Sashe 62
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fuska a haɗe Jafar ya koma gida ganin haka ya sa Safna ta ɗan sha jinin jikinta, da yake Jafar a ƙule yake da abin da Safna ta yi masa ko kallon kirki bai yi mata ba. Can kan table Jafar ya fara duba wa bai ga komai ba, fuska a haɗe ya furta.
"Ina abinci?"
"Ban dafa ba!"
"Saboda me?"
A watse Safna ta ce, "Saboda haka na yi ra'ayi, ni fa gaskiya na gaji wallahi ba zan juri girki kullin ba, saboda ba cin na kirki kake ba." Jafar bai tanka mata ba ya faɗa banɗaki, Safna ta jima tana fakon Jafar a kan wayarsa. Don haka tana ganin ya shiga toilet da sauri ta ɗauki wayarsa ta fara duba whatsapp chats, babu wata baƙuwar lamba da ta gani wacce ta danganci hirar soyayya. Cikin gallery ta duba nan ma babu wasu baƙin hotuna da ba ta san da su ba. Wata folder ta gani an rubuta J&J kamar yadda a folder da ke ɗauke da hotunanta ita da Jafar ya rubuta J&S, ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi. Da sauri ta saka hannu za ta buɗe sai gani ta yi akwai key a ciki. Motsin Jafar ta ji zuciyarta na suya ta kafe ƙofar da kallo.
"Wannan folder mene ne a cikinta? Kuma mene ne ma'anar sunan da ka rubuta?" Jafar bai tanka mata ba, ya karɓi wayarsa ya juya zai yi gaba. Da sauri Safna ya sha gabansa cikin tsiwa ta ce. "Magana nake yi ka mayar da ni mahaukaciya, wace ce wacce kake soyayya da ita ban sani ba." Jafar ya lumshe ido jin wani abu na sake fusgarsa a kan Uwani, ya watsa mata idanunsa a lumshe sannan ya ɗora hannunsa a gefen ƙirjinsa ya furta.
"Wata mai muhimmanci ce a gare ni, ba iya mai muhimmanci ba a duk sauka da hauhawar numfashina na fita da tsantsar so da ƙaunarta..."
Tun bai rufe baki ba Safna ta shaƙe masa wuya tana zunduma ashar sannan ta ce.
"Wallahi ka yi ƙarya ka tozarta ni Jafar, wallahi ba ka isa. Uban wa ya ce ka fara soyayya da ita..."
Jafar hannu ya É—aga kamar zai mare ta sai kuma ya sauke, ya fisge jikinsa haÉ—e da hankaÉ—a ta sannan ya koma falo zuciyarsa na suya.
"Wato damar da Safna ta samu a wurin Mami har ta kai haka kenan? Tabbas ya zama wajibi na ɗauki mataki a kanta." Jafar ya raya a ransa. Kuma tun daga wannan ranar ya koma kwanan falo ita ma Safna ta shiga fushi da shi, abin duniya ya haɗe mata. Sai ta yi kamar ta kira Mommynta sai kuma ta fasa, amma hukuncin da Jafar ya ɗauka a kanta ba ƙaramin zafi ya yi mata ba. Dalilin da ya sa suka ci gaba da zaman doya da manja, ganin ba za ta iya jura ba ya sa watarana Safna ta je ta samu Jafar ta ba shi haƙuri don Safna ba ƙaramar soyayya take yi wa Jafar ba. Ta kuma ci burin gano ko wace ce ke ƙoƙarin kwace mata miji, ta ci alwashin ko 'yar gidan uban waye sai ta nuna mata iyakarta.
A haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya har lokacin bikin Auta ya ƙarato, duk wani shirye-shiryen biki ita da Uwani suke tsarawa sai Aunty. Wani abin kuma ta kira Shukra a waya su tattauna don Shukra ta sauko sosai ba kamar da ba, kamar wancan karon duk wani abu da ya danganci cimar taro ta cikin gida Daddy ya damƙa wa Aunty komai. Game da kayan kitchen da kayan ɗaki ne Daddy ya kira Mami suka tattauna domin ya ba ta haƙƙinta, saboda kawo wannan lokacin Mami ta haƙura da jiran gawon shanu ta fawwala wa Allah lamuranta.
Aunty ta yi rawar gani wurin tsayawa tsayin daka ta gyara Auta tamkar yadda ta haÉ—a wa Uwani haÉ—in kayan gyara a wurin BOJUWA 08032773332, hakan ya sake É—aga darajarta a wurin su Shukra da Daddy. Hatta Mami ta fara zubar da makamanta don ta lura ita take kiÉ—a kuma take rawarta.
"Dada gaskiya babu abin da zai hana ni zuwa bikin Auta, ni fa wallahi zaman gidan ma ya ishe ni a ce kullin ina gida daga asibiti sai gida." Uwani ta furta wa Dada a shagwaɓe lokacin da ta kawo mata ziyara.
"Ƙaniyarki Uwani, wa yace miki mai tsohon ciki tana shiga cikin taro? A hir ɗinki ki kiyaye ni, ke ba ki san ana haɗuwa da tanɗau da lasau ba?" Uwani ta tura baki gaba ta ce.
"Ai wallahi ni dai kurwata ta fi ƙarfinsu, a wannnan karon sai dai ku yi haƙuri. Don ni fa na gama shirye-shiryen biki hatta jaka da takalmi babu abin ban tanadi na fitar biki ba." Dada ta riƙe baki ta ce.
"To ai shi kenan, idan ba ki yi gaddama ba ai ba a ce ke jinin Umaru ba ce." Daga haka suka ci gaba da hira. Da Dada za ta tafi kuwa Uwani ta maƙale a kan dole sai ta bi ta sun tafi tun da bikin Auta saura bai fi kwana huɗu ba. Babu yadda Dada ta iya haka Uwani ta cika akwatinta da komai da ta san za ta buƙata suka wuce da Dada. Tun suna hanya Uwani ta tura wa Auta da Aunty saƙon ta bi Dada, Auta ta ce mata washegari za ta zo daga nan sai su wuce gidan lalle. Cikin Uwani ya tsufa sosai don ta shiga wata na tara, ta yi ƙiba kamar ba ita ba.
Ranar alhamis aka fara bikin Auta kuma a ranar ne ta yi bridal shower, ranar Juma'a ya kasance kamu. Duk wani gyaran kai da lalle da aka yi wa Auta tare aka yi wa Uwani, hatta kwalliya a wuri ɗaya aka yi musu. Daga wurin make up ne kuma suka wuce hall ɗin da za a yi kamu. Hall ɗin ya ƙayatu sosai da adon kayan gargajiya, Uwani atamfa lace ta saka wacce aka buga mata aiki a gaban rigarta. Sai ɗaurin ɗankwalin da aka kafa mata ba ƙaramin kyau ta yi ba, musamman da ta yi ƙiba ga cikin jikinta ba ƙaramin karɓarta ya yi ba. 'Yan uwa da ƙawayensu na makaranta sai tsiya ake yi wa Uwani. Tana nan zaune a kan kujera, ita da wasu classmate ɗinsu na makaranta suna hira Safna ta ƙarasa cikin doguwar rigar wani tsadaddan material. A gefen kujerar Uwani ta zauna ta ɗan saki murmushi tana faɗin.
"Sannu!"
Ɗago kan da Uwani ta yi karaf suka sauka a kanta. Tabbas ko a cikin mafarki ba za ta gagara manta fuskarta ba, duk da ta kwana biyu da ganinta amma kamaninta na nan daram a ƙwayar idonta. Sai ɗan haske da murjewar fata da ta sake yi, ko babu tantama ta tabbata wannan Safna ce. Tunanin Uwani ya katse a daidai lokacin da ta riski muryar Madina tana faɗin.
"Aunty Safna ga wurin zama can ko har kin zauna..." Maganar Madina ta maƙale sakamakon ido biyu da suka yi da Uwani.
"Na riga na zauna Madina, ba na son ƙarar speaker can." Safna ta furta ta sakin murmushi.
Littafin kuÉ—i ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan no 07062062624 idan littafi ya kammala 800 neðŸ«
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
A wayance Madina ta amsa tana barin wurin, cikin zuciyarta tana mamakin irin kyau da murjewar da Uwani ta ƙara yi.
Wani abu ne yake taso wa Uwani a zuciyarta, a hankali ta runtse idonta tana karanto duk wata addu'a da tasan za ta sanyaya mata zafin da take ji a cikin ranta.
"Mai shanu ya dai? Kada ki haife mana ɗa a filin nan fa, idan abar ta zo wuce mu shiga ɗakin ajiyar gift kin san tsaf zan karɓi haihuwarki." Ɗaya daga cikin ƙawayen su Uwani Nabila ta furta cikin zolaya, da yake a makaranta mafi yawa sunan da ake kiranta ita da Auta kenan. Jin sunan da aka ambata ya sa Safna ta ɗago ta dube ta, don babu tantama tun da ta ji inkiyar sunan Jafar ta fahimci ita ma Uwani ɗaya daga cikin 'yan uwansa ce. Sosai ta ga yanayin kamannin Uwani da na Auta, ta basar ta ci gaba da latsa wayarta. Murmushin yaƙe Uwani ta yi ta ce.
"Sai kace babu manya a wurin zan bari ki karɓi haihuwata Nabila, wallahi kin ma raina ni da yawa." Yadda Uwani ke mu'amala da ƙawayenta a ɗan zaman da Safna ta yi haka kawai ra ji sun birge ta. Jakarta ta zuge da niyyar ɗaukan kuɗin liƙin da za ta yi wa Auta, ta dafe kanta sakamakon matuwar da ta tuna ta yi. Da sauri ta ciro wayarta ta latsa lambar Jafar, ba a ɗauki lokaci ba ya ɗauka.
"Baby na yi mantuwa wallahi!"
Daga can ɓangaren Jafar ya furta.
"Me kika manta?"
Saukar kalaman Jafar ya yi daidai da bugun ƙirjin Uwani da ke kusa da Safna, don tana jiyo maganarsa raɗau a kunnenta. Zuciyarta ta shiga harbawa da ƙarfi fat-fat. Wani irin kishinsa ya turnuƙe ta. Tana cikin wannan yanayin ta riski muryar Safna na faɗin.
"Wallahi kuɗin da zan yi liƙi na manta a kan mirror."
"Ni kuma kin ga yanzu na fito daga gida zan ƙaraso nan." A shagwaɓe Safna ta narke tana faɗin.
"Please baby don Allah ka taho mini da su." Shiru Jafar ya yi sannan ya furta.
"Sai na ƙaraso."
Safna ta sake narkewa tana faÉ—in.
"Don Allah Baby..."
A hanzarce Uwani ta tashi daga wurin jin zuciyarta na barazanar tarwatse mata, a can kujerar da su Dada ke zaune ta ja wata ta zauna. Suna haɗa ido da Auta sakar mata murmushi, shiru Uwani ta yi tana jin zuciyarta babu daɗi. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla, ta kwantar da kanta a jikin table a daidai lokacin Aunty ta ƙarasa wurin. Aunty ta yi kyau sosai gwanin birgewa, ɗagowar da Uwani ta yi ne ya sa Aunty ta fahimci tana cikin damuwa. Hannunta ta kama suka bar cikin mutane sannan ta ce.