← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 71

Sashe 18

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannu a hankali kwanaki suka fara gangarowa har bikin su Uwani ya ƙaraso, shirye-shirye daga kowanne ɓangare ya yi nisa. Dangin mahaifiyar Uwani da mahaifiyarta ba ƙaramin ƙoƙari suka yi ba, haka su baba Yunusu su suka yi wa Uwanu komai har da su gara. Ƙawayen Uwani su Zulai, Hansatu, Furaira da Kubra sai rawar kai suke su a dole ga manyan ƙawayen amarya. Jafar kuwa ya yi wata irin rama ya ɗan yi duhu kamar shi ne macen, ita kuwa Uwani ko ajikinta sai ma warkajaminta take yi.

Ranar juma'a ita ce ranar da aka yi kamun Uwani kuma a ranar ne za a kai ta, tun ranar alhamis aka rangaɗa wa Uwani lallen dungulmi hannu da ƙafa. Ranar Juma'a da sassafe Dada ta ja Uwani uwar ɗaki ta ce.

"Uwani ni kam ina kunyar a kai ki ɗaki da wannan uwar kwarkwatar, kin san dai Jafaru da tsirfa tsiya. An ya ba aske miki kan nan zan yi baki alaikum, ba tare da wani ya sani ba." Ita kanta Uwani kan ya ishe ta ga yawa ba gyara ga kuma kwarkwata, don haka ba ta musa wa Dada ba. Da kanta ta karɓi kuɗi ta sayo reza, kamar masu yin wani ɓoyayyan sirri haka Dada da Uwani suka shige uwar ɗaki. Da farko almakashi Dada ta sa ta fara sauke mata kan tass sannan ta bi shi da reza ta yi mata ƙwal kwabo. Nan take Uwani ta ji wata ni'imtacciyar iska na shiga kanta, Dada ta bi ta banɗaki ta wanke mata kan tass sai ga kan Uwani ya fita ƙwal kamar bayan silba yana sheƙi. Bayan Uwani ta gama shiri ta kawo ɗankwali ta ɗaure kanta da shi, tun da ta ji iska na shigarta ta ci alwashin daga ranar idan kanta ya taru aski za ta dinga yi.

A daren ranar ne kuma aka shirya Uwani domin kai ta ɗakin mijinta, saboda haka Baba Yunusu ya tara 'yan uwansa aka yi wa Jafar da Uwani nasiha. Uwani na daga cikin mayafinta sai satar kallon iyayen nata take, Jafar kuwa ya haɗe fuska ya sunkuyar da kai ƙasa abin duniya ya haɗe masa. Har an zo fita da Uwani sai Dada ta ja ta gefe ta fara yi mata raɗa a kunne, lokaci ɗaya sai ji aka yi Uwani da Dada sun bushe da dariya. Bayan Dada ta gama mata nasiha sai kuma ta rushe da kuka, sai da aka lallashi Uwani sannan suka wuce Dada ta riƙe hannun Jafar da Uwani suka shiga mota. Ragowar 'yan kai amarya kuma suka bi sauran motoci aka wuce da su gidan Mami.

Sai da Dada ta kai Jafar da Uwani har sashen Mami domin ta yi musu nasiha, a yatsine ita da 'yan uwata suka tarbe su don yadda ta hangi Uwani tare da Jafar har ji ta yi kamar ta shaƙe ta. Su Dada na fitowa suka ci karo da su Amir shi da wasu abokan Jafar guda biyu.
Dada ta wuce da Uwani sashenta shi kuma ya wuce wurin su Amir.

"Ango ango!"
Amir ya furta yana dariyar ƙeta.
"Kai ba na son iskanci." Jafar ya faɗa a daƙile.

"Wato wata miyar fa sai dai a maƙota, abokina ga fa alƙawarina na cika." Amir ya yi maganar cike da shaƙiyanci yana ɗago masa ledar kaji. Jafar duk tsiyar da suke yi masa shiru ya yi ya ƙyale su, ganin dare ya fara yi ne ya sa suka tilasta masa shiga cikin gidan.

