen Dada shi ne yake kallon ƙofa da sauri ya faɗa ciki a guje cikin fitar hayyaci, Dada na tsaye da ɗaurin ƙirji za ta sauya kaya sai ganin mutum ta yi ya shigo a guje yana wuri-wuri da wawure-wawure.

"Hasbunallahu wa ni'imalwakeel kai wane gansamemen ƙaton ne haka..." Kalaman Dada suka maƙale sakamakon jin Salim na fisgar zanin jikinta ta ƙasa yana tura kai don shi maɓoya yake nema.

"Kai don ubanka ba ka ganin ni tsohuwa ce, wai me kake nema a ciki ne?" Salim ya sake hankaɗe kansa yana shirin bankaɗe Dada ta faɗi a ƙasa, ganin haka ya sa Dada ta saka kuka tana faɗin.

"Yau wane salon kwartanci ne haka ido biyu tun dare bai yi ba." Dada ta furta tana fisgar zanin shi ma Salim yana ja. Ganin Salim da gaske tura kansa yake yana yunƙurin sauke zanin Dada a ƙasa ya sa ta fasa ihu tana faɗin.

"Jama'a ku kawo mini É—auki ku ceci tsohuwa a hannun kwarto."

"Don Allah ki ɓoye ni zai sauke mini fuskata daga jikin kaina." Salim ya faɗa cikin tashin hankali, yana sake fisgar zanin Dada yana tura kansa ciki.
"Don Ubanka ka rasa a ina za ka ɓoye sai a cikin zanina, kai amma dai yau Allah Ya haɗa ni da lalatattun kwaratan zamani." Salim bai bi ta kan Dada ba ya sure zanin jikinta ya yi uwar ɗakinta a guje, sai ga Dada daga ita sai ɗan tofi shi ma ya zazzago ƙasa saboda kiciniyar da suka sha da Salim.

Shukra ban da ihu da zille-zille babu abin da take yi, don Ba ka da nauyi ya sauke ta amma ya ƙi, yara kuwa sai bin su suke a guje suna masa waƙa da tafi. Wannan ya sake ingiza shi ya ci gaba da gudu da Shukra a saman kansa, ɗankwali da mayafinta tuni suka cire tun a ƙofar gida. Sai da ya gaji don kansa ya je wata ƙatuwar kwata ya tsoma ta a ciki.

"Allah Ya isa tsakanina da kai." Shukra ta furta cikin kuka. Hannu ya zira a aljihu ya ciro wata ƙatuwar goruba ba ta yi aune ba sai ji ta yi ƙwal ya buga mata a goshi, ya juya ya ci gaba da tafiya. Azaba ta sa Shukra ta rushe da kuka, ga zurfin kwatar ya mata nisa ba za ta iya fitowa ba ga zafin dukan goruba a goshi. Kafin wani lokaci tuni goshinta ya yi wani malolo a daidai wurin da ya ƙwala mata.

Cike da takaici Dada ta rushe da kuka sannan ta ce, "Jama'a ku zo ya ƙwace mini zanin jikina, ku kawo mini ɗauki kwarto har uwar ɗakin tsohuwa."

07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚

*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

SHAFI NA TAKWAS

Uwani saboda dariya har kwanciya ta yi a ƙasa, Ba ka da nauyi ya ƙarasa wurinta tun bai yi magana ba ta miƙa masa ɗayar ƙullin gyaɗar.

"Ba ki da nauyi ta yi malolo." Haka yara suka dinga yi wa Shukra waƙa suna tafi, ban da kuka babu abin da take yi saboda tsananin kunya da ɓacin rai. Da ƙyar wasu matasa suka kori yaran suka yi kama-kama suka tsamo ta a cikin kwata. Tana tafe ruwan kwata na ɗiga wasu daga cikin yaran suka fara yi mata wata waƙar.

ÆŠoyi, É—oyi É—oyi.
ÆŠoyi damalma kashi.
ÆŠoyi tukunyar kashi.

A haka Shukra ta ƙarasa gida nan ma wasu daga cikin tsurarin yara suka bi ta Uwani na take musu baya, Shukra na shiga sashensu ta ɓarke wa Mami da wani irin kuka.
Chapter 13 · 0% Book details