Har kan gado Dada ta kai Uwani, suna shiga ɗakin Uwani ta fisge mayafin tana kalle-kalle. Dada kuwa sai murmushi take tana sa wa su Baba Yunusa albarka. Sai da Dada ta zo tafiya a nan ne fa Uwani ta maƙele ta tana wani irin kuka mai ban tausayi, ita a dole sai Dada ta zauna. Sai da Inna Atika ta zare wa Uwani ido sannan ta koma laƙwas kan kado ta zauna. Gabaɗaya manya suka tafi daga Uwani sai ƙawayenta su Furaira.

"Ke kam Uwani a duniya me za ki nema? Ga miji kin samu ga gidan miji kamar na kwamihina. To ke kuwa kukan me za ki yi?" Furaira ta faɗa, da yake duk cikinsu ta girme musu nesa ba kusa ba. Uwani ta goge ƙwalla nan take su Furaira suka dinga yi wa Uwani huɗuba kala-kala, wani su ƙyalƙyale da dariya wani kuma su tashi su gwada abin da suka ce Uwani ta yi.

Suna cikin haka sai ga sallamar su Amir, Uwani da sauri ta ta ja mayafi ta rufe fuska tana murmushi, ita a dole irin kunyar nan ta amare. Tun da su Amir suka shigo Furaira take wata irin kwarkwasa, bayan sun gaisa a gefe ta hangi Jafar ya sunkuyar da kai ƙasa. Furaira ta ƙarasa gabansa fuskarta cike da ɗige-ɗige ta saka mayafin a kafaɗa, ga wasu hannuwan jajayen rigar mama da suka leƙo ta kafaɗarta. Furaira yi farrr da ido ta ce.

"Angonmu na ga kana cikin damuwa, idan ka yi haƙuri za mu ba ku wuri kai da amaryarka ku gwangwaje amarcinku, wannan tagumin ai ba naka ba..." Tun da Furaira ta fara magana Jafar ya kafe ta da ido yana kallon tsana, wani irin takaici ya mamaye shi. Jin abin da ta faɗa ya sa ya ɗago ya ɗauke fuskarta da mari. Sai ga Furaira daɓar a ƙasa, waɗansu manyan tagwayen taurari na yi mata yawo a fuska. Ganin abin da ya faru da Furaira ya sa su Zulai suka fita a guje har mayafai da ɗankwalayansu na faɗuwa ƙasa.

Amir na shirin magana Uwani ta buÉ—e kai daga cikin mayafi ta furta. "Haba Ya Jafar yanzu a gaban abokanka za ka zubar mini da mutumci? Furaira fa ka mara gaskiya ba ka..."
"Rufe mini ba ki."
Jafar ya buga mata tsawa, sai da ta muguÉ—a masa baki sannan ta shiga wurga masa harara don a wannan karon Jafar ya ba ta haushi sosai.

"To ango mu dai maƙasudin zuwanmu shi ne..." Da sauri Jafar ya katse Salis.
"Ba na son hayaniya Salis sai da safe." Amir ya gimtse dariya yana miƙa masa ledar kajin hannunsa ya ce.
"Au har korar mu kake, shegen gora mum muna kan hanya..." Gabaɗaya sauran abokan Jafar suka saka dariya, sai da suka yi wa Uwani sallama sannan suka fita. Uwani saboda ɓacin ran abin da ya yi wa su Furaira ko tanka musu ba ta yi ba.

Jafar na raka su ya koma falo ya zaune, a gajiye ya tuɓe babbar rigar jikinsa ya faɗa kan kujera yana lumshe idanu. Wayarsa ce ta fara neman agaji, da sauri ya ɗago ya duba. Safna ce ke kiransa don haka ya yi rejecting sannan ya kira ta.

"Baby wuni guda ka manta da ni." Daga can ɓangaren ta furta a shagwaɓe.
"Ta ya ya zan manta da ke cutie?" Ya amsa mata.

"Akwai wanda ya taɓa mini gwarzona ga dukkan alamu, baby me yake damunka? Kwana biyu na gagara gane kanka." Murmushi Jafar ya yi sannan ya furta.

"Daddy ne ya saka ni wani aikin so na gaji sosai."
"Ok, ka yi wanka ka huta da safe ma yi magana becouse akwai maganar da nake son yi da kai." Dam! Ƙirjin Jafar ya buga ba tare da ya san dalili ba, ya yi ƙarfin halin amsa mata sannan suka yi sallama.

Tun bayan fitar su Jafar Uwani ta fisge mayafin kanta, ta shiga ɓuruntun duba ɗakin ta buɗe wannan ta leƙa wannan. Bayan ta gama dube-dubenta ta koma bakin gado ta zauna, tuno huɗubar su Furaira ta yi da wacce Dada ta yi mata sai kawai ta saki murmushi. Banɗaki ta faɗa ta yi wanka, sannan ta buɗe akwatin lefenta ta zaro wata doguwar riga. Sai da ta ɗaga wata riga ta ƙare mata kallo sannan ta furta.

"Ashe shi ma ya Jafar ƙwallon ɗan iska ne a fakaice ban sani ba, dubi irin rigar fitsararrun indiya da ya sa aka sayo mini. Allah Ya sawaƙe ina zan yi wannan lalacewar Dada ta ga ya wa baba Mamman, haka kawai ya yi mini faɗa." Uwani ta cusa rigar cikin akwatin sannan ta zaro wasu riga da wando ta saka. Sabuwar hula ta farke ta saka a kan ƙwaryar molon kanta, sai kuma ta ciro wasu sababbin panties da rigar mama guda bibbiyu ta farke tana dariya. Can drower kayan Jafar ta buɗe ta jefa guda biyu sai kuma ta taka gado ta saƙale biyu a saman drower, ta koma tana bin ledar kajin da kallo ƙamshi na dukan hancinta. Ganin Jafar ba shi da niyyar dawowa ya sa ta ɗauko ledar kajin da sauran kayan shaye-shaye ta baje ta hau lodawa cikinta.

Uwani na nan zaune Jafar ya shiga ko kallon ƙurarta bai yi ba ya nufi drower kayansa domin ya ɗauki towel zai shiga wanka, yana buɗe drower sai jin abu ya yi a kansa rigar mama ta faɗo. Dama Uwani su Furaira sun ce ta yi haka ne, wai yin hakan na jan hankali ango da ƙara danƙon ƙauna. Shi kuwa Jafar yana buɗewa da ya ji abu ya faɗo kansa yaraf da sauri ya buga uban tsalle yana faɗin.

"Wayyo ɓera, wayyo Allah ɓera a kaina." Uwani na daga wurin da take zaune sai dariya take, a gefen kafaɗarsa ya hangi rigar a fusace ya fisge a yatsine ya furta.
"Mene ne wannan."
Uwani ta kanne dariyarta ta É—an basar ta ce.

"Me ka gani to? Ba kai ka saƙalo a jikinka ba? Wai dama duk wannan muzuran da kake yi tsoron ɓera kake?" Jafar ya fisge rigar ya wurga mata, ya ƙarasa ya bige bakinta haɗe da matse shi da hannunsa. "Idan ba ki daina mini rashin kunya ba sai na fasa bakinki." Towel ya ɗauka har zai shiga toilet ɗin da ke cikin ɗakin ko me ya tuna sai ya fice ta nufi public toilet, bayan ya yi wanka ya ɗauko filo ya dawo falo ya kwanta. A kan kujera ya kwanta ya ji kwanciyar babu daɗi ya miƙe kenan ya ji bugun ƙofa, kafin ya tambaya ya ji muryar Mami da sauri ya buɗe Mami ta shiga tana bin ɗakin da wulaƙantaccan kallo.
Chapter 18 · 0% Book